CUTAR BASIR
Babu abu mai ban tausayi ko kuma damuwa kaji Mace tace wai ashe haka BASIR yake lalata Maza ya maida su kamar mu.
Ko mai tsananin Soyayya tsakanin Mace da Namiji, shine dai ayi Aure a Karshe, san nan a zauna matsayin Mata da Mijinta.
A cikin Hakkokin da aka dorawa Miji wanda babu makawa sai ya sauke shine Kwanciyar Aure a tsakaninsu, kada kuma ya gaza sau 1 a cikin Kwana 4.
Amma Mace tayi Aure, ta baro Gidajen Iyayenta, ana yi mata Murna, ana Allah ya kawo Katsantar Daki,bkuma tazo ta sami Ango bashi da Banbanci da ita kanta, to babbar matsala ta faru.
Saboda haka in har Mace ta kai Karar Mijinta cewa ashe 'Yar Uwarta aka Aura mata, to Tsofaffi sun gano abinda take nufi, sai a fara nema masa magani kuma cikin gaggawa don kada murnar Amarya ta koma ciki.
Yanzu labari ya bazu cewa mafi yawan Mata da zarar an sa musu ranar Biki, sun fara nema da kuma shan Maganin Mata, wato maganin basu Kuzarin Shimfida, da wanda zai kara musu Ni'ima da Annashuwa, da kuma wanda zai basu damar juriya da dadewa suna yin Ayyuka.
Haka suma Maza da zarar ance ga Watan bikinsu yazo, sai kaji ana cewa a hada masa Maganin Daci da Basir da kuma Zagi, kaga yana ta shan dauri domin biyan bukatar Amaryarsa.
Idan akaci sa'a ya zarce a haka, to wannan bangaren shi ya tsere sa'a, amma in aka sami komawa baya sai muce Allah ya sawwaka. Wasu sunce abinda yake kawowa Maza raunin da suke fama dashi a yau sune:
1=Ayyuka masu wahala saboda neman Dari da Kobo, sai Namiji ya dawo a gajiye, ya kasa tabuka komai, yana kallon Uwargida amma haka zai bacci.
2=Aikin Office wanda yake daukar tsawon lokaci Namiji yana zaune a kan Kujera, shima duk bayansa da Kugunsa ya gaji, sai yazo ya dami Uwargida ko Amarya da Minshari.
3=Yawan cin kayayyaki sarrafaffu na gwangwani dana Kwalaye, wanda an sanya musu sinadarori kala-kala, sai shima ya raunata jijiyoyin Namiji.
4=Rashin Wasanni na dogon lokaci, sai kawai Namiji ya biya Bukatarsa lokacin da Mace ta fara shaukinsa, a sannan shi kuma ya koma kamar wani Toron Agwagwa ba sauran Karfi.
5=Rashin yin Atisaye ko motsa Jiki a wajen Mai gida, da kuma yawan cin Naman Shanu ko na Tumaki da Awake (Red Meat), maimakon yawan cin Naman Tsuntsaye kamar Kaji, Dan Shila, Zabbi da sauransu
6=Rashin yan Addu'oi da Zikirorin Safiya da Maraice, wa'yanda Sunnar Manzon Allah (saw) ta koyar, sai ka sami Shaidan ya sanyawa Mutum Kasala ta Jiki da sauran gabobi.
Shine yasa Manzon Allah (saw) ya zama yana yin Addu'ar wanzuwa da rayuwa tare da karfinsa. "WA QUWWATUNA ABADAN MA AHYAYTANA". Wa'yan nan da wasu dalilai yasa dole ne Maza suci gaba da rashin biyawa Matansu bukatu, matukar basu gyara ko canja rayuwarsu ta yau da kullum da kuma tsarin cin Abinci ba, to Namiji zai zama kullum cikin bawa Amarya ko Uwargida hakuri.
Ko kuwa yaya ku gani 'Yan uwa???
gud :oops:
ReplyDelete