GIRMAN KAI KASHI NA TAKWAS 8

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 4:

Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?

Ci gaba...

4- Mulki ko Sarauta

Mulki ko sarauta kan sanya mutum yin girman kai da wulaqanta mutane da mayar da mutane bayinsa kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya ba mu labarin Fir'auna, wanda giyar mulki ta dauke shi ya zama mai girman kai da dagawa da mayar da mutane bayinsa; ya kashe wanda ya kashe ya raya wanda ya raya, ta kai shi har sai da ya yi da’awar allantaka, kamar yadda Allah (swt) ya ce:

"Fir’auna ya yi shela a cikin mutanensa ya ce: Ya ku mutane na, shin ba ni ne nake da mulkin Misra kuma wadannan qoramun su ke gudana ta qarqashi na ba? Shin ba kwa gani ne? Shin baku ganin ni ne fiyayye ba wannan wulaqantaccen da ko kusa ba ya iya bayayyana magana ba?" - (Suratu Zukhruf, aya ta 50 -51).

Wannan ayar tana nuna yadda Fir'auna ya yi girman kai da alfahari da wulaqanta Annabi Musa (as), saboda mulkin Misra da yake hannunsa, har ma yana goranta ma sa daurewar harshe.

Irin wannan shi ne halin da yawa daga cikin ma su mulki, su na ganin cewa mulkinsu ko sarautarsu ta ba su damar cin zarafin na qasa da su da wulaqanta su da goranta mu su cewa su ba komai bane.

A wata ayar kuma, Allah (swt) ya ce: “Haqiqa Fir’auna ya yi dagawa a ban qasa, ya mayar da mutanen qasar bangare –bangare, yana qasqantar da wani sashe a cikin su, yana yanka ‘ya‘yansu maza, yana barin yayansu mata a raye. Haqiqa shi ya kasance daga cikin ma su barna a ban qasa." - (Suratul Qasas, aya ta 4).

Wannan ayar da wadda ta gabata sun nuna dagawar Firauna, da yadda giyar mulki ta dauke shi ya rarraba al'umma bangare bangare don ya sami damar mallakarsu da wulaqanta su da yin yadda ya ga dama da su, kamar yadda wasu masu mulki su ke yi a yanzu.

Haka Allah ( ya faxa a wata ayar ya ce: “Fir’auna ya yi girman kai, shi da rundunarsa a ban qasa, ba tare da haqqi ba. Kuma sun yi zaton cewa haqiqa su, ba za su komo zuwa gare mu ba." - (Suratul Qasas aya ta 39).

Irin wannan girman kai, wanda mulki ke haifarwa, har ila yau, ya kan sanya mutum ya qaryata annabawan Allah da yin jayayya da su, da yin da’awar abin da mutum bashi da shi, kamar yadda Allah (swt) ya ba mu labarin Annabi Ibrahim (as) da wani mai mulki a zamaninsa.

Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Shin ba ka ga wanda ya yi jayayya da Annabi Ibrahim (as) dangane da Ubangijisa, Don Allah ya bashi mulki? Ya yin da Annabi Ibrahim (as) ya ce: Ubangijina shi ne wanda yake rayawa kuma yake kashewa, sai ya ce: ni ma ina rayawa, kuma ina kashewa. Sai Annabi Ibrahim (as) ya ce: haqiqa Allah (swt) yana fito da rana daga gabas, kai kuma ka fito da ita daga yamma. Sai aka kunyatar da wanda ya kafirta. Kuma Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai.” - (Suratul Bakara, aya ta 258)

Kamar haka ne a yanzu giyar mulki take daukar wadansu shugabanni, su ke ta zubar da jini a duniya da mayar da mutane bayi, ba tare da wani haqqi ba, illa dai kawai girman kai da nuna isa da qasaita. Allah ya shirye mu baki daya.

°

°

Sai mun hadu a fitowa ta 8 da yaddar ALLAH

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA