HATTARA DA AIKIN MUTANEN ANNANBI LUT
HATTARA DA AIKIN MUTANEN LUT HUDUBA DAGA MASALLACIN ABU HURAIRA (RA), SOKOTO A KAN HATSARIN LUWADI
Bismillahir Rahmanir Rahim Hudubarmu ta yau tana magana ne game da wata barna da ta bayyana a cikin wannan alumma ta manzon Allah (S) wadda a asalin halittar yan adam ba a san ta ba, amma kwatsam ta taba bayyana a cikin wata alumma ta mutane, Allah (SWT) bai yi masu jinkiri bayan an yi musu waazi sun ki saurare ba, take sai Allah (T) ya share su daga doron kasa. Allah ya aiko malaiku suka yi mu su azabar da ba a taba wa dan adam ita ba. Allah ya aiko malaiku suka shafe idanunsu, sannan suka jirkitar da kasa a kan su, sannan aka yi masu ruwan duwatsun azaba. Wannan barna da suka aikata ta sake bacewa daga doron kasa illa ma sha Allah.
Kuma sai Allah (Swt) ya kawo mana labarinsu a cikin surori tara na Alkurani:
(Suratul Aaraf:80-84, Hud:77-83, Hijr:57-77, Anbiya:74-75, Shuara:160-175, An- Naml:54-58, Ankabut:28-35, Saffat:133-138 da kuma Suratul Qamar:33-39).
Sannan sai manzon Allah (Saw) ya bayyana cewa, wannan balai da wadancan mutanen suka aikata zai sake bayyana a cikin wannan alumma. Amma kuma a duk tsawon rayuwarsa (S) ba a ji duriyar wannan fasadi ba a ko ina. Duniya tana tafiya, zamani na kara nisa, wannan alfasha ta bayyana a kasashen kafirai. A hankali ta rarrafo zuwa cikin fasikan musulmi. Yau da gobe tun ana boye ta har aka fara bayyana ta. A hankali a hankali sai ga maabota wannan alfasha suna kafa kungiyoyi masu zaman kansu, suna fira da kafafen yada labarai, suna fitowa jerin gwano don bayyana raayinsu. Kai, a wasu kasashen ma har an fara yin doka don kariyar yancinsu ga aikata wannan alfasha kuma a ba su dama su yi bukin tabbatar da ita a bainar jamaa. Sannan ana son wai mu ma mu bi sawun masu nema masu yanci. Ya ku bayin Allah, wannan alfasha da mummunan aiki wanda Allah yake yin fushi da masu yin sa shine aikin mutanen annabi Lut (AS). Ba domin yin fadakarwa daga barna ya zama wajibi ba.. Ba domin alamun wannan fitina sun fara bayyana cikin jamaar musulmi ba.. Ba domin Allah (TWT) ya ja kunnen mu daga wannan mugun aiki cikin alkurani ba, kuma manzon Allah (S) ya sha tsoratar da alummarsa daga wannan mugun aiki ba.. da ba zamu taba ambaton wannan shashanci a kan mimbari ba. Me ake nufi da Luwadi? Luwadi wani aiki ne na kazanta da yake kasancewa a tsakanin namiji da namiji irin shigen abinda yake kasancewa a tsakanin mata da miji ta hanyar dubura (mafitar kashi, matattarar kazanta). An kira shi da sunan Liwadi ne don jingina shi ga mutanen da aka aiko ma annabin Allah Lut (AS), ba don jinginawa ga shi annabin ba. Alhamdu lillah, a yarenmu na Hausa wannan alfasha ba ta da suna, wanda ya nuna cewa, Allah ya kiyaye tarihin iyayenmu da kakanninmu daga wannan kazantar; ba su san ta ba sam. Tun daga lokacin da Allah (SWT) ya saukar da fushinsa a kan mutanen annabi Lut (AS) ne ya kasance idan malaiku suka ga ana yin irin wannan alfasha a bisa kasa sukan gudu su buya zuwa sassan duniya jin tsoron abinda Allah zai hukunta ma mutanen wannan yanki. Kasa da duwatsun da ke a wannan muhallin sukan kai kara ga Allah madaukakin sarki, fatar ko zai ba su iznin su kifar da kasa a kan wadannan mabarnata. Ba zamu yi mamaki ba idan muka ji wata kasa ta yi bukin ba da yancin auren jinsi kamar yadda suke kiran sa a wannan ranar Allah ya aiko masu da girgizar kasa, a matsayin wani gargadi a kan munin abinda suke yi. Illolin Liwadi Wannan bakar dabia; Luwadi tana cikin manyan abubuwan da ke jawo fushin Allah kamar yadda kissar mutanen annabi Lut (AS) take nunawa. Kuma babu shakka tana gaba da Zina wajen muni da hatsari da fusatar da ubangiji. Shehun malami Ibnul Qayyim (almajirin Ibnu Taimiyyah) yana cewa, duk wanda ya ke tadabburin asirran alkurani yana gane cewa, Allah (SWT) ya fi azzama shaanin Luwadi a kan Zina. Domin da madaukakin sarki ya hana Zina sai ya ce:
(( ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻘْﺮَﺑُﻮﺍ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﺰِّﻧَﺎ ﻭَﺳَﺎﺀَ ﻓَﺎﺣِﺸَﺔً ﺳَﺒِﻴﻠًﺎ )).
Amma da ya ambata wannan mugunyar alfasha sai madaukakin sarki ya ce:
(( ﻗَﺎﻝَ ﺇِﺫْ ﻭَﻟُﻮﻃًﺎ ﻟِﻘَﻮْﻣِﻪِ ﺍﻟْﻔَﺎﺣِﺸَﺔَ ﺇِﻧَّﻜُﻢْ ﻟَﺘَﺄْﺗُﻮﻥَ ﺳَﺒَﻘَﻜُﻢْ ﻣَﺎ ﺃَﺣَﺪٍ ﺑِﻬَﺎ ﻣِﻦَ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﻌَﻻَﻤِﻴﻦَ )) .
Kasancewar Zina an kira ta “Fahisha” ba da alif da lam ba ya mayar da ita daya daga cikin manyan zunubai. Amma shi wannan danyen aikin sai aka kira shi “Alfahisha” shine ainihin zunubin wanda ba wani zunubi da ke tarayya da shi. Wal iyazu billah. Haka kuma, da namiji ya kwantar da kai namiji ya yi alfasha da kai gara ya kwantar da kai ya sa wuka ya kashe ka. Saboda me? Mutuwa ba abin kunya ba ce. Kuma kowa ma zai mutu. Watakila ma a sanadiyyar kisan da ya yi ma ka samu shahada, ka gamu da gafarar Allah. To, shi wanda aka lafta ma wancan danyen aiki ai ka ga an lalata ma sa rayuwa, an gurbata shi da kazanta kuma watakila ayi ma sa tukuici da wani mugun ciwo da ba zai bar shi ba har ranar da zai bar duniya. Wannan ita ce hikimar da ta sa Allah ya ba waliyyi zabi idan an kashe ma sa da ko dan uwa in ya so ayi kisasi a kashe wanda ya kashe shi, in kuma ya so ya yafe ya samu lada wurin Allah. Amma su wadannan tozartacci; da na sama da na kasa duk manzon Allah (S) ya ce a kashe su. Wannan ta fuskar addini kenan. A dalilin barin fixirar Allah da yan luwadi suka yi suna fuskantar gurbatar hali da lalacewar dabia iri iri. Sai ka gan su suna da mugunta da rashin kunya da bushewar zuciya da rashin tausayi da raunin himma da karancin kishi. Haka kuma zaka gan su da wauta da karancin tunani da mutuwar zuciya. Saboda wannan mutuwar zuciyar ne zaka ga yana da wahala mai wannan alfasha bai taba yin wani naui na Shirka ba domin a tare suke tafiya, ya-alla ko ya sani ko bai sani ba. Kuma gwargwadon wada wannan kazanta ta kafu a cikin zuciyarsa zai kara kafuwa a cikin Shirka wadda Allah bai gafara ga mai yin ta ranar alkiyama. A nan suna tarayya da Zina. Shi ya sa Allah (T) ya ce game da annabinsa Yusuf (AS):
{ َﻚِﻟَﺬَﻛ ﻟِﻨَﺼْﺮِﻑَ ﺍﻟﺴُّﻮﺀَ ﻋَﻨْﻪُ ﻭَﺍﻟْﻔَﺤْﺸَﺎﺀ ﻣِﻦْ ﺇِﻧَّﻪُ ﻋِﺒَﺎﺩِﻧَﺎ ﺍﻟْﻤُﺨْﻠَﺼِﻴﻦَ { [ ﺳﻮﺭﺓ ﻳﻮﺳﻒ : 24 ]
Wasu daga cikin matsalolin da ‘yan luwadi ke fama da su sun hada da damuwa da matsanancin tsoro. Saboda biyar Allah ita ke sa natsuwa, sabonsa kuwa shi ke kore aminci. Haka kuma suna fama da cin rai da son kadaici da yawan waswasi da rashin tsayuwar raayi da munana zato ga mutane da kuma ganin kamar kowa ya san sirrinsu. A duk lokacin da zaka hadu da mai irin wannan mugunyar dabia abinda sauran mutane yan uwanka ke kallo gare ka ba shi yake kallo ba. Shi ba abinda ya dame shi sai sigar jikinka, launin fatarka, kalar maganarka, yanayin suturarka..
Haka zai rinka waswasai da tunane-tunane a kan ka har sai ya cire suturar da Allah ya yi maka, ya kallo ka tsirara a cikin zuciyarsa. Kana nan kana gaisawa da shi ko kana zantawa da shi alhalin shedan na can ya tsallaka da shi zuwa wata duniya yana wani motsi irin na mai tabuwa baka san ma abinda yake ciki ba. Ta fannin lafiya, babu wata mugunyar cuta da dan luwadi bai iya gamuwa da ita.
A kullum ilimin kimiyya na zamani kara gano wasu manyan curutoci yake yi. Da an ce mi ne ne mafarinsu? Sai ka ji masana sun ce, sun taso ne daga cikin ‘yan luwadi. Wal iyazu billah. Babu shakka manzon Allah (S) ya yi gaskiya da ya ce:
” ﺍﻟﻔﺎﺣﺸﺔ ﻟﻢ ﺗﻈﻬﺮ ﺣﺘﻰ ﻓﻲ ﻗﻮﻡ ﺑﻬﺎ ﻳﻠﻌﻨﻮﺍ ﺇﻻ ﻓﺸﺎ ﻓﻴﻬﻢ ﺍﻟﻄﺎﻋﻮﻥ ﻭﺍﻷﻭﺟﺎﻉ ﺗﻜﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﻓﻲ ﺃﺳﻼﻓﻬﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻀﻮﺍ “.
Alfasha ba za ta bayyana a cikin wasu mutane ba har su rinka bayyana ta face sai annoba da miyagun curutoci sun yadu a cikin su wadanda kakanninsu ba su taba sanin su ba. Ban da miyagun curutoci zaka iske kuma yan luwadi suna fama da wadannan matsaloli:
1. Rashin shaawar mace koda kuwa yana iya saduwa da ita. Daga nan in abin ya yi yawa sai ya kai ma kasawarsa gaba daya ga kusantar iyalinsa in ba zata ba shi dama ya je ma ta a mugun wuri ba.
2. Daga nan sai ya fara kai ga matakin samun raunin mazakutarsa gaba daya ta yadda bai da iko a kan abinda ke fita daga cikin ta. Daga nan sai ya kasa rike abinda ke fita bayansa. To, daga nan kuma curutoci daban daban zasu iya samun kafar kwankwasa kofarsa.
3. Ciwon typoid da na gudawa na cikin wadanda ba su bukatar sallama ga gangar jikinsa saboda dukkansu suna da zumunta mai karfi da kazanta.
4. Sai kuma ciwon Siphilys (ﺍﻟﺰﻫﺮﻱ) wanda aka gano shi tun karni na 15 wanda kuma mutane kawai yake kamawa ta hanyar wata yar karamar kwayar cuta da ba a iya ganin ta da idon dan adam kai tsaye, ana ce ma ta Treponema pallidum. Da farko wannan kwayar cuta za ta kama gaban mai yin wannan danyen aiki da duburar wanda ake wa, sannan a hankali sai ta rarrafa zuwa ga lunsayaininsa, sannan ta wuce zuwa ga hantarsa, ta shiga cikin hanjinsa da sauran kayan cikinsa. Babu kuma irin abinda ba ta iya haifarwa kamar shanyewar jiki da sandarewar jijiya da makanta da curutoci marasa iyaka.
Wannan ciwo yaduwarsa ta fi yawa a kasashen Turai da Amerika saboda karfin yaduwar wannan alfasha a can.
5. Akwai kuma ciwon da ake kira Gonorrea (ﺍﻟﺴﻴﻼﻥ) wanda babu wani ciwon da ya kai shi yaduwa a duniya, saboda a kowace shekara kamar wada WHO ta ce ana samun sama da mutane miliyan 250-500 masu kamuwa da shi a duniya kuma akasarinsu masu matsakaitan shekaru ne. Wannan ciwo idan ya kama wadannan mutane ya kan haifar da kuraje masu kaikayi ga alaurarsu a matakin farko, sannan su fara fidda ruwa masu warin gaske, daga nan sai ya kuntata mafitar fitsari ya mayar da marar mutum jawur. Sai mutum ya rinka fama da wahala wurin fitsari da ciwon kai da raunin jiki. Idan kwayar wannan cuta ta kai ga magudanar jini to a nan kuma sai illa ma sha Allahu.
6. Akwai Herpes. Wani ciwo ne mai ban tsoro wanda maaikatar lafiya ta kasar Amurka ta tabbatar cewa babu maganinsa har yanzu. Kuma an tabbatar da kamuwar sama da miliyan ashirin a cikin kasar ta Amurka da wannan ciwo. Abinda ya sa bakteriyarsa ta fi hatsari shi ne ita kai tsaye take wucewa daga gabban jikin mutum na boye zuwa ga kwakwalwa. Ita kuma kwakwalwa da zaran ta kamu da cuta to kashi 90% ba a warkewa. Kuma kamar yadda wani Dr. Moris yake cewa, bisa ga binciken da suka gudanar a Ingila, mafi yawan masu kamuwa da shi yan shekaru 15 ne zuwa 30.
7. Daga nan sai uwa uba ciwon AIDS abinda aka sani a kasashen faransa da SIDA. Mu kuma nan ana ce ma shi kabari kusa. Ba zamu yi maganar wannan ciwon ba a wannan huduba saboda magana ce mai tsawo. Kuma akwai hukumomi na musamman da aka dora masu alhakin wayar da kan jamaa a kan shi daga matakin karamar hukuma har zuwa ta tarayya. Illa dai kawai zamu yi nuni a nan da cewa, wannan ciwo yan luwadi ne suka yi nakudarsa suka haifar ma duniya shi. Kuma ya zama wata ukuba wadda har ta kan cimma wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba. Lahira tana da hukunci. Allah ka isar muna, ka kare mu, ka jibince mu, ka ba mu ikon kyakkyawan tuba zuwa gare ka.
8. Akwai wani ciwo kuma da yan shekarun nan ya sake bullo ma duniya wanda Dr. kenneth Moor ya ce ya fi AIDS hatsari wurare biyu:
1. A yayin da AIDS ke iya shekara uku yana rarrafe a cikin jikin mutum shi wannan wata shida kacal yake yi.
2. Duk irin alamomin tafi sannu da shiga kwana da sa dogon haske da AIDS yake yi shi ba shi yin su, kwatsam yake bayyana kuma yakashe nan take. Shi ma wannan sun ba shi sunan kwayar cutar masoya kuma ga yan luwadi ake samun shi. Allah muna rokon ka kariya. Hukuncin Yan Luwadi Sahabban manzon Allah (S) sun hadu a kan haddin yan luwadi cewa, shine a kashe su.
Amma sun banbanta wajen wane irin kisa ya kamata ayi ma su? Sayyidina Ali (R) fatawarsa ita ce a kone su da wuta. Kuma sayyidina Abubakar ya mara masa baya a wannan fatawa. Sayyidina Khalid bin Walid ya zartar da ita.
Shi kuma Ibnu Abbas (R) cewa ya yi a haurar da su bene mafi tsawo ko tsaunin da ya fi kowane tsayi a cikin garinsu, sai a turo su daga can, suna isowa kasa sannan a bi su da jifa har a kashe su. Wasu kuma cikin sahabbai suna ganin kawai a sa takobi a kashe su. Wasu kuma su ce haddi za a yi ma su irin na mazinacin da ya taba aure; a jefe su, ko sun taba auren ko ba su taba yi ba. Wasu malamai a wannan zamanin namu cewa suke yi, lalle kisan ya tabbata ga duk wanda aka kama shi muraran cikin wannan alfasha, amma alhaki ne na alkali ya duba ya ga wane ya fi zama maslaha da tsoratarwa ga zamanin da ake ciki. Wannan shi ne raayin Sheikh Bakr bn Abdallah Abu Zaid Allah ya jikan sa. Ya za ka game dan luwadi? Allah ya haramta yada alfasha a tsakanin musulmi.
Kuma ya yi kyacin azabamai radadi a duniya da lahira ga wadanda suke son a yada labarin alfasha a tsakanin jamaar musulmi. Saboda haka, kuskure ne babba ka zargi wani da irin wannan mugun aiki ba tare da wata hujja bayyananna ba. Yana da kyau mu tuna da labarin zuwan Abdullahi bn Muti da jamaarsa wurin Muhammad bn Al-Hanafiyyah dan sayyidina Ali (RA) a lokacin da suke kai karar sarki Yazidu dan Muawiyah suna masu tuhumarsa da shan giya.. Muhammad bn Ali ya ce ma su: kun gan shi yana shan ta? Suka ce, aa. Kun gan shi yana aman ta? Suka ce, aa. Ya ce, to ta yaya kuka sani? Suka ce, mu dai mun tabbata wallahi yana shan ta. Sai ya ce ma su, Allah bai yarda da irin wannan sheda taku ba, don ya ce:
(( ﺇﻻ ﺷﻬﺪ ﻣﻦ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﻫﻢ ))
A nan zan so in kawo maganar Sayyidina Abdullahi dan Abbas (R) inda yake cewa: “Alamomin mutanen annabi Lut (AS) guda goma ne:
ﻭﺣﻞ ﺗﺼﻔﻴﻒ ﺍﻟﺸﻌﺮ ﺍﻷﺯﺭﺍﺭ ﺍﻟﺒﻨﺪﻕ ﻭﺭﻣﻲ ﻭﺍﻟﺤﺬﻑ ﺑﺎﻟﺤﻤﺎﻡ ﺑﺎﻟﺤﺼﻰ ﻭﺍﻟﻠﻌﺐ ﺍﻟﻄﻴﺎﺭﺓ ﻭﺍﻟﺼﻔﻴﺮ ﺑﺎﻷﺻﺎﺑﻊ ﻭﻓﺮﻗﻌﺔ ﺍﻷﻛﻌﺐ ﻭﺇﺳﺒﺎﻝ ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻭﺣﻞ ﺃﺯﺭ ﺍﻷﻗﺒﻴﺔ ﻭﺇﺩﻣﺎﻥ ﺷﺮﺏ ﺍﻟﺨﻤﺮ
Sannan ya ce, a cikin wannan al’umma za a samu wata dabi’a da ba a taba samu a can baya ba ita ce, mace ta kwanta da mace. Wal iyazu billah Na kawo wadannan alamomin ne domin mu yi hattara da koyi da su, ba domin mu rinka nunin duk wanda bisa ga jahilci da rashin sani yake yin wani abu a cikin su ba muna cewa shi dan luwadi ne.
Nauoin Luwadi Ya ku bayin Allah! Luwadi iri biyu ne. Mafi girman su shine wanda muka gama magana a kan sa; namiji ya kwanta da namiji domin biyan bukatarsa. Na biyu shi ne namiji ya sadu da mace ta inda wadancan kazamai suke saduwa da maza; ta wajen kazanta. Wannan shi ma babbar kabaira ne bisa ijmain duk malaman musulmi in ban da yan Shiah.
Hadisai da dama sun inganta a kan haramta shi da tabbatar da laanar Allah ga mai saduwa da matarsa da dubura. Haka kuma yin haka ya saba ma fixirar da Allah ya halicci halittunsa a kan ta:
1. Idan muka duba, Allah ya haramta saduwa da mace ta halastaccen wuri a lokacin da take haila saboda kazamta. To, ina ga wurin da shi ne matattarar kazantar kuma matabbatarta?!
2. Matarka tana da hakke a kan ka na gamsar da bukatarta da jin dadinta kamar yadda kai kake da wannan hakke a kan ta. To, ina biyan bukata ga matar da ka matse ta ta inda ba nan ne Allah ya sanya jin dadinta da bukatarta ba?!
3. Ta yaya za a ci gaba da haifuwar jamaa, duniya ta wanzu in aka dawo ana bin mata ta inda ba a shuka?!
4. Allah cikin hikimarsa ya shirya gaban mace don karbar abinda ya sharanta tayadda idan mijinta ya kusance ta sai niima ta lullube ta, gabanta ya fidda ruwa mai yauqi don sawwake abinda Allah ya hukunta. Wannan ba ga dan adam kawai ba, ga dukkan halittu. To, don mekai dan adam za ka bar inda Allah ya tsara, ka fuskanci baya; gidan kazanta da wari da nakkasa?!
Wannan nauin alfasha na biyu shi ma ba a san shi ba cikin alummar musulmi can da farko. Wani mutum ana ce da shi Abul Hubab ya tambayi Ibnu Umar (R) ya ce: ko ana iya yin TAHMIDH da Kuyangi? Sai Ibnu Umar ya ce: mene ne haka? Ya ce: saduwa da su ta dubura. Ibnu Umar (R) ya ce: Auzu billahi! Akwai musulmin da ke haka? Wannan ya nuna wata mugunyar alada ce da ta fara zo ma musulmi ta hanyar bayi yan kasashen waje masu aladun majusawa da maguzawa da aka kamo a wajajen yaki. Kuma daga sabo da wannan ne aka fara kai wa ga naui na farko.
Allah ya kare mu. Wani abin ban tsoro da takaici shi ne cewa, binciken da ake yi a duniya yana nuna ba manyan mazaje baligai kadai ke wannan danyen fasikancin ba, ba kuma su kadai ake nema da yin sa ba. A kasar Amurka cikin kowadanne yara maza dari ana samun akalla goma da aka taba yi ma su fyade ko aka nuna alama. Kasar Ingila wadda ta ce ta ji ta gani abin ba laifi ne ba, a yanzu haka ana sane da akalla yara maza kanana 60,000 wadanda dadiro da katti shi kadai ne sanaarsu. Me muke ciki a yau mu a kasarmu? Muna iya shedar tsarkin alummarmu? Babu shakka akwai alamomi da ke nuna wannan balai yana nan yana rarrafowa a cikin musulmi. Kuma bokaye da miyagun malamai na daga cikin wadanda suke taimakawa wajen yaduwar wannan alfasha a cikin alumma saboda wahayin da shaidanunsu suke yi musu. Wani dan siyasa ya tabbatar min da labarin wani malami in ji shi wanda yan siyasa suka je neman saa gurin sa, sai ya umurce su da yin alfasha da kananan yara maza guda 70. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiiun. Ya ya za mu kare yayanmu daga wannan balai?
1. Da farko dai babu abinda ya kai tarbiyya ta gari ta hanyar nuna ma yaro son Allah da bin umurninsa.
2. Akwai bukatar mu ba wa yayanmu hakkensu na kusanci da nuna kauna. Abinda malam bahaushe ya fi kowa matsala a kansa. Bahaushe bai san ya sunbaci yaronsa ba, ko ya rungume shi yana tawai, ko ya rika hannunsa yana yi masa wasa, sawaun dan karami ne yaron ko matashi. To, da yake Allah ya yi wannan dabiar a cikin zukata, yaron da duk bai sami wannan kusanci da manya a gidansu ba zaka gan shi da kishirwar kusantar manyan mutane. Abinda zai sa a cikin sauki ya fada hannun irin wadannan arnan shaidanu idan suna kusa da shi in ba a ci saa ba.
3. Mu rage gwada masu wasu nauoin zamantakewar soyayya da ke tsakaninmu da iyalanmu. Sau da yawa wannan yakan jawo yaro ya ji yana bukatar wani abu mai kama da haka in ya gane ma idonsa. Daga nan sai shaidan ya aukar da mugun abu a tsakaninsa da yan uwansa ko abokansa.
4. Da zaran yaro ya kai matsayin sanin abinda yake hatsari gare shi a sanar da shi.
- Idan yaro ya shekara biyu a fara nuna ma sa muhimmancin boye wasu sassan jikinsa.
- Idan ya yi hankali a sanar da shi cewa laifi ne jikin wani ya hadu da wani namiji ko mace domin Allah ba ya son haka sai in an aurar da mace ga namiji. Karanta kissoshin alkurani kamar kissar mutanen annabi Lut da ta annabi Yusuf (AS) na cikin abinda zai taimaka a kan wannan.
- A yi kokarin bude kofar tattaunawa da su don jin koke-kokensu da korafe- korafensu. A bari su rinka fadin abu idan ya faru gare su ba tare da an kwatse su ba domin sau da yawa za su shiga matsala su ji tsoron fada har ta aukar da su ga inda ba a so.
5. Mu sani cewa, tsarewar da muke ma dokokin Allah ta kan sa Allah ya kare mana iyalanmu. Duk mutumin da ya keta alfarmar diyan jamaa ya lalata su, ya ci amanar iyayensu tarbiyyar da zai yi kokarin yi ma yayansa da horar da su ba zata hana in Allah ya so ya dauki fansa a kansa ba, sai wani ya zo shi ma ya lalata nasa.
6. Banbanta wurin kwana a tsakaninsu da zaran sun kai shekara goma kamar yadda sunna ta karantar da mu.
7. Mu kula da duk wanda yake da hulda da gidajenmu komi kusancinsa gare mu ko ga matayenmu. Kamar yadda yake wajibi mu kula da abokanensu da suke kai da komo tare musamman wadanda suka grime su. Haka su ma malamai a makarantun yara dole ne a dauki matakan da suka kamata don hana shaidanu daga ciki yin lalata da diyan jamaa.
8. Mu kula da suturar da yaranmu suke sa wa musamman idan suna da jiki mai dan gwabi- gwabi, kada a bari suna sa tufafin da ke suranta jikinsu.
9. Mu lura da kayan wasa da na buda ido na zamani da muke kawowa a cikin gidajenmu. Akwai balaoi da yawa a cikin wasu daga cikinsu.
10. Mu yawaita adduar neman shiriya a gare su kamar yadda alkurani da sunna suka koya mana. Ina magani? Ya ku wadanda aka jarraba da wannan fitina, kuka auka cikin wannan musiba! Babu wani magani ga wannan fitina sai tuba. Tuba zuwa ga Allah da tsarkin zuciya da kyakkyawan nufin ba ku komawa. Sannan ku yawaita addua domin addua tasirinta babba ne. Babu laifi ku sa mutanen kirki wadanda ba su cin haram su yi mu ku addua.
ْﻦَﻋ ﺭﺿﻲ ﺃَﺑِﻲ ﺃُﻣَﺎﻣَﺔَ ﻋﻨﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻗَﺎﻝَ : ﺇِﻥَّ ﻓَﺘًﻰ ﺷَﺎﺑًّﺎ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓَﻘَﺎﻝَ : ﺭَﺳُﻮﻝَ ﻳَﺎ ﺍﺋْﺬَﻥْ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻟِﻲ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺍﻟْﻘَﻮْﻡُ ﻓَﺄَﻗْﺒَﻞَ ﺑِﻻﺰِّﻧَﺎ . ﻓَﺰَﺟَﺮُﻭﻩُ، ﻣَﻪْ ﻗَﻻُﻮﺍ : ﻣَﻪْ . ﻓَﻘَﺎﻝَ : «ﺍﺩْﻧُﻪْ » . ﻣِﻨْﻪُ ﻓَﺪَﻧَﺎ ﻗَﺮِﻳﺒًﺎ، ﻗَﺎﻝَ : « ﺃَﺗُﺤِﺒُّﻪُ ﻓَﺠَﻠَﺲَ . ﻟِﺄُﻣِّﻚَ »؟ ﻗَﺎﻝَ : ﻟَﺎ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻗَﺎﻝَ : ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ « ﻭَﻟَﺎ ﻓِﺪَﺍﺀَﻙَ . ﻳُﺤِﺒُّﻮﻧَﻪُ ﻗَﺎﻝَ : « ﺃَﻓَﺘُﺤِﺒُّﻪُ ﻟِﺄُﻣَّﻬَﺎﺗِﻬِﻢْ » . ﻟِﺎﺑْﻨَﺘِﻚَ »؟ ﻗَﺎﻝَ : ﻭَﺍﻟﻠَّﻪِ ﻟَﺎ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﻳَﺎ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻓِﺪَﺍﺀَﻙَ . ﻗَﺎﻝَ : ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ « ﻭَﻟَﺎ ﻟِﺒَﻨَﺎﺗِﻬِﻢْ » . ﻳُﺤِﺒُّﻮﻧَﻪُ ﻗَﺎﻝَ : « ﺃَﻓَﺘُﺤِﺒُّﻪُ ﻟِﺄُﺧْﺘِﻚَ »؟ ﻗَﺎﻝَ : ﻭَﺍﻟﻠَّﻪِ ﻟَﺎ ﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻗَﺎﻝَ : ﻭَﻟَﺎ ﻓِﺪَﺍﺀَﻙَ . « ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﻳُﺤِﺒُّﻮﻧَﻪُ ﻟِﺄَﺧَﻮَﺍﺗِﻬِﻢْ» . ﻗَﺎﻝَ : « ﺃَﻓَﺘُﺤِﺒُّﻪُ ﻟِﻌَﻤَّﺘِﻚَ »؟ ﻗَﺎﻝَ : ﻟَﺎ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻗَﺎﻝَ : ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ « ﻭَﻟَﺎ ﻓِﺪَﺍﺀَﻙَ . ﻟِﻌَﻤَّﺎﺗِﻬِﻢْ » . ﻳُﺤِﺒُّﻮﻧَﻪُ « ﺃَﻓَﺘُﺤِﺒُّﻪُ ﻟِﺨَﻻَﺘِﻚَ ﻗَﺎﻝَ : »؟ ﻗَﺎﻝَ : ﻭَﺍﻟﻠَّﻪِ ﻟَﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻗَﺎﻝَ : « ﻭَﻟَﺎ ﻓِﺪَﺍﺀَﻙَ . ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﻳُﺤِﺒُّﻮﻧَﻪُ ﻗَﺎﻝَ : ﻓَﻮَﺿَﻊَ ﻟِﺨَﻻَﺎﺗِﻬِﻢْ » . ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻳَﺪَﻩُ « ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﻗَﺎﻝَ : ﺍﻏْﻔِﺮْ ﻭَﻃَﻬِّﺮْ ﺫَﻧْﺒَﻪُ، ﻭَﺣَﺼِّﻦْ ﻗَﻠْﺒَﻪُ، ﺑَﻌْﺪُ ﻓَﻠَﻢْ ﻓَﺮْﺟَﻪُ » . ﺫَﻟِﻚَ ﻳَﻜُﻦْ ﺍﻟْﻔَﺘَﻰ ﺷَﻲْﺀٍ ﻳَﻠْﺘَﻔِﺖُ ﺇِﻟَﻰ .
A nan (S) sai ya sa hikima da kwarewa wajen cire ma sa son barnar da nuna ma sa muninta. Sannan kuma sai ya hada ma sa da addu’a.
2. Ka nisanci duk abubuwan da ke kai ka ga wannan fitina. Wasu finafinai, wasu shaidanai, miyagun abokan hulda wasu wuraren shakatawar da ke jan ra’ayinka ga wannan aiki dss.. Da duk wani dalilin da ke jan ka zuwa ga wannan ma’asi ka kulla gaba da shi saboda ka shirya da Allah.\
3. A kullum idan shaidan ya so ya ja ka zuwa wannan kazanta yi sauri ka tuna ma rayuwarka irin lafiya da mutuncin da Allah ya ba ka. Za ka so ka wa Allah tukuici da bata su ta wannan hanya? Ya zaka yi idan Allah ya jarabce ka a dalilin wannan ma’asi da wani irin mugun ciwo daga cikin ciwarwatan da muka fada?!
4. Ka tuna Allah a lokacin da shedan yake kyarkyarar ka. Kwatanta kanka ka shiga da abokin bala’inka kun kulle kofa kuma har wani ya hau wani kun fara wannan kazanta. Kwatsam ashe kaddara ta sa kofa ta bude. Sai ga wani mutum mai girman daraja a idonka wanda kake jin nauyinsa, kamar ace surukinka ko malaminka ko maigidanka. Kai, ko ma yaron gidanka. Ya kake jin zuciyarka zata kasance? To, don me zaka mai da Allah kasa da matsayin duk wadanda kake jin kunya? Daga karshe, ya ku bayin Allah! Mu sani – kamar yadda Ibnul Qayyim ya fada: Hakurin barin sabo ya fi sauki a kan hakurin abin da sabo ke jawowa. Shi dai sabo ala tilas ne:
Ya jawo maka ukuba.
Ko ya hana maka wani jin dadi da ya fi wanda ka samu wurin sabon.
Ko ya bata ma ka lokaci mai daraja da kake bukata.
Ko ya zubar ma ka da mutuncin da ya fi kima gare ka a kan wannan sabon.
. Ko ya lashe wasu kudin da za a yi maka hisabi a kan su. Da sadaka ka yi da su ko kyauta, kai ko faduwa suka yi ya fi maka sauki.
Ko ya kawar ma ka da wata ni’ima wacce Allah zai ba ka, ba don ka yi sabon ba.
Ko ya buda ma wani makiyinka kofar samun sa’a a kan ka.
Ko ya mantar da kai wani abu mai amfani da ya kamata ace yana cikin tunaninka.
10. Ko ya janyo maka wani bakin jini da bacin suna a tsakanin bayin Allah. Ya Allah ka yi manakariya da mu da iyalanmu daga sharrin kan mu da sharrin shaidan, ka gyara zukatanmu da dabi’ummu, ka sawwake yin tuba ga masu sabo daga cikinmu, ka saukar da rahamarka a gare mu da aminci a cikin wannan kasa tamu da sauran kasashen musulmi.
Comments
Post a Comment