GIRMAN KAI KASHI NA SHIDA
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?
Ci gaba...
3- Ilimi:
Ilimi yakan sanya mutum girman kai da alfahari da jiji da kai da wulaqanta wadansu. Yin haka kuwa asara ne da tabewa, kamar yadda magabata na qwarai su ka yi nuni a cikin maganganunsu:
Imam Ibn Abdus (sunansa: Al Imam al Hujja, Abu Ahmad Muhammad bn Abdus bn Kamil Assiraj Assulami Albagdadi, ya yi ruwaya daga Aliyu bn al-Ja'ad da Imam Ahmad da Abubakar bn Abi Shaiba da sauransu. Daga cikin dalibansa kuma akwai imam Addabarani da wasunsa, ya rasu a shekara ta 293 bayan Hijira) ya ce: "A duk sanda mai ilimi ya sami girma da daukaka, to, jiji da kai ya fi saurin zuwa gare shi, sai dai wanda Allah ya kare shi da datarwarSa, kuma ya cire son shugabanci daga ransa." - (Ibnu Abdil Barri ya rawaito shi, Jamiu Bayanil Ilmi wa Fadhlihi, lamba ta 962 juzii na 1 shafi na 569, bugun Daru Ibnil Jauziy, Tahakikin Abdul Asbal Azzuhairiy).
Kuma yin girman kai da ji-ji-da-kai da taqama don mutum yana jin cewa yana da ilimi, malamai sun ce jahilci ne, kamar yadda babban malamin nan Masruq ya ce: “Ya ishi mutum ilimi ya kasance yana tsoron Allah. Kuma ya ishi mutum jahilci ya kasance yana jiji da kai da iliminsa." - (Ibnu Abdil Barri ya rawaito shi, Jamiu Bayanil Ilmi wa Fadhlihi, lamba ta 962 juzii na 1 shafi na 569, bugun Daru Ibnil Jauziy, Tahakikin Abdul Asbal Azzuhairiy).
Wadannan munanan dabi’u annoba ne ga mai ilimi kamar yadda malamin nan Aliyu bin Sabit Allah ya yi masa rahama yace: “Dukiya, annobarta ita ce almubazzaranci da yi wa mai ita kwace. Shi kuwa ilimi annobarsa ita ce: jiji da kai da rashin haquri." - (Ibnu Abdil Barri ya rawaito shi, Jamiu Bayanil Ilmi wa Fadhlihi, lamba ta 567 juzii na 1 shafi na 959, bugun Daru Ibnil Jauziy, Tahakikin Abdul Asbal Azzuhairiy).
Haka kuma jiji da kai abu ne dake janyowa mai ilimi qasqanci da wulaqanci kamar yadda aka rawaito daga Ka’ab (ra) ya ce: "Haqiqa idan da iliminka ya cika tsakanin sama da qasa, kuma kana da jiji da kai, Allah ba zai qara ma ka komai ba sai qasqanci da tawaya." - (Duba littafin da aka ambata a sama, lamba ta 567, shafi na 959).
Abin mamaki, za ka ga wadansu Allah ya ba su ilimin addini ko na boko ko ilimin sana'a, su na yin girman kai da ji-ji-da-kai da wulaqanta mutane da raina su, musamman ma wadansu tsangayu na jami'oi su na raina wasu tsangayoyin da ba su ba, ballanatana ma wadanda ba su yi ilimin bokon ba.
Da yawansu kuma su na samun zuga ne daga wadansu malamansu cewa tsangayar da kuke ta fi kowacce tsangaya, ku ne ma su daukaka, ku ne fiyaiyun mutane. Da wannan zugar sai ta sa su girman kai da ji-ji-da-kai da wulaqanta mutane ba tare da wani dalili ba.
Babu shakka, wannan jahilci ne, domin duk mutumin da yake da ilimi da kuma hankali, ba zai wulaqanta mutane ba, domin zai yi amfani da iliminsa ne, ya ilimantar da alummarsa, ya fitar da su daga qangin jahilici, da na bauta. Kuma ya tsaya yaga alummarsa sun ci gaba. Kuma ba zai hana kansa neman ilimi da ba na tsangayarsa ba, musamman ilimin addini wanda zai gyara ma sa rayuwarsa duniya da lahira. Amma wadansu mutane sun tabe, sun yi asara, sun dauki kansu cewa sun fi qarfin su nemi ilimin addini, su na ganin cewa ci-baya ne, gidadanci ne, su su ke da ilimin zamani. Daga qarshe za su cuci kansu, su cuci zuriyarsu, su cuci alummar su, sai mutum ya wayi gari da baqin ciki, da asarar rayuwa da tashin hankali saboda rashin ilimin addini har ya hadu da Ubangijinsa. Mu na neman tsarin Allah.
° ° °
°
Sai mun hadu a fito ta 07 da yardar Allah
Comments
Post a Comment