MUHIMMANCIN HAKURI

MUHIMMANCIN HAKURI

IMRAN BN HUSAIN yana daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww). Allah ya jarabceshi da ciwon Basur.

Da yayi hakuri ya jure wannan jarrbawar sai Allah yayi masa wata baiwa. Wato ya kasance duk inda yake sai Mala'iku su rika zuwa suna gaisawa dashi.

Yana cikin wannan yanayin, rannan sai yaje yasa akayi masa wata tsaga saboda maganin Basur din. Sai kuma ya lura da cewa tun da ya magance chutar, Mala'ikun nan sun dena zuwa gaisheshi.

Don haka ya dukufa da addu'a yana rokon Allah ya dawo masa da basur din. Nan da nan sai Basur ya dawo, Kuma Mala'ikun ma suka ci gaba da zuwa gaisheshi.

Wannan labarin yana karantar damu muhimmancin yin hakuri abisa duk wata jarrbawar da mutum ya tsinci kansa aciki.

Watakil Allah ya jarrabeka ta hanyar Jinya, ko Talauci, ko damuwa tsakaninka da abokan aikinka, ko matarka. ko tsakaninki da Mijinki ko Kishiyarki, ko tsakaninka da abokan zamanka, Ko iyayenka, ko 'ya'yanka, ko makobtanka.

To amma idan ka jure ka mayar da lamarin zuwa ga Allah, sai ka samu babbar kyauta tun daga nan duniya, sannan aranar lahira Allah ya girmamaka da babban matsayin da baka taba tsammani ba.

Ya Allah ka Qara mana hakuri bisa abinda ka jarrabemu dashi, Kar ka dora mana abinda ba zamu iya jurewa ba.. Kuma ka bamu ikon cin jarabawar.

Ameeen.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA