WAYE A DUNIYA KAFIN ALLAH
WAYE A DUNIYA KAFIN ALLAH? .
Wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani jarumi kuma kafirin mutum, ga tsananin karfi ga zalunci da mugunta.
.
Wata rana wannan kafiri ya fito yana yawo a cikin gari, sai yaji wani Malamin Musulmi yana wa'azi, saboda dadin wannan wa'azi na Malamin yasa mutane suka taru sosai don saurarensa. .
Ko da wannan kafiri ya iso wurin, sai yayi ihu mai razanarwa, har sai da kowa da yake a wurin ya tsorata, sannan yace; Na zo maku da wata tambaya daya da nake so ku amsa mani, duk wanda ya amsa ta daidai daga cikin ku zan bashi dukiya ta tare da zama bawansa, kuma zan kasance acikin addininku, Mai gasgata shi.
Tambayar ita ce; WAYE A DUNIYA KAFIN ALLAH? Tare da hujja mai karfi. ..
Duk mutanen dake a wurin suka kasa bashi amsar wannan tambaya.
.
Sai wani yaro karami ya fito yace: zan amsa maka tambayar ka amma nima sai ka fara amsa tambayar da zanyi maka yanzu, idan har ka amsa daidai to nima zan baka amsar tambayar ka. .
Mamaki ya cika wannan kafiri ganin cewa karamin yaro ya fito zai ja dashi, sai ya Amsa ma wannan yaro da cewa ina jinka. .
Yaro ya fara kirga kamar haka: 1,2,3,4,5,6,7,8 ,9,10..... Sannan ya tambayi wannan kafiri menene gaba? Sai ya amsa masa: 11,12,13,14,15.
Sai yaro ya dakatar dashi yace; To yanzu so nake ka dawo baya daga 10 zuwa 1.
. Wannan kafiri yayi kamar yadda wannan yaro ya umarce shi; 10,9,8,7,6,5,4, 3,2,1,0.
. Sai yayi shiru. Yaron yace cigaba mana. Kafiri ya amsa da cewa ai duk wanda yasan kidaya yasan cewa lamba 1 itace farko babu wata kafin ita, kuma ba'a taba yi ba.
.
Sai yaro yace, ya akayi ka yarda cewa 1 ce farkon lamba amma baka yardar cewa Allah shi kadai ne ba'ayi wani ba kafin shi? Sai wannan kafiri yayi shiru ya rasa abin cewa, tun daga ranar ya musulunta ya kuma zama dalibi a wurin wannan yaro.
WANNAN YARO BA KOWA BANE ILLA "IMAM ABU HANIFA"(Rahimah ullah) Allah Ya Kara Daukaka Addinin Musulunci Ameen.
. zaka iya biyomu ta wannan shashi domin Samsun labarai bandariya. rabswudil.mywapblog.com/
Comments
Post a Comment