JIYE MIN MAGANAR NAN SHIN WAI DA GASKE NE MATA SUNFI MAZA SON AURE????
MUN FI MAZA SON AURE
"Ni ban san me ya sa maza ba sa son yin aure ba, ki duba sai a yi shekara ba a yi aure a unguwarmu ba, kuma ga 'yan matan muna da yawa, su kuma samarin sun ki yin koda dan tayin nan ne ma, kin san fa MUN FI MAZA SON AURE....".
"Kin ga idan zan samu Miji wallahi na hakura da karatun, daman neman Miji ne ya kai ni, koda dan Ustaz ne kuwa".
Wannan firar ce ta ja hankalina a dazu da wasu 'yan mata suke yi. Don haka ita ce matashiyar maganata a yau.
Da yawa cikin Mata suna so su ji Saurayi ya fara tayin kawo kudin zance ko tambaya gidansu, musamman a lokacin da suka ga ana hada-hadar auren wata cikin kawayensu, sauran kuma har yanzu empty. Kuma nan take su yi kokarin sakkowa farashin kasa ko su ma sa samu wanda zai taya.
Kamar yadda Mata ke matukar son Aure; haka Maza ma ke son Aure, kowa na son Aure. Sai dai inda matsalar take amincewar Mace ga wanda ya bijiro mata da sunan Aure.
Da yawan cikin Mata sukan bai wa wanda ke son Aurensu gwale-gwale musamman idan sun ga suna da Samari fiye da guda, kowa yana da ranar firarsa, in an yi rashin sa'a ta tashi a tutar babu. Da Magidanci zai bijirowa yarinyar da yake son 'kara aura, sai ta fara gindaya masa wasu sharudan da idan ba a yi sa'a ba sai dai su rabu, duk da irin soyayyar da suka kwasa.
Wata za ta bukaci sai dai a raba musu gida da Uwargidan, ta yadda in bai da hali sai dai ya hakura. Uwargidan da za a wa kishiya kuwa, nan ma wata balahirar ce, domin yadda aka yi wa amarya kayan lefe, wai ita ma haka za a yi mata, ba tare da duba talauci na mijin ba, har suna cewa: "Ai duk wanda ya nemi karin Aure yana da shi ne".
Idan kuwa sabon Aure ne, kuma an yi sa'a har Budurwar ta amince, to ita da kanta za ta tsara kayan lefen da Mijin zai sayo mata, a wani lokacin ma da ita za a je a sayo kayan, koda kuwa bai da halin sayen wadannan kayan, to ta gwammace ya ci bashi; idan ya so bayan Aure ya fara rigimar biyan bashi.
Haka batun gidan da za su zauna ma, nan ma idan bai mata ba, wata sabuwar matsala ce.
A wasu lokutan iyaye mata ne ke katsalandan a harkan gidan da mai Auren 'yarsu zai kai ta. Abin takaici, a dalilin rashin wadatattun dakuna, sai ka ga an fasa yin aure da da'awar wai dakin ba zai dauki kayan jere ba.
Abinda iyaye ba su fahimta ba kuwa, ana zaman Aure da Soyayya koda babu kayan alatu, amman kayan alatu ba sa zaunar da Aure matukar babu soyayya.
Rena sana'a ko jarin mai neman Aure suna taka muhimmiyar rawa wajen zagwanyewar aure ko yawaitar mata a rasa mai aurensu.
Da wani mai karamar sana'a zai zo neman Auren wacce ta kammala Digiri (Degree), zai yi wuya ta saurare shi domin tana ganin ta wuce ajinsa, musamman ma idan bakinsa sakandare (Secondary) ko Difloma (Diploma).
To ire-iren wadannan dalilai da wadansunsu, wadanda buri da son zuciya ya musu ja-gaba, su suke kawowa mazajen suna shayin taya Aurensu koda kuwa sun gani suna so.
Amman tabbas Maza na son Aure sosai da sosai.
Comments
Post a Comment