SHINKAFA DAFADIKA MAI KWAI
Abin bukata
ruwan kwakwa kofi 5
shinkafa gwangwani 3
timatir manya 5
timatirin gwangwani 1
mai madaidaici
kanunfari kc1
gishiri don dandano
ganye bay kadan
albasa
attaruhu kadan
tafarnuwa
yadda za ayi
A dafa ruwan dumi a zubawa shinkafa kafin a dafa ta.
A jajjaga attaruhu tare da tafarnuwa. asa mai a wuta idan ya soyu sai a zuba jajjagaggun kayan miya a kawo timatirin gwangwanin nan a zuba akai su soyu gaba daya idan sun soyu sai a zuba ruwan kwakwan nan akai tare da ganyen bay.
Daya tafaso sai a wanke shinkafa a zuba a rufe ta idan ana so a hada ta dankalin turawa a zuba mata gishiri daidai gwargwadon bukata.
Idan ta dahu za a iya cin ta da naman kaza soyayyaye ko kifi. wannan dafadukar wata nauin dafaduka ce da babbain ta da wanda aka sani shine ruwan kwakwa da aka sa. a wasu kashen afrikan ake yinta kamar cameroun kuma ana girka ta da nama amma wannan na bada zabi za a iya anfani da abin da ake bukata.kamar wanda basa cin nama
zasu iya anfani da wannan hadin.
Comments
Post a Comment