GIRMAN KAI KASHI NA TARA
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?
Ci gaba...
6- Yawa:
Yawan mabiya, ko na dangi ko na ‘ya‘ya sukan sanya wadansu mutane girman kai da dagawa. Dalili kuwa shi ne; Allah madaukakin Sarki ya ce:
“Bamu aika wani mai gargadi a cikin wata alqarya ba, face ma su dukiya da shugabannin garin sun ce; lallai mu ma su kafurcewa ne ga abin da aka aiko ku da shi. Kuma su ka ce: mu ne mafi yawan dukiya da ‘ya‘ya kuma mu ba za a azabtar da mu ba.” - (Suratu Sabai aya ta 34 35).
A wata ayar kuma Allah madaukakin Sarki ya bamu labarin mutumin da ya mallaki gonaki biyu, kuma kowacce ya sami amfanin gona mai yawa, amma maimakon ya gode wa Allah sai ya yi dagawa da girman kai, da jin isa, da gorantawa abokinsa, inda ya ce masa:
Ni ne na fi ka yawan dukiya da xinbin jama’a (magoya baya).” - (Suratul Kahafi aya ta 34).
Wadannan ayoyi na nuni akan yadda wasu su ke alfahari da yawan 'ya ‘ya da dinbin jama’a magoya baya, kamar yadda su ke alfahari da dukiya.
Wannan ta sanya babban malamin nan Imam Qatada (Qatada bn Da'ama as-Sadusi al-Basari, babban tabi'I masasanin tafsiri da hadisi da lugga da tarihin larabawa, ya yi ruwaya daga ibn sarjis da anas bn malik da Abiddufail d hasanul basari da sauransu. Ya rasu a shekara ta 118 bayan hijira) ya ce:
“Wallahi wadannan su ne burin kowane fajiri; yawan dukiya da tara dinbin mabiya.” - (Tafsiru Ibni Kasir, karkashin ayar da ta gabata, mujalladi na 3, shafi na 93, bugun maktabatu Daru Salam).
Idan an lura da wadannan ayoyi da kuma maganar wannan babban malami wato Imam Qatada, za a qara tabbatar da cewa tara dukiya da dinbin mabiya su ne suke sanya wadansu mutane, musamman wasu daga ‘yan siyasa da ma su mulki da malamai a yanzu su ke girman kai da jin isa da cika baki da alfahari da kuma fasadi a ban qasa da qin karbar gaskiya. Da zuga mabiya su zubar da jinin bayin Allah wadanda basu jib a basu gani ba. Shin basu san Allah zai iya juyar da wadannan mabiyan su zama maqiyansu tun daga nan duniya ba? Ko ko sun manta cewa Allah zai kama su a ranar Alqiyama ne? Lallai ne su gaggauta tuba da komawa ga Allah Subhanahu wa Taala. Allah ya shirye mu da su baki daya.
Sai mun hadu a fitowa ta 10 da yardar Allah
Comments
Post a Comment