Rashin Nasara A Kan Boko Haram Ba Zai Sa Ni Yin Murabus Ba Daga Mulki, Inji Buhari

Rashin Nasara A Kan Boko Haram Ba Zai Sa Ni Yin Murabus Ba Daga Mulki, Inji Buhari . . A wata tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da kafar yada labarai ta Al Jazeera, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta kawar da 'yan kungiyar Boko Haram nan da karshen wannan shekara, amma kuma ya kara da cewa za su iya yin zaman sulhu da 'yan kungiyar domin sako 'yan matan Chibok. . "Muna bukatar su tabbatar mana da cewa suna nan a raye, kuma cikin koshin lafiya, to za mu iya tattaunawa da su. A shirye muke da yin zaman sulhun idan har mun tabbatar 'yan matan Chibok din suna nan a raye". . Shugaban kasan ya bayyana cewa za su yi nasara a kan Boko Haram nan da karshen wannan shekara, inda ya fadawa kafar yada labaran ta Al Jazeera cewa "kafin nan da karshen wannan shekara za mu kawar da Boko Haram, wanda kuma hakan zai zama karshensu. Harin da suke kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ya kusa kawowa karshe". Idan ba mu yi nasara a kan Boko Haram ba nan da watan Disamba, ba zan yi murabus daga mulki ba". . “Maimakon haka zan ci gaba da tafiyar da gwamnati har sai na ga bayan Boko Haram.”

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA