DUNIYA KENAN

Magana kamar magani ce idan ta yi yawa sai ta sa cuta.

Jita-jita maketata ne suke shirya ta, wawaye ne suka yada ta, maras sani ne yake aiki da ita.

Mugun aboki kamar inwa ne sai kana cikin haske kake ganin sa.

Duk yadda takardar kudi ta lalace kudi ce, takardar nama kuwa ko an shafa mata mai banza ce.

Gaskiya mabudin nasara ce, hakuri mabudin ni'ima ne, ilimi kuwa mabudin arziki ne.

Duniya dakin jarabawa ce, kowa da alkalaminsa da takardarsa, amma kowa da lokacin da aka dibar masa, idan ya kare nan take za a kwace takarda a kai ta wajen maki da tantancewa. Kada ka damu da abinda wani ya rubuta ko yake rubutawa. Kai dai shiga taitayinka, kowa tasa ke fisshe shi.

Rayuwa da mutuwa sun yi kama da juna. A ranar da ka zo duniya ka taho tsirara sai an yi maka wanka a tufata ka. Haka ma idan ka mutu sai an tsiraice ka, a wanke ka, sannan a suturta ka. A lokacin da ka shigo duniya ba ka iya tafiya sai dai a dauke ka. Haka ranar mutuwa ba ka san ma ana taulahi da kai ba. Ka shigo duniya kana kuka mutane suna murna suna jin dadi. Ka shuka alheri domin idan suka koka ranar mutuwarka ka kasance kana cikin jin dadi.

Duk abinda ka samu a duniya a nan za ka bar shi ko kuma shi ya tafi ya bar ka. Ribaci arzikinka ta hanyar sadaka tun mai abin bai karbe abinsa ba

Banbancin Mumini da Fajiri na bayyana ne idan suka samu arziki ko suka rasa. Mumini idan ya samu zai kankan da kansa ga Allah ya kyautata ma bayin Allah. Idan ya rasa kuma zai hakura ya bar ma Allah. Fajiri idan ya wadata zai yi girman kai ga jama'a, ya yi butulci ga Allah. Idan kuwa ya rasa to ya fi kowa raki da kai karar Allah a wurin mutane.

Wanda ya tara abubuwa biyar ya cika maras arziki: Rashin kunya da kekashewar zuciya da bushewar idanu da kwadayin duniya da dogon buri. Allah ka kiyaye mu daga tabewa.

Sanya ma rayuwarka manufa, kuma ka dage wajen cimma ta. Wanda ya bi tsuntsu biyu a lokaci daya zai rasa su gaba daya.

Idan ka yi jayayya da wawa za ka koma wawa irin sa. Ko jayayya abokin yi gare ta.

Idan zuciyarka ta raya maka sabon Allah ka tuna mata abubuwa guda uku: Allah na ganin ka, mala'iku na rubuta aikinka, mutuwa na kan hanyarta zuwa gare ka.

Kowa yana ado a ranar Idi amma ba kowa ne yake samun gafarar Allah ba. Yi kokari ka fita a wannan ranar ba ka da hakken kowa a kan ka.

Ilimi yana kawar da talauci. Shawara tana hana da-na- sani. Hakuri kuma shi ne maganin zaman duniya.

Kada ka ji tsoron yin addu'a saboda girma ko yawan zunubanka. Ka tuna cewa a kowane hali kai bawan Allah ne. A daidai lokacin da Shedan ya saba ma Allah, ya roke shi kuma ya karba.

Idan ka rasa abinka kada ka rasa hankalinka. Damuwa ba ta mayar maka da batacce, ba ta dawo maka da matacce, ba ta hana kaddara yin aikinta. Bar ma Allah duk abinda ya same ka, sai Allah ya ishe ka a cikin duk lamarinka.

Ruwan sama ba ya canja dandanon ruwan teku. Haka shi ma tsayayyen mutum maganar mutane ba ta canja shi.

Kwano idan ba komai a cikin sa ya fi kara. Haka shi ma mutum idan ka ji ya cika amo to fanko ne. Ruwan marmaro mabubbugar albarka, da sannu suke yin aiki ba da hayaniya ba.

Wanda ya cuci kasarsa daidai yake da wanda ya dauki kudin babansa ya bai wa barayi. Babansa ba zai yafe masa ba, barayi kuma ba zasu gode masa ba.

Mutane uku ka darajanta su: Dattijo da Malami da Mahaifi. Mutane uku ka tausaya masu: Tsoho da Macce da Yaro karami. Abu uku kada ka manta su: Mutunci da Addini da Mutuwa. Abu uku ka tsarkake su: Jikinka da tufanka da zuciyarka. Abu uku kada ka daina neman su: Ilimi da arziki da shiga aljanna.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA