FINA FINAN BATSA [BLUE FILMS]
FINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS)
Blue Films fina finai ne da wasu tsageru daga cikin Yahudawa suke shiryawa wanda yana da illa sosai.
Domin yanzu anyi ittifakin cewa ba abinda yake saurin rufta mutum zuwa zinace-zinace kamar shi kallon Blue Film din wanda zamani yazo dashi baga namiji ba ba kuma ga mace ba.
Babban abin takaici yanzu yan mata sunfi kowa kwarewa wajen iya kallon wannan lalaci na Blue Film.
HUKUNCIN SA:
Kallon tsaraici haramun ne a shari'ar musulunci in banda na matarka ko na mijinki ballantana kuma kallon saduwa tsakanin Mazinata wannan abune mai matukar muni sosai.
Allah yana cewa:
"Ka gayawa muminai maza su rintse idanuwansu daga kallon haram kuma su kiyaye farjinsu daga yin zina.
Yan uwa mu kiyaye, duk wanda yake kallon irin wandannan abubuwa to lalle yayiwa Allah tawaye.
A wani gurin Allah yana cewa:-
Kada ku kusanci zina hakika ita zina Alfasha ne kuma mummunan hanyace.
Kunga saboda halakar da take cikin zina sai Allah yace kada mu kusan ceta, shi kuwa irin wannan kallon yakan sanya masu yinsa su afka cikin zina kai tsaye.
Manzon Allah (S. A. W) yana cewa:
"Allah ya tsinewa mai kallon tsaraici da kuma wanda ake kallon tsaraicin nasa.
Daga karshe ina kara jawo hankalin masu yi su tuba su daina.......!!! Dan Allah Daure ka Rubuta Amin bamusan tawa za'a kar6a ba.
YA ALLAH KA TSARKAKE MANA ZUKATANMU, KA KARE ZURI'AR MU DAGA AFKAWA CIKIN MUMMUNAR BALA'IN DAKE TATTARE DA KALLON BLUE FILMS.
NAGODE
ReplyDelete