RAYUWAR JAMI'A

Rayuwa tana cike da rudani da abubuwa masu ban al'ajabi, mamaki, haushi, ban dariya da kuma ban takaici ammafa ni tunda nake ban taba ganin ko jin abinda nagani kuma naji a jami'aba. Idan akacemin lalacewar jami'a yakai makura ada za'a iya kwana ana musu dani, amma ayanzu nasan cewa sai dai atakaita.

Bana mantawa wata rana muna zaune da wata kawata sai wata kanwarta ta kirata tace tanason ganinta, ta gaya mata inda muke tazo ta samemu, tana zuwa tasa mata kuka "wai yan' dakin sune idan ta kwanta suke shashshafata, takai kararsu amma sunce ba zasu daina ba sai dai tabar dakin" karshen abin kuma dole dai tabar dakin.

Wai ace 'ya'yan hausawa musulmi ne suke kungiyoyi na madigo a jami'oinmu tun suna boyewa wai har sun daina, kiri kiri yarinya zata nunama ita' yar Lesbian ce. waiyazubillah.

Sunmata cewa babu tantirai sai wada suke aikata mumunan aiki kuma Duke bayyanwa SUNY.

Yanzu ace a jami'oinmu in yarinya tashiga kafin namiji daya yayi kokarin lalatama 'ya mata biyar sunyi wannan kokarin, Da wata makaranta ta kafa hukuma tayi mata bincike akan masu har kar Lesbian karshe dai sai hakura sukai dan kusan a 'yan mata hudu zaka samu daya tana wannan harkar ko fiye da haka sai sukaga in sukace za suyi kora to basu gyara ba kenan dole sai wa'azuzzuka aka rika shirya musu domin fadakarwa.

Ni abinda yake cimin tuwo a kwarya shin a halin da jami'a take ciki bama kamar ta kwana inda zakaga 'yar shekarar farko da' 'yar shekarar karshe a daki daya ta saka hotonta a screen saver dinta tazama baby dinta kai wasuma sun koma kwanciya gado daya, yayin da wasu dakunanma ware kansu suke inkuma an kawoki dakin to zasu nemeki inkinki sai dai kibar dakin wanda ba kowacce yarinyace take shaba, domin yadda suke da wayo da kuma gogewa sai dai Allah ya kwaceki.

Shin bawani mataki da hukumomin jami'oi zasu dauka domin rage ko kawo karshen wannan mummunar dabi'a a cikin al'ummarmu???

ALLAH kashiyar da bayinka.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA