GIRMAN KAI
GIRMAN KAI
SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
GODIYA
Dukkan godiya da yabo da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah wanda ya siffantu da girma da qasaita. Ina gode ma sa godiya mara adadi, domin shi ne ya can-can-ci yabo a farko da qarshe. Ina qara godiya ga re shi (swt) wanda bisa rahamarSa ne ya bani ikon rubuta wannan littafi mai suna: GIRMAN KAI, SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Ina salati da sallama ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (saw) jagoran ma su qanqan da kai. Tsira da amincin Allah su tabbata a gareShi da AlayanSa da sahabbanSa da wadanda su ka biyo su da kyautatawa.
Bayan haka, wannan littafi ne da ya qunshi bayani game da girman kai da abubuwan da su ke jawo shi da bayanin hadarinsa da kuma hanyoyin da za a magance shi.
Wanda Malaminmu Shaikh abdulwahhab Abdallah bn Muhammad ya wallafa game da wannan babbar cuta kuma Mallam ya yi bayani mai gamsarwa bisa dogaro da ayoyin Alqur'qni da ingantattun hadisai wajen bayyana hadarin wannan cuta da maganinta. Wadda da yawa daga cikin al'ummar musulmi a kowane mataki na rayuwa su ka jarrabu da ita, babu malami babu mai neman sani, babu mai mulki ko attajiri babu talaka. Kuma da yawansu suna dauka hakan shi ne daidai.
A bangare guda kuma mallam ya yi bayanin wasu halaye da mutane kan dauka girman kai ne alhali kuwa ba sa cikin girman kai.
Daga qarshe muna roqon Allah ya sanya albarka a wannan littafi, ya sanya shi kuma ya zama mai amfani ga al'ummar annabi (saw). Shi kuma Malamimmu Shaikh Abdulwahab bn Abdallah bn Muhammad, Allah Ya saka ma sa da alkhairi game da irin wadannan aiyuka da ya keyi na taimakon addini da kuma kare martabar manzon Allah (saw) da sahabbanSa da yada sunnarSa babu dare babu rana. Kamar yadda muke roqon Allah Ya albarkaci zuriyarsa da mu almajiransa da dukkanin wanda ya taimaka wajen wannan aiki, amin.
°
° ° °
Sai mun hadu a fito ta 02 da yardar Allah
Comments
Post a Comment