FANKE

abin bukata

filawa kofi 2

kofi 1 1/2 na ruwan dumi

ckb 1 na yis

1/2 na sikari

kc 1 na gishiri

vanilla don dandano

albasa kankararriya

yadda za ayi

a zuba yis cikin ruwan dumi don ya narke sai a zuba akan filawa tare da sikari,gishiri da vanilla

a kwaba su baki daya yayi dan tauri a sami wuri me dumi a ajiye don ya tashi a sami kamar aa daya.

a dora mai a wuta idan yayi zafi sai kisa hannunki ki dinga yankowa kina sawa a cikin man.

idan ya soyu zaki ga ya zama ruwan kasa.za a iya ci da shayi ko kunu ko lemo.

kada amanta kwabin kada ya zama ruwa-ruwa ko tauri.

Comments

Popular posts from this blog

FARILLAN SALLAH

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH