LABARIN WANI MAI ARZIKI

LABARIN WANI MAI ARZIKI

Watarana Annabi Musa (as) yana zaune sai wani yaro yazo ya sameshi yace "Ya Annabin Allah, ina so ka roka min Ubangijinka ya bani arziki da dukiya".

Sai Annabi Musa (as) yace masa "Zaka rayu shekara Sittin ne aduniya. Shin Kafi son Ubangiji ya baka arzikin nan acikin shekaru 30 na farkon rayuwarka ne, Ko kuwa a shekaru 30 na Qarshen rayuwarka?"

Sai yaron nan yaje ya rika tunani yana hangen Qarshen rayuwarsa, kuma yana kallon farkonta. Daga karshe dai sai ya dawo yace ma Annabi Musa (as) "Na Zabi abani arzikin nan acikin shekaru Talatin da Farkon rayuwata".

Wannan saurayin ya manta da cewa idan ya tsufa zai hadu da jinya da raunin Jiki irin na tsufa..

Shikenan Annabi Musa (AS) ya roka masa Allah akan wannan bukatar. Kuma Allah ya amsa masa. Nan da nan sai gashi ya fara tara arziki da dukiya Har ya girma ya zama Hamshakin mai kudi.

Amma fa duk da haka ya kasance yana bu'de ma sauran mutane hanyoyin arziki, Yana taimakon Mutane yana basu dukiya har ma yana bama wasunsu Jarin yin kasuwanci. Wasu kuma ya taimaka musu akan bunkasa Sana'o'insu ko Noma ko kiwon da sukeyi.

Kuma yakan taimaka ma wasu wadanda suke son yin aure amma babu halin yinsa. Yana daukar nauyin marayu da miskinai.

Bayan shekara Talatin ta wuce, duk da haka arzikin nan nasa bai Qare ba. Babu abinda ya chanza acikin yawaitar dukiyarsa.

Wannan abu ya bama Annabi Musa (as) mamaki. Don haka ya tafi ganawa da Ubangiji sai ya tambayeshi cewa Gashi shekaru Talatin din nan sun Wuce (Amma arzikin mutumin nan bai Qare ba).

Sai Allah ya amsa masa da cewa "NA SAMU BAWAN NAN NAWA YANA BU'DE KOFOFIN ARZIKI GA SAURAN BAYINA. DIN HAKA NAJI KUNYAR IN TOSHE MASA KOFOFIN ARZIKINA ZUWA GARESHI".

Hakika akwai babban darasi acikin wannan Qissar musamman ga masu arzikin cikinmu. Wadanda Allah ya azurtasu amma basu Qaunar waninsu ya samu daga garesu.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA