GIRMAN KAI KASHI NA GOMA.
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?
Ci gaba...
7- Fasahar harshe da iya bayani:
Fasahar harshe da iya bayani yana sanya wadansu mutane girman kai da ji-ji-da-kai da wulaqanta mutane, kamar yadda hadisi ya tabbata daga Jabir bn Abdullah (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa yana cikin wadanda su ka fi soyuwa a gare ni kuma mafi kusanci da ni a ranar alqiyama wadanda su ka fi kyakkyawar dabia. Kuma ya na daga cikin wadanda na fi qi, wadanda za su nesanta da ni a ranar alqiyama, su ne ma su yawan surutu (Al-Imamun Nawawiy ya fassara kalmar sarsaruna a harshen larabci da cewa: Sarsar, shi ne mai yawan kallafawa kansa gwanintar zance. Wadannan mutane su ne Ash-Sheikh Al-Usaimin ya siffanta su da cewa idan su na waje wani bai isa ya yi magana ba. Idan wani zai yi magana sai sun nemi su danne shi da surutu) da ma su nuna burga a cikin maganarsu (Kalmar (Mutashaddiqun), Imamun Nawawiy ya fassara ta da cewa: Mutashaddik: shi ne mai girman kai ga mutane idan yana magana, yana cika baki don jin cewa shi mai fasaha ne, yana jin cewa maganar shi tana da girma da muhimmanci. Wadannan mutane, As-Shaikh Usaimin ya siffanta su da cewa: su ne ma su riyawa cewa sun fi kowa fasahar harshe. Har gama garin mutane ba sa fahimtar abinda su ke fada) da kuma ma su yalwata magana don nuna gwaninta. (Al-Imam Anawawi ya fassara (Mutafaihiqun) da cewa: Mai cika bakinsa da surutu, yana buda magana, yana amfani da baqin kalmomi don nunawa mutane girman kai da jin daukaka da fifita kansa akan wasu)” Sai sahabbai su ka ce: “Ya Manzon Allah mun san ma su yawan surutu da ma su nuna burga a cikin maganar su, amma ba mu san kalmar (mutafaihiqun) ma su yalwata magana don nuna goninta ba.” Sai ya ce: “su ne ma su girman kai.” - (Hadisi ne Hassan, Tirmiziy ne ya rawaito shi, hadisi na 2018, bugun Baitul Afkar Ad-Dauliyyah).
°
Sai mun hadu a fitowa ta 11 da yardar Allah
Comments
Post a Comment