Sanatocin PDP sunyi Bore akan Amincewa da Amaechi da majalisa tayi a yau.

Sanatocin PDP sunyi Bore akan Amincewa da Amaechi da majalisa tayi a yau.

Sanatocin sun fice daga majalisan a daidai lokacin da za'a amince da sunan Amaechi da nufin basu yarda da zabin nasa ba.

Dukda haka shugaban Majalisan Dattawan Bukola Saraki yayi burus da kokarin hana hakan inda ya amince da Zabin Amaechi din tsakaninshi da 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC.

Majalisar Dattawa ta amince da zabin ministoci 17 bakwai data tantance a majalisan wadanda suka hada da Adebayo Shittu, Kadjiat Abba Ibrahim, Heineken Lokpobiri, Claidius Omoyele Daramola, Baba Shehuri Mustapha, James Ocholi, Isaac Folorunsho Adewole, Bawa Bwari, Geoffrey Onyeama, Zainab Ahmed, Masur Mohammed Danladi, Usani Uguru, Okechukwu Elemanah, Anthony Anwuka, Mohammed Musa Bello, Adamu Adamu da Aisha Abubakar.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA