Posts

Showing posts from October, 2015

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarkatuh, yau a fagen Fiqhu zamu dubi abubuwa guda uku wanda suke da alaka da tsarki, abubuwan sune Maniyyi, da maziyyi da wadiy,

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarkatuh, yau a fagen Fiqhu zamu dubi abubuwa guda uku wanda suke da alaka da tsarki, abubuwan sune Maniyyi, da maziyyi da wadiy, 1.maniyyi: Shi wannan wani ruwa ne da yake fitowa lokacin Yin jima’i ko mafarki ko makamantansu, yana da kauri in na namiji ne, inkuma ta macece yana nan tsiriri kuma yana fita da karfi, yana bibiyar juna. Hukuncin maniyyi: Akwai tsabani tsakanin maluma kan kasancewar maniyyi najasa ne ko ba najasa ba, abinda ya dace mutum dai yayi in maniyyi ta shafi tufafinsa ko jikinsa shine in maniyyin bai bushe ba sai ya wanke wurin da ruwa, inkuma ya bushe sai ya kankareshi. sannan hukuncin wanda maniyyin ta fito daga jikinsa, shine zaiyi wankan janaba, In maniyyin ya fito ta jima’i ne ko mafarki, hakanan mutumin daya farka daga bacci yaga maniyyi ajikinsa Shima zaiyi wanka. amma in mutum yayi mafarki ya tashi baiga wani maniyyi ajikinsa ba toh babu wani wanka akansa. hakanan mutumin da yake farke maniyyi ta fito ba tare da wata sha’awa...

GIRMAN KAI KASHI NA SHA DAYA.

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 8- Yawan Ibada: Yawan Ibada ya kan sanya wadansu mutane girman kai da wulaqanta mutane. Ma su irin wannan dabi’ar su na ganin cewa su su ne na Allah, su ne masu matsayi a gurin Allah, su ne 'yan gwagwarmaya da jihadi, su na ganin ragowar mutane kamar halakakku ne. Dalili kuwa shi ne, hadisi ya tabbata daga manzon Allah (saw) ya ce: “Idan kun ji mutum yana cewa mutane sun halaka to shi ne mafi halakar cikin su.” - (Muslim: 2823). Al-Imam an-Nawawiy ya ce: “Wannan hanin, an yi shi ne ga wanda ya fadi haka don jiji da kansa da qasqantar da mutane da daukaka kansa a kansu. Wannan shi ne haramun.” - (Riyadus Salihin, karkashin hadisi na 1598). Kuma wani hadisin ya inganta daga Abu Hurairah (ra), daga Manzon Allah (saw) ya ce: “Wadansu ‘yan uwa guda biyu sun kasance a cikin Banu Israila, dayansu ya kasance yan...

Sanatocin PDP sunyi Bore akan Amincewa da Amaechi da majalisa tayi a yau.

Sanatocin PDP sunyi Bore akan Amincewa da Amaechi da majalisa tayi a yau. Sanatocin sun fice daga majalisan a daidai lokacin da za'a amince da sunan Amaechi da nufin basu yarda da zabin nasa ba. Dukda haka shugaban Majalisan Dattawan Bukola Saraki yayi burus da kokarin hana hakan inda ya amince da Zabin Amaechi din tsakaninshi da 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC. Majalisar Dattawa ta amince da zabin ministoci 17 bakwai data tantance a majalisan wadanda suka hada da Adebayo Shittu, Kadjiat Abba Ibrahim, Heineken Lokpobiri, Claidius Omoyele Daramola, Baba Shehuri Mustapha, James Ocholi, Isaac Folorunsho Adewole, Bawa Bwari, Geoffrey Onyeama, Zainab Ahmed, Masur Mohammed Danladi, Usani Uguru, Okechukwu Elemanah, Anthony Anwuka, Mohammed Musa Bello, Adamu Adamu da Aisha Abubakar.

CUTAR BASIR

Babu abu mai ban tausayi ko kuma damuwa kaji Mace tace wai ashe haka BASIR yake lalata Maza ya maida su kamar mu. Ko mai tsananin Soyayya tsakanin Mace da Namiji, shine dai ayi Aure a Karshe, san nan a zauna matsayin Mata da Mijinta. A cikin Hakkokin da aka dorawa Miji wanda babu makawa sai ya sauke shine Kwanciyar Aure a tsakaninsu, kada kuma ya gaza sau 1 a cikin Kwana 4. Amma Mace tayi Aure, ta baro Gidajen Iyayenta, ana yi mata Murna, ana Allah ya kawo Katsantar Daki,bkuma tazo ta sami Ango bashi da Banbanci da ita kanta, to babbar matsala ta faru. Saboda haka in har Mace ta kai Karar Mijinta cewa ashe 'Yar Uwarta aka Aura mata, to Tsofaffi sun gano abinda take nufi, sai a fara nema masa magani kuma cikin gaggawa don kada murnar Amarya ta koma ciki. Yanzu labari ya bazu cewa mafi yawan Mata da zarar an sa musu ranar Biki, sun fara nema da kuma shan Maganin Mata, wato maganin basu Kuzarin Shimfida, da wanda zai kara musu Ni'ima da Annashuwa, da kuma wanda zai basu damar juri...

GIRMAN KAI KASHI NA GOMA.

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 7- Fasahar harshe da iya bayani: Fasahar harshe da iya bayani yana sanya wadansu mutane girman kai da ji-ji-da-kai da wulaqanta mutane, kamar yadda hadisi ya tabbata daga Jabir bn Abdullah (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa yana cikin wadanda su ka fi soyuwa a gare ni kuma mafi kusanci da ni a ranar alqiyama wadanda su ka fi kyakkyawar dabia. Kuma ya na daga cikin wadanda na fi qi, wadanda za su nesanta da ni a ranar alqiyama, su ne ma su yawan surutu (Al-Imamun Nawawiy ya fassara kalmar sarsaruna a harshen larabci da cewa: Sarsar, shi ne mai yawan kallafawa kansa gwanintar zance. Wadannan mutane su ne Ash-Sheikh Al-Usaimin ya siffanta su da cewa idan su na waje wani bai isa ya yi magana ba. Idan wani zai yi magana sai sun nemi su danne shi da surutu) da ma su nuna burga a cikin maganarsu (Kalmar ...

HATTARA DA AIKIN MUTANEN ANNANBI LUT

HATTARA DA AIKIN MUTANEN LUT HUDUBA DAGA MASALLACIN ABU HURAIRA (RA), SOKOTO A KAN HATSARIN LUWADI Bismillahir Rahmanir Rahim Hudubarmu ta yau tana magana ne game da wata barna da ta bayyana a cikin wannan alumma ta manzon Allah (S) wadda a asalin halittar yan adam ba a san ta ba, amma kwatsam ta taba bayyana a cikin wata alumma ta mutane, Allah (SWT) bai yi masu jinkiri bayan an yi musu waazi sun ki saurare ba, take sai Allah (T) ya share su daga doron kasa. Allah ya aiko malaiku suka yi mu su azabar da ba a taba wa dan adam ita ba. Allah ya aiko malaiku suka shafe idanunsu, sannan suka jirkitar da kasa a kan su, sannan aka yi masu ruwan duwatsun azaba. Wannan barna da suka aikata ta sake bacewa daga doron kasa illa ma sha Allah. Kuma sai Allah (Swt) ya kawo mana labarinsu a cikin surori tara na Alkurani: (Suratul Aaraf:80-84, Hud:77-83, Hijr:57-77, Anbiya:74-75, Shuara:160-175, An- Naml:54-58, Ankabut:28-35, Saffat:133-138 da kuma Suratul Qamar:33-39). Sannan sai manzon Allah (Saw) y...

GIRMAN KAI KASHI NA TARA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 6- Yawa: Yawan mabiya, ko na dangi ko na ‘ya‘ya sukan sanya wadansu mutane girman kai da dagawa. Dalili kuwa shi ne; Allah madaukakin Sarki ya ce: “Bamu aika wani mai gargadi a cikin wata alqarya ba, face ma su dukiya da shugabannin garin sun ce; lallai mu ma su kafurcewa ne ga abin da aka aiko ku da shi. Kuma su ka ce: mu ne mafi yawan dukiya da ‘ya‘ya kuma mu ba za a azabtar da mu ba.” - (Suratu Sabai aya ta 34 35). A wata ayar kuma Allah madaukakin Sarki ya bamu labarin mutumin da ya mallaki gonaki biyu, kuma kowacce ya sami amfanin gona mai yawa, amma maimakon ya gode wa Allah sai ya yi dagawa da girman kai, da jin isa, da gorantawa abokinsa, inda ya ce masa: Ni ne na fi ka yawan dukiya da xinbin jama’a (magoya baya).” - (Suratul Kahafi aya ta 34). Wadannan ayoyi na nuni akan yadda wasu su ke alfahari da...

MUHIMMANCIN HAKURI

MUHIMMANCIN HAKURI IMRAN BN HUSAIN yana daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww). Allah ya jarabceshi da ciwon Basur. Da yayi hakuri ya jure wannan jarrbawar sai Allah yayi masa wata baiwa. Wato ya kasance duk inda yake sai Mala'iku su rika zuwa suna gaisawa dashi. Yana cikin wannan yanayin, rannan sai yaje yasa akayi masa wata tsaga saboda maganin Basur din. Sai kuma ya lura da cewa tun da ya magance chutar, Mala'ikun nan sun dena zuwa gaisheshi. Don haka ya dukufa da addu'a yana rokon Allah ya dawo masa da basur din. Nan da nan sai Basur ya dawo, Kuma Mala'ikun ma suka ci gaba da zuwa gaisheshi. Wannan labarin yana karantar damu muhimmancin yin hakuri abisa duk wata jarrbawar da mutum ya tsinci kansa aciki. Watakil Allah ya jarrabeka ta hanyar Jinya, ko Talauci, ko damuwa tsakaninka da abokan aikinka, ko matarka. ko tsakaninki da Mijinki ko Kishiyarki, ko tsakaninka da abokan zamanka, Ko iyayenka, ko 'ya'yanka, ko makobtanka. To amma idan ka jure ka mayar da la...

LABARIN WANI DAFILLO

FULANI MANYA Wani bafulatani zaije sayar da shanu kasuwa sai aka bashi takalmi babba irin na shiga ruwa, idan ya sayar ya zuba kudin aciki saboda 'yan fashi. Bayan ya sayar da shanu ya zuba kudin a takalmi kamar yadda aka umarceshi, suna cikin tafiya a hanyar dawowa gida sai ga 'yan fashi sukace kowa ya fito daga mota, Dan fulani yana fitowa sai ya zuba da gudu cikin jeji yan fashi suka bi bayansa koda suka iskeshi sukayi checking dinsa basu samu komai ba sai N20 sai babbansu yace lalle fulani akwai abin dariya kaida N20 gareka kake wahalar damu, yace wlh nima danasan ita zaku dauka dana tsaya ai nayi zaton kudin cikin takalmina zaku dauka.....

KISAN SIR. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA

Image
KISAN SIR ABUBAKAR TAFAWA BALEWA. Na John McIntosh ( Baturen Ingila masanin tarihin Nijeriya) Bayan sun kamoshi (Sir Tafawa Balewa) suka (daureshi a cikin mota suka yi ta jansa a kasa suna cikin mota inji Dan Masanin Kano) suka zagaye wasu wurare cikin Lagos dashi kafin su zarce bayan gari dashi. A can ne suka azabtar dashi, suka nakada masa bugun tsiya suka wulakantashi. Sannan suka tilasta masakurbar barasa da zukar sigari - Abubuwan da bai tabayi a rayuwarsa ba kasantuwarsa musulmi mai riko da addinin. Bayan sun kammala muzgunamasa, sai ya rokesu alfarma da su barshi yayi sallah ta karshe kan su kasheshi tunda ya tabbatar kasheshi zasu yi. Nan take a wulakance suka bashi izini. Bayan ya idar da sallar sai ya dubesu yace " Iyamuri ! Iyamuri ! Iyamuri !" Ya cigaba da cewa da yardar Allah ba zasu taba mulkar Nijeriya ba, zasu tarwatsu, za a tsanesu duk inda suke, zasu yi fama da bakin ciki iri iri da bala'oi, zasu yi fama da gaba daga sauran yan kasa. Bayan ya gama sai ya...

YAR UWATA KINSAN WANNNAN KUWA

*Kyau shi yake rudin maza, amma Ilimi shi yake sawa ajima ana tare? *Yanga shi yake rudin maza, amma iya magana ne yake gamsar dasu? *Jan aji yana qara miki aji a gaban mutane, yawan surutu yana sanyawa a raina ki? *Gaskiyarki tana qara miki qima a gaban mijinki, Karya tana yarfa ki da rage miki kima? *Zuwa da budurcinki gidan mijinki shine kawai 'yancinki, da zarar kin wulaqanta shi kin shiga matsala, kin gamu da wulaqanci da gori na har abada? *Bayyana sirrin aurenki babu inda zai kaiki, 6oyeshi tare da magance shi tsakaninki da maigida shine kawai mafita a gareki? *Idan kika bawa kudi zuciyarki, zaki wulaqanta, idan kika baiwa Allah zuciyarki zaki samu kulawa na har abada? *Tara mazaje babu inda zai kai ki, za6en daya tamkar da goma shine mafita? *Yawan dariya ko murmushinki zai sanya maza su raina ki, kama kai da maintaining zai qara miki girma? *Haquri da na gidanku shine mutuncinki, sa ido kan abin hannun maza babu inda zai kaiki? ...Ko wacce mace sarauniya ce sai dai wacce t...

GIRMAN KAI KASHI NA TARA.

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 5- Qarfi: Qarfin jiki yakan sanya mutum yin girman kai da ji-ji-da-kai da jin isa da dagawa. Irin wannan ya faru ga Adawa a lokacin da Annabinsu Annabi Hudu (as) ya ke kiran su zuwa bautawa Allah, sai su ka yi girman kai. Kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Su kuwa Adawa sai su ka yi girman kai a ban qasa ba tare da wani haqqi ba, kuma su ka ce: wane ne ya fi mu qarfi? Shin ba su gani ba cewa haqiqa Ubangijin da ya halicce su shi ne mafi qarfi fiye da su? Kuma sun kasance su na jayaya da ayoyinmu.” - (Suratul Fussilat, aya ta 15). Wannan aya tana nuna yadda Adawa su ka yi girman kai da dagawa saboda qarfi da Allah ya ba su, su ka manta cewa Allah da ya halicce su shi ne ya halicci qarfin, kuma shi ne ya ba su shi, mai makon su gode ma sa sai su ka qalubalanci annabinSa da cewa: wane ne ya fi mu qarfi?...

HAWA ACHABA

HAWAN BABUR GA YA MACE Hawa babur ga ya mace musansan man wace ta balaga ko matar aure ba karamin kuskure bane domin zaka ga matar aure akan babur na haya ana janta kuma jikinta na taba namai jan babur din kuma shima na taba nata. Haka abin yake a gurin ya mace budurwa zakaga ta hau babur wanda mafiya yawacin masu hayar idan suka fahimci cewar wannan budurwa suka dauka zakaga cewa zaman nasu ya canza maana dai yana dan gogarta. Duk dai abin da yaban haushi shine da misalin karfe shida da yan mintin ina zaune a dan bakin titi sai naga wani dan achaba dauke da wasu mata har guda biyu yana jansu anzu daf da irin jakin babangida yana latsa burki naga sun hankado shi maana kirjin daya daga cikinsu turo bayansa sakamakon birkin da ya matsa. Amma abin mamki kokadan abin bai dameshi ba haka zalika itama bai dameta ba haslima ita danna wayarta kawai takeyi babu mamakima charting takeyi. Haka ranan naje zan wuce ta wani wuri inda yan achaba suke taruwa naji wani dan achaba nacewa kainifa najima ...

RAYUWAR JAMI'A

Rayuwa tana cike da rudani da abubuwa masu ban al'ajabi, mamaki, haushi, ban dariya da kuma ban takaici ammafa ni tunda nake ban taba ganin ko jin abinda nagani kuma naji a jami'aba. Idan akacemin lalacewar jami'a yakai makura ada za'a iya kwana ana musu dani, amma ayanzu nasan cewa sai dai atakaita. Bana mantawa wata rana muna zaune da wata kawata sai wata kanwarta ta kirata tace tanason ganinta, ta gaya mata inda muke tazo ta samemu, tana zuwa tasa mata kuka "wai yan' dakin sune idan ta kwanta suke shashshafata, takai kararsu amma sunce ba zasu daina ba sai dai tabar dakin" karshen abin kuma dole dai tabar dakin. Wai ace 'ya'yan hausawa musulmi ne suke kungiyoyi na madigo a jami'oinmu tun suna boyewa wai har sun daina, kiri kiri yarinya zata nunama ita' yar Lesbian ce. waiyazubillah. Sunmata cewa babu tantirai sai wada suke aikata mumunan aiki kuma Duke bayyanwa SUNY. Yanzu ace a jami'oinmu in yarinya tashiga kafin namiji daya yayi ko...

JIYE MIN MAGANAR NAN SHIN WAI DA GASKE NE MATA SUNFI MAZA SON AURE????

MUN FI MAZA SON AURE "Ni ban san me ya sa maza ba sa son yin aure ba, ki duba sai a yi shekara ba a yi aure a unguwarmu ba, kuma ga 'yan matan muna da yawa, su kuma samarin sun ki yin koda dan tayin nan ne ma, kin san fa MUN FI MAZA SON AURE....". "Kin ga idan zan samu Miji wallahi na hakura da karatun, daman neman Miji ne ya kai ni, koda dan Ustaz ne kuwa". Wannan firar ce ta ja hankalina a dazu da wasu 'yan mata suke yi. Don haka ita ce matashiyar maganata a yau. Da yawa cikin Mata suna so su ji Saurayi ya fara tayin kawo kudin zance ko tambaya gidansu, musamman a lokacin da suka ga ana hada-hadar auren wata cikin kawayensu, sauran kuma har yanzu empty. Kuma nan take su yi kokarin sakkowa farashin kasa ko su ma sa samu wanda zai taya. Kamar yadda Mata ke matukar son Aure; haka Maza ma ke son Aure, kowa na son Aure. Sai dai inda matsalar take amincewar Mace ga wanda ya bijiro mata da sunan Aure. Da yawan cikin Mata sukan bai wa wanda ke son Aurensu gwale-gw...

DRAGON STYLE IN FACEBOOK

Image
[[1416434548593449]] [[1416434691926768]] [[1416434828593421]] [[1416434935260077]] [[1416435078593396]] [[1416435155260055]] [[1416435215260049]] [[1416435325260038]] [[1416435438593360]] [[1416435511926686]] [[1416435611926676]] [[1416435661926671]] [[1416435751926662]] [[1416435971926640]] [[1416436085259962]] [[1416436211926616]] [[1416436311926606]] [[1416436421926595]] [[1416436578593246]] [[1416436808593223]] [[1416437021926535]] copy and paste to your status update

RUBUTA SUNANKA MAI STYLE A FACEBOOK.

[[175439099301489]] a [[175439199301479]] b [[175439602634772]] c [[175440839301315]] d [[175440882634644]] e [[175441022634630]] f [[175441165967949]] g [[175441239301275]] h [[175441289301270]] i [[175441332634599]] j [[175441605967905]] k [[175441712634561]] l [[175441992634533]] m [[175442382634494]] n [[175442552634477]] o [[175442625967803]] p [[175442732634459]] q [[175442825967783]] r [[175442942634438]] s [[175443035967762]] t [[175443089301090]] u [[175443252634407]] v [[175443315967734]] w [[175443439301055]] x [[175443529301046]] y [[175443609301038]] z shi Kuma flat ne

RUBUTA SUNANKA CIKIN STYLE A FACEBOOK

Image
[[175443755967690]] a [[175443852634347]] b [[175443892634343]] c [[175443932634339]] d [[175444019300997]] e [[175444129300986]] f [[175444202634312]] g [[175444292634303]] h [[175444355967630]] i [[175444412634291]] j [[175444462634286]] k [[175444639300935]] l [[175444749300924]] m [[175445025967563]] n [[175445109300888]] o [[175445239300875]] p [[175445379300861]] q [[175449672633765]] r [[175451449300254]] s [[175452515966814]] t [[175454065966659]] u [[175457029299696]] v [[175458032632929]] w [[175459712632761]] x [[175461015965964]] y [[175461065965959]] z shim a wannan iri hoton sama zaibayar kowane alphabet try it. Note:kada a manata a inda kake rubuta status naka zaka sa.

SA SUNANKA A CIKIN CIRCLE A FACEBOOK TA DA WANNAN CODE

Image
misali kamar haka duk alphabet da ka dauka haka zai zama. [[268042140001833]] A [[268042716668442]] B [[268043013335079]] C [[268043276668386]] D [[268043510001696]] E [[268043736668340]] F [[268044026668311]] G [[268044343334946]] H [[268044903334890]] I [[268045263334854]] J [[268045443334836]] L [[268045753334805]] M [[268045966668117]] N [[268046153334765]] O [[268046510001396]] P [[268046840001363]] Q [[268047516667962]] R [[268047900001257]] S [[268048106667903]] T [[268048353334545]] U [[268048616667852]] V [[268048816667832]] W [[268049130001134]] X [[268049363334444]] Y [[268049560001091]] Z

GIRMAN KAI KASHI NA TAKWAS 8

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 4- Mulki ko Sarauta Mulki ko sarauta kan sanya mutum yin girman kai da wulaqanta mutane da mayar da mutane bayinsa kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya ba mu labarin Fir'auna, wanda giyar mulki ta dauke shi ya zama mai girman kai da dagawa da mayar da mutane bayinsa; ya kashe wanda ya kashe ya raya wanda ya raya, ta kai shi har sai da ya yi da’awar allantaka, kamar yadda Allah (swt) ya ce: "Fir’auna ya yi shela a cikin mutanensa ya ce: Ya ku mutane na, shin ba ni ne nake da mulkin Misra kuma wadannan qoramun su ke gudana ta qarqashi na ba? Shin ba kwa gani ne? Shin baku ganin ni ne fiyayye ba wannan wulaqantaccen da ko kusa ba ya iya bayayyana magana ba?" - (Suratu Zukhruf, aya ta 50 -51). Wannan ayar tana nuna yadda Fir'auna ya yi girman kai da alfahari da wulaqanta Annabi Musa (as), sabo...

FANKE

abin bukata filawa kofi 2 kofi 1 1/2 na ruwan dumi ckb 1 na yis 1/2 na sikari kc 1 na gishiri vanilla don dandano albasa kankararriya yadda za ayi a zuba yis cikin ruwan dumi don ya narke sai a zuba akan filawa tare da sikari,gishiri da vanilla a kwaba su baki daya yayi dan tauri a sami wuri me dumi a ajiye don ya tashi a sami kamar aa daya. a dora mai a wuta idan yayi zafi sai kisa hannunki ki dinga yankowa kina sawa a cikin man. idan ya soyu zaki ga ya zama ruwan kasa.za a iya ci da shayi ko kunu ko lemo. kada amanta kwabin kada ya zama ruwa-ruwa ko tauri.

FINA FINAN BATSA [BLUE FILMS]

FINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS) Blue Films fina finai ne da wasu tsageru daga cikin Yahudawa suke shiryawa wanda yana da illa sosai. Domin yanzu anyi ittifakin cewa ba abinda yake saurin rufta mutum zuwa zinace-zinace kamar shi kallon Blue Film din wanda zamani yazo dashi baga namiji ba ba kuma ga mace ba. Babban abin takaici yanzu yan mata sunfi kowa kwarewa wajen iya kallon wannan lalaci na Blue Film. HUKUNCIN SA: Kallon tsaraici haramun ne a shari'ar musulunci in banda na matarka ko na mijinki ballantana kuma kallon saduwa tsakanin Mazinata wannan abune mai matukar muni sosai. Allah yana cewa: "Ka gayawa muminai maza su rintse idanuwansu daga kallon haram kuma su kiyaye farjinsu daga yin zina. Yan uwa mu kiyaye, duk wanda yake kallon irin wandannan abubuwa to lalle yayiwa Allah tawaye. A wani gurin Allah yana cewa:- Kada ku kusanci zina hakika ita zina Alfasha ne kuma mummunan hanyace. Kunga saboda halakar da take cikin zina sai Allah yace kada mu kusan ceta, shi kuwa irin wa...

WATA HIKAYA MAI MAANA

HIkAYA Wani bature ne ya musilinta kuma ya lizamci karatun Qur'ani Sai wani dansa da ba musilmi ba yake tambayarsa"babakulum kana karanta Qur'ani kuma kai bakajin larabci bakasan me kake cewa ba menene amfanin hakan??" Idan yacemai akwai lada bazai fahimta ba tinda kafiri ne. Sai yayi amfani da hikimar da Allah yabashi ya dauki wani dostbin♻ wanda fari ne amma gawayi yabatashi yacema dannan nasa yadebo mai ruwa aciki sai dan yace"yaza'ayi kwando yadebi ruwa??" Baban yace tayarda nake fahimtar Qur'ani Sai dan yaso ya gwada yagani yayi yunkurin dibar ruwa da kwando har kusan sau 10 amma yaki debowa sai yadawo yace yakasa Sai baban yace to bakaga kwandon yayi haske ba sai mamaki yakama dan sai baban Yace " HAKA DUK WANDA YA LIZIMCI KARANTA QURAN ZUCIYARSHI ZATAYI HASKE KODA BAYA FAHIMTAR MA'ANAR SA" ALLAHUMA JA'ALNA MIN MAN YAQARA'AL QURANA WA YARDA WALATAJA'ALNA MIN MAN YAQARA'AHU FAYADILLA WA YASHKA

SHINKAFA DAFADIKA MAI KWAI

Abin bukata ruwan kwakwa kofi 5 shinkafa gwangwani 3 timatir manya 5 timatirin gwangwani 1 mai madaidaici kanunfari kc1 gishiri don dandano ganye bay kadan albasa attaruhu kadan tafarnuwa yadda za ayi A dafa ruwan dumi a zubawa shinkafa kafin a dafa ta. A jajjaga attaruhu tare da tafarnuwa. asa mai a wuta idan ya soyu sai a zuba jajjagaggun kayan miya a kawo timatirin gwangwanin nan a zuba akai su soyu gaba daya idan sun soyu sai a zuba ruwan kwakwan nan akai tare da ganyen bay. Daya tafaso sai a wanke shinkafa a zuba a rufe ta idan ana so a hada ta dankalin turawa a zuba mata gishiri daidai gwargwadon bukata. Idan ta dahu za a iya cin ta da naman kaza soyayyaye ko kifi. wannan dafadukar wata nauin dafaduka ce da babbain ta da wanda aka sani shine ruwan kwakwa da aka sa. a wasu kashen afrikan ake yinta kamar cameroun kuma ana girka ta da nama amma wannan na bada zabi za a iya anfani da abin da ake bukata.kamar wanda basa cin nama zasu iya anfani da wannan hadin.

Hanyar bude layi wanda aka rufe

YADDA ZAKA BUDE SIM DINKA WANDA AKAYI BLOCKING. (UNBLOCK-SIMCARD) Bi wadannan matakan => ka sanya layin naka wanda akayi blocking din nasa a cikin waya, => Daga nan sai ka cire layin sannan sai ka kashe wayar. =>sai kuma ka kara sanya layin again, daga nan sai ka kunna waya , ka danna wannan code din: *22233421# bayan wannan => sai ka danna sabon pin din da kake bukata.

LABARIN BAFFULATANI DA BARAWO

Wani Dan fulani ne kullum a gona sai anyi masa sata. sai watarana yace bari na buya ko zan kama barawon. Can kawai saiga barawo yazo ya debi kaya zai tafi sai danfulani yakamashi yace yau akwai lugude a ruga. suna cikin tafiya sai barawon yace ya manta takalminsa sai danfulani yace yi gudu kaje ka dauko ina jiranka shiru shiru barawo bai dawo ba,sai dan fulani ya tafi gida, yaje yana bawa baffansa labari sai baffan nasa yace, amma kai akwai sakarai maimakon kace ya tsaya kaje kadauko masa. Wai da dan fulanin da baffan nasa wane yafi wani sakarci a cikin su ??

GIRMAN KAI KASHI NA SHIDA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 3- Ilimi: Ilimi yakan sanya mutum girman kai da alfahari da jiji da kai da wulaqanta wadansu. Yin haka kuwa asara ne da tabewa, kamar yadda magabata na qwarai su ka yi nuni a cikin maganganunsu: Imam Ibn Abdus (sunansa: Al Imam al Hujja, Abu Ahmad Muhammad bn Abdus bn Kamil Assiraj Assulami Albagdadi, ya yi ruwaya daga Aliyu bn al-Ja'ad da Imam Ahmad da Abubakar bn Abi Shaiba da sauransu. Daga cikin dalibansa kuma akwai imam Addabarani da wasunsa, ya rasu a shekara ta 293 bayan Hijira) ya ce: "A duk sanda mai ilimi ya sami girma da daukaka, to, jiji da kai ya fi saurin zuwa gare shi, sai dai wanda Allah ya kare shi da datarwarSa, kuma ya cire son shugabanci daga ransa." - (Ibnu Abdil Barri ya rawaito shi, Jamiu Bayanil Ilmi wa Fadhlihi, lamba ta 962 juzii na 1 shafi na 569, bugun Daru Ibnil Jau...

GIRMAN KAI KASHI NA BIYAR

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 2- Arziki ko yawan dukiya: Su kan sanya mutum girman kai da ji-ji-da-kai da alfahari da wulaqanta wanda ba shi da shi kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya ba mu labarin Qaruna da dukiyar da yake da ita da dagawar da yake yi wa alummarsa. Allah (swt) ya ce: “Haqiqa Qaruna ya kasance daga cikin mutanen annabi Musa sai ya yi mu su dagawa. Mun ba shi taskoki (ma su yawa) wadanda makullansu su kan yiwa jama'a ma su qarfi nauyin dauka. Ya yin da mutanen sa su ka ce ma sa, kar ka yi GIRMAN KAI, da alfahari domin haqiqa Allah ba ya son ma su girman kai da alfahari." - (Suratul Qasas, aya ta 76). Wannan ayar ta nuna mana cewa, Allah madaukakin Sarki wanda ya halicce mu kuma ya ke da cikakken arziki, kuma ya ke bayar da arziki ga wanda ya ga dama ya hana mu yin girman kai da alfahari da dagawa akan dukiyar d...

mayar da rubutu blue a facebook wanda basai kayi amfani da # ba

domin mayar da rubutunka blue a Facebook kayi amfani da wannan code din. @@[1:[0:1: Rubuta abin da kake so anan ]]

FACEBOOK HAPPY BIRTHDAY CODE STYLE

1. [[175464589298940]] [[175464659298933]] 2. [[175464752632257]] [[175464975965568]] 3. [[175465069298892]] [[175465152632217]] 4. [[175465259298873]] [[175465385965527]] 5. [[175465475965518]] [[175467689298630]] 6. [[175467805965285]] [[175467895965276]] 7. [[175468245965241]] [[175468305965235]] 8. [[175469495965116]] [[175469632631769]] 9. [[175470122631720]] [[175470292631703]] 10. [[175473399298059]] [[175473495964716]] 11. [[491132910979467]] [[189507867925520]] Examples Click to see sample Click to see another sample NOTE: Number 4 is be long to Christian birthday because it include with cross +. So Muslims be careful.

Sako Daga kishiya by Umar

Sako daga kishiya by UMAR . . Salam sako ne daga kishiya, Haba 'yan uwana mata meyasa Bakwa so nane ? Duk wadda akace za'a kawo mata Ni sai tace bata so na, Wayyo ni kishiya ina zansa kaina Ne 'yan uwana mata, Haba 'yan uwana mata kuyimin Waje a gidajenku mana, Kona samu wajan da zanyi baje koli na, Wallahi bazan gallabe kuba daku Da yaran ku, 'Yan uwa na mata dan Allah kudaina gudu na mana, Wayyo ni kishiya ina zansa kaina Ne, Nasan wata zataji tausayi na ta yimin waje a gidanki kawai, Kinga saikin gwada sannan zaki gane ina da amfani a gidanki, Nidai kutaimaka mini nasamu waje Na daina yawo agari haka,

YADDA ZAKAI RECHARGING[SAKA KUDIN WAYA] NA LAYINKA DA KUDINKA NA BANKI A DUK INDA KAKE DA WAYARKA.

YADDA ZAKAI RECHARGING[SAKA KUDIN WAYA] NA LAYINKA DA KUDINKA NA BANKI A DUK INDA KAKE DA WAYARKA. Sauki ne wannan ga masu account a banki saboda matsalar rashin katin waya a wani gurin to ga hanya tazo da ko a daji kake kuma kana da account a banki zaka iya recharging din wayarka muddin akwai network a gurin. NOTE:-ka tabbatar layin da yake way ark a da shi ka bude account din bankinka. 1.GUARANTEE TRUST BANK. 737 amount# 2.FIRST BANK. 894 amount# 3.FIDELITY BANK. 770 amount# 4.ACCESS BANK. 901 amount# 5.STERLING BANK. 882 amount# 6.FIRST CITY MONUMENT BANK[FCMB]. 389 214*1*amount# 7.WEMA BANK. 332 035*amount# KARIN BAYANI:~wajen da nake sa "amount" ina nufin lambar adadin kudin da kake bukata.

GIRMAN KAI KASHI NA HUDU

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? AMSA: Sabubban da su ke kawo girman kai da ji-ji-da-kai su na da yawa, amma ga mafiya shahara daga cikin su: 1. Alfahari da asali 2. Yawan dukiya 3. Ilimi 4. Mulki ko sarauta 5. Qarfi 6. Yawan mabiya 7. Fasahar harshe 8. Yawan ibada 9. Kyawun halitta. Ga bayananasu kamar haka: 1- Asali: Yakan sanya mutum yin girman kai, imma asalin jinsi ko na iyaye ko na qabila. Asali jinsi: Dalilin mu na cewa asalin jinsi ya kan sanya mutum yin girman kai shi ne: Abin da ya faru tsakanin Iblis da Annabi Adam (as) yayin da Allah (swt) ya umarce shi da ya yi wa Annabi Adam sujjada sai ya qi. Allah (swt) ya ce: "Sai Allah ya ce, mene ne ya hanaka yin sujjada ga abin da na halicce shi da hannu na? shin girman kai ka yi? Ko ka kasance a cikin ma su dagawa (ne)? Sai ya ce: Ni na...

LABARIN WANI ATTAJIRI.

Wani attajirine yayi niyyar rabawa masu karamin karfi ragunan sallar layya, saiyaje wani masallaci yasa aka ajiye ragunan abayan masallaci,anayin sallamar sallah sayya mike yace ina mutun daya me tsoron Allah? sai wani ya daga hannu,sai yace bisimillah, sai suka fita bayan masallacin aka yanka masa rago akace ya dauka ya wuce gida saiya dawo cikin masallacin yace ina wani me tsoron Allah,wani ya sake daga hannu shima sukaje aka yanka masa shima ya dauka yatafi gida akaro na uku sai mutumin ya manta yashiga da wukar kuma ga jini ajikinta yadawo masallacin yace ina wani me tsoron Allah? suna ganin wukar a hannunsa da jini kuma sun lura da duk mutanenda ya kira basu dawoba sai sukayi tsit kowa yakasa daga hannu can sai ladan yace, saidai ko liman shi yafi kowa tsoron Allah, da sauri liman yace inji uwarwa??

BABBAN TASHIN HANKALIN!!!!!!!!!!!!!

BABBAN TASHIN HANKALI!!! . . . Hadisi ne zan karanta muku Amma ina neman alfarma guda awajenku kafin ku karanta hadisin nan... Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau. . . Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Qarshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya. Yazeedur Raqqaashiy ya karbo hadisin daga Anas bn Malik (ra) yana cewa: . . Watarana Mala'ika Jibreelu (as) yazo wajen Manzon Allah (saww) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba. Yazo, gaba dayan launin fuskarsa ya chanza. Sai Manzon Allah (saww) yace masa "MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CHANJA HAKA?". . . Yace "Ya Muhammadu (saww) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta. . . Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Qabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamat...

GIRMAN KAI KASHI NA UKU.

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 3: Shin yin TSAFTA da yin ADO yana cikin girman kai? AMSA Yin tsafta da yin ado da saka tufafi ma su kyau ba ya cikin girman kai. Barima musulunci ya kwadaitar da yin tsabta ta gangar jiki da ta tufafi da muhalli kamar yadda ya zo a fadar Allah (swt) Suratul Muddassir aya ta 4. Wasu daga cikin malaman tafsiri sun fassara ta da cewa: "kuma ka tsarkake tufafinka”. Haka kuma ya tabbata cewa manzon Allah (saw) ya fi kowa tsafta, ya kasance mai yawan yin asuwaki, kuma ya umarci al'ummarSa da yin aswaki da tsabtar gangar jiki da yanke farce da cire gashin hammata da na mara da rage gashin baki da yin shayi (kaciya) da sauransu. Kuma ya umarci alummarSa da yin wanka da sanya tufafi ma su kyau da sanya turare. Ya kuma kasance yana hani ga warin jiki da warin baki da abin da ya ke jawo su; kamar cin Tafarnuwa da danyar Albasa, da rashin yin askin hammata da duk abin da zai janyo doyi ...

WAYE A DUNIYA KAFIN ALLAH

WAYE A DUNIYA KAFIN ALLAH? . Wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani jarumi kuma kafirin mutum, ga tsananin karfi ga zalunci da mugunta. . Wata rana wannan kafiri ya fito yana yawo a cikin gari, sai yaji wani Malamin Musulmi yana wa'azi, saboda dadin wannan wa'azi na Malamin yasa mutane suka taru sosai don saurarensa. . Ko da wannan kafiri ya iso wurin, sai yayi ihu mai razanarwa, har sai da kowa da yake a wurin ya tsorata, sannan yace; Na zo maku da wata tambaya daya da nake so ku amsa mani, duk wanda ya amsa ta daidai daga cikin ku zan bashi dukiya ta tare da zama bawansa, kuma zan kasance acikin addininku, Mai gasgata shi. Tambayar ita ce; WAYE A DUNIYA KAFIN ALLAH? Tare da hujja mai karfi. .. Duk mutanen dake a wurin suka kasa bashi amsar wannan tambaya. . Sai wani yaro karami ya fito yace: zan amsa maka tambayar ka amma nima sai ka fara amsa tambayar da zanyi maka yanzu, idan har ka amsa daidai to nima zan baka amsar tambayar ka. . Mamaki ya cika wannan kafiri ganin c...

NIMA AURE NAKESO.

KEMA AURAN KIKE SO Nakan sha mamaki a duk lokacin da na ji mata suna tattauna maganar da ta shafi Aure, musamman idan na ji sun zake wajen nuna bukatuwarsu ga Auren. Jiya ma haka na ji yan Mata uku suna tafiya suna maganar Auren wata kawarsu da ya gabato, ba wai maganar irin hidimar da suka tanadarwa bikin ba ce abinda ya ja hankali na, a'a, kokawar da dayarsu take yi dangane da rashin samun tsayayyen saurayin da yake sonta da gaske kuma zai aure ta. "Ki duba yadda nake da kyau, kuma ina da kokarina daidai gwargwado, amma wai har WANCE........ ta samu Mijin Aure ni kuwa shiru, wallahi da akwai yadda zan yi a fasa Auren in ya so kowa ya rasa da zan yi". Sai dayar ta ce: "Da ni fa ya nuna yana so amma ban ba shi fuska ba saboda na ga ba kala ba ne, ga shi na tsaya kallon ruwa kwado ya min kafa. Kuma kin san abinda ya fara hada mu da shi, wai ni zai yiwa wa'azi na daina kula samarin ajinmu". Sai ta ukun ta ce: "Ku dai kawai ku yi fatan Allah ya ba su zaman...

Rashin Nasara A Kan Boko Haram Ba Zai Sa Ni Yin Murabus Ba Daga Mulki, Inji Buhari

Rashin Nasara A Kan Boko Haram Ba Zai Sa Ni Yin Murabus Ba Daga Mulki, Inji Buhari . . A wata tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da kafar yada labarai ta Al Jazeera, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta kawar da 'yan kungiyar Boko Haram nan da karshen wannan shekara, amma kuma ya kara da cewa za su iya yin zaman sulhu da 'yan kungiyar domin sako 'yan matan Chibok. . "Muna bukatar su tabbatar mana da cewa suna nan a raye, kuma cikin koshin lafiya, to za mu iya tattaunawa da su. A shirye muke da yin zaman sulhun idan har mun tabbatar 'yan matan Chibok din suna nan a raye". . Shugaban kasan ya bayyana cewa za su yi nasara a kan Boko Haram nan da karshen wannan shekara, inda ya fadawa kafar yada labaran ta Al Jazeera cewa "kafin nan da karshen wannan shekara za mu kawar da Boko Haram, wanda kuma hakan zai zama karshensu. Harin da suke kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ya kusa kawowa karshe". Idan ba mu yi nasara a kan Boko Haram ba...

LABARINA

Ido 4 mukayi da ita wallahi ban gane ta ba ashe itace???? Tun a first semester da muka hadu a layin registration bamu sake haduwa ba sai a level 200 naje e-library inyo printing na wata paper kai wai kunsan menakeson fada makune? Hmm watoh yarinyar ta hadu but inda ta bata kanta shine wallahi tana shafe-shafe duk fuskarta fodane wani murmushi data Taimin ai nan take na shiga kyarma ina yaqe da wasu wasi a zcyta ni banaso ta zo inda nake dalilina shine ina tsoron yan matan higher level shiyasa i just believe in friendship ko ya kukace??

GIRMAN KAI KASHI NA BIYU.

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. Tambaya Ta 1: Mene ne GIRMAN KAI da JIJI DA KAI? AMSA: Girman kai shi ne qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane. Wannan ma'ana ta zo a cikin hadisin Abdullahi bn Masud (ra) cewa wani mutum ya tambayi manzon Allah (saw) game da girmankai sai, manzon Allah (saw) ya ce: “Girman kai shi ne qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane”. - (Sahihu Muslim:167). Shi kuwa jiji da kai shi ne mutum ya riqa alfahari da taqama da fankama da baiwar da Allah ya ba shi ta asali ko ilimi ko sarauta ko kyawun halitta ko yawan dukiya da sauran su. Tambaya Ta 2: Girman kai nau'i nawa ne? AMSA: Girman kai naui biyu ne: 1. Girman kai na kafurci. Misalinsa shi ne girman kan da Iblis ya yi wa Allah (swt). Da kuma kafurai da su ka kafircewa Allah da Annabawa. 2. Girman kai na sabo. Wannan shi ne mutum ya riqa qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane. Sai mun hadu a fitota 03 da yardar Allah Allah yasa mudace. Ameeeeen

Kuduba Wannan

GIRMAN KAI

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. GODIYA Dukkan godiya da yabo da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah wanda ya siffantu da girma da qasaita. Ina gode ma sa godiya mara adadi, domin shi ne ya can-can-ci yabo a farko da qarshe. Ina qara godiya ga re shi (swt) wanda bisa rahamarSa ne ya bani ikon rubuta wannan littafi mai suna: GIRMAN KAI, SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Ina salati da sallama ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (saw) jagoran ma su qanqan da kai. Tsira da amincin Allah su tabbata a gareShi da AlayanSa da sahabbanSa da wadanda su ka biyo su da kyautatawa. Bayan haka, wannan littafi ne da ya qunshi bayani game da girman kai da abubuwan da su ke jawo shi da bayanin hadarinsa da kuma hanyoyin da za a magance shi. Wanda Malaminmu Shaikh abdulwahhab Abdallah bn Muhammad ya wallafa game da wannan babbar cuta kuma Mallam ya yi bayani mai gamsarwa bisa dogaro da ayoyin Alqur'qni da ingantattun hadisai waje...

SOYYAYA A PRISON

 SOYAYYA A PRISON Labarin Wata budurwa da akayiwa sharri kisan kai, akaje kotu Alkali ya yanke mata hukuncin daurin rai da rai prison. Aka kai ta prison bayan ta shiga bata da wani aiki sai kuka, ana nan sai wani mutum da yake aiki a prison din, aikinsa kawai idan mutum ya rasu yazo yayi dawainiyar sanya mamacin a akwatu a rufeshi. Sunnan aje a bunne gawar. Kullum sai ya ganta tana kuka har watarana yaje ya tambayeta ta kwashe Labarin ta kaf tagaya masa, tace kuma kukan da takeyi kako yaushe idan ya shigo sai yazo wajenta sun gaisa yana dai dan debe mata kewa, har soyayya ta shiga tsakanin su sosai har suna cewa ba wanda ya isa ya rabasu Tab. Sai dai kuma tayaya xasuyi auren? Wata rana suna hira sai tace yakamata mu san yanda zamuyi na kubuta muje muyi Aure sai yace mata to yaza ayi, sai ta bada shawara cewa IDAN ANYI MUTUWA A GIDAN ZATA JE TA SHIGA CIKIN AKWATIN DA GAWAR TAKE IDAN YAZO SHI DA YARANSA SAI YA RUFE KAWAI IDAN AKA BINNE SU SAI YAJE DAGA BAYA YA TONE TASU GUDU, ya amsa ya...