GIRMAN KAI KASHI NA SHA DAYA.
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?
Ci gaba...
8- Yawan Ibada:
Yawan Ibada ya kan sanya wadansu mutane girman kai da wulaqanta mutane. Ma su irin wannan dabi’ar su na ganin cewa su su ne na Allah, su ne masu matsayi a gurin Allah, su ne 'yan gwagwarmaya da jihadi, su na ganin ragowar mutane kamar halakakku ne. Dalili kuwa shi ne, hadisi ya tabbata daga manzon Allah (saw) ya ce:
“Idan kun ji mutum yana cewa mutane sun halaka to shi ne mafi halakar cikin su.” - (Muslim: 2823).
Al-Imam an-Nawawiy ya ce:
“Wannan hanin, an yi shi ne ga wanda ya fadi haka don jiji da kansa da qasqantar da mutane da daukaka kansa a kansu. Wannan shi ne haramun.” - (Riyadus Salihin, karkashin hadisi na 1598).
Kuma wani hadisin ya inganta daga Abu Hurairah (ra), daga Manzon Allah (saw) ya ce: “Wadansu ‘yan uwa guda biyu sun kasance a cikin Banu Israila, dayansu ya kasance yana aikata zunubi, dayan kuma mai qoqarin ibada, sai ya kasance mai qoqarin ibadar bai gushe ba yana ganin dayan akan zunubi ya ke, sai ya rinqa cewa da shi ka rage!, sai wata rana ya tarar da shi yana aikata zunubi, sai ya ce ma sa: ka bari! sai shi kuma ya ce: ka bar ni tsakanina da Ubangijina, an sanyaka ka zamanto mai bibiyata ne koda yaushe? Sai ya ce: “Na rantse da Allah! Allah ba zai gafarta maka ba”, ko kuma “Allah ba zai shigar da kai aljanna ba” sai aka dauki rayukan su, sai su ka hadu a gurin ubangiji maaukakin Sarki, Sai Allah madaukakin Sarki ya cewa mai qoqarin ibada; “Ka san ni ne? ko kuwa kana da iko da abin da ke hannuna?” Sai ya cewa mai aikata zunubin; “ka tafi ka shiga al-jannah da rahama ta,” sai yace da dayan; “a tafi da shi zuwa wuta."
Abu Hurairah (ra) ya ce: “Na rantse da wanda raina ya ke hannunsa; ya fadi kalmar da ta jawo ma sa asarar duniyarsa da lahirarsa." - (Abu Dawud: 4901. Kuma Al-Hafiz Al-Iraqiy ya ce: Hadisi ne Hasan. Takhriju ahadisi Ihyau Ulumid-Din, juzui na 5, shafi na 2039).
Wannan ya nuna yadda wasu suke ji da ibadarsu, su na ganin cewa su na da wani girma a gurin Allah, amma ragowar mutane ba komai ba ne. Wadansu ma shaidan ya shige su, har su na da'awar sun fi annabawa, su na mayar da kan su alloli. Haqiqa wannan bata ne da tabewa da asarar rayuwa duniya da lahira. Allah ya shirye mu baki daya. ≤p> wasu kuma sun rudu har su na cewa wasu bayin Allah sun gafarta mu su zunubansu, ko kuma su rinqa jin cewa ai su yanzu ba su da wata matsala, har su rinqa rabawa mutane aljanna ko kuma su yi mu su alqawarin za su cece su a ranar alqiyama, wasu har tabbas su ke bawa mabiyansu da su yi duk abinda su ke so sun lamince mu su. Alal haaqiqa shaidan ya yi wasa da wadannan, kuma sun nuna ba su san Allah ba don haka ba sa jin tsoronSa da ganin girmanSa da kwarjininSa.
Amma manyan annabawa Ulul Azmi da su ka san girman Allah dari-dari su ke yi da shi, duk kuwa da matsayin da su ke da shi a wajensa ba sa kallon yawan ibadarsu, su na jin kunyar haduwa da shi sakamakon laifi guda daya da su aganinsu su ke ganinsa babban laifi ne, duk kuwa da cewa a wajen Allah wannan laifin na su abin yafewa ne.≤p> Manzon Allah (saw) ya ba mu labarin cewa: idan aka tashi alqiyama mutane za su shiga halin damuwa da tashin hankali, za a sauko da rana qasa-qasa, gumi zai shanye wasu mutane, qwaqwalen wasu mutane za su tafarfasa. Sai Allah (swt) ya kimsa wa wasu daga bayinSa muminai cewa su je wurin manyan manzanni Ulul Azmi su nema mu su ceto. Manzon Allah (saw) ya ce:
“Sai su je wajen annabi Adam (as) sai su ce ya Adam! Kai ne uban bani Adama, Allah ya halicce ka da hannunSa, kuma ya busa ma ka rai daga ruhinSa, kuma ya umarci mala'iku su ka yi ma ka sujjada, ka nema mana ceto a wajen Ubangijinmu, shin ba ka ga halin da muke ciki ba? Shin ba ka ga abinda ya ame mu ba? Sai Annabi Adamu (as) ya ce: “lallai a yau Ubangijina ya yi fushin da bai taba yin irinsa ba ba kuma zai qara yin irinsa ba a bayan sa, kuma lallai Ubangijina ya hana ni cin wata bishiya sai na saba ma sa, don haka ta kai na nake yi, ku tafi wajen wani na, ku tafi wajen annaabi Nuhu (as).
Sai su je wajen Annabi Nuhu (as) sai su ce ya Nuhu: “kai ne farkon manzanni a ban qasa, kuma Allah ya kiraka bawa mai yawan godiya, ka nema mana ceto a wajen Allah, shin baka ganin halin da mu ke ciki? Shin ba ka ga abinda ya same mu ba?” Sai Annabi Nuhu (as) ya ce: “lallai a yau Ubangijina ya yi fushin da bai taba yin irinsa ba, ba kuma zai qara yin irinsa ba a bayan sa, lallai ni na yi wata addu'a akan al'ummata, don haka ta kaina na ke yi.
Ku tafi wajn wani na, ku tafi wajen Annabi Ibrahim (as)."
Sai su tafi wajen Annabi Ibrahim (as) sai su ce da shi: “ya Ibrahim! Kai annabin Allah ne kuma badadinsa daga mutanen da ke ban qasa, ka nema mana ceto a wajen Allah shin ba ka ganin halin da mu ke ciki? Shin ba ka ga abinda ya same mu ba?" Sai shi ma ya ce da su: “lallai a yau Ubangijina ya yi fushin da bai taba yin irinsa ba, ba kuma zai qara yin irinsa ba a bayan sa, sai ya fadi maganganunsa guda uku da ya yi tauriyya (Tauriyya it ace mutum ya fadi magana mai hrshen damo wadda za a fahimci ma'nar da shi kuma ba ita yake nufi ba) a cikin su saboda hikima ta da'awa, don haka ta kaina na ke yi. Ku tafi wajen wani na, ku tafi wajen Annabi Musa (as)."
sai su tafi wajen Annabi Musa (as), sai su ce: “ya Musa kai ne wanda Allah ya fifita ka da manzancinsa da kuma yin zance da kai akan sauran mutane, ka nema mana ceto a wajen Allah, shin ba ka ganin halin da mu ke ciki ba ? shin baka ga abinda ya same mu ba?” Sai shi ma ya ce da su: lallai a yau Ubangijina ya yi fushin da bai taba yin irinsa ba ba kuma zai qara yin irinsa ba a bayan sa, lallai ni na kashe wata rai wadda ba a umarce ni da kashewa ba, don haka ta kaina na ke yi.
Ku tafi wajen wani na, ku tafi wajen Annabi Isa (as)" sai su tafi wajen Annabi (as),sai su ce: ya Isa! Kai Manzon Allah ne, kuma ka yi Magana da mutane kana cikin zanin goyo, kuma kai Kalmar Allah ce da ya sanya ta a mahaifar Nana Maryam kuma ruhi ne daga gare shi.
Ka nema mana ceto a wajen Allah (swt), shin ba ka ganin halin da muke ciki? Shin ba ka ga abinda ya same mu ba?"Sai ya ce: lalli Ubangijina ya yi fushin da bai taba yin irinsa ba a yau kuma ba zai yi irinsa ba a nan gaba, (bai fadi zunubinsa ba, amma duk da haka zai ce): ta kaina nake yi, ku ta fi wajen wani na, ku tafi wajen Annabi Muhammad (saw)".
Sai su je wajen Manzon Allah (saw), sai su ce ya Muhammad (saw)! Kai Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa, Allah ya gafarta ma ka abin da ya gabata daga zunubanka da ma wanda baka yi ba. Ka nema mana ceto a wajen ubangijinmu, shin ba ka ganin halin da muke ciki ? shin ba ka ga abinda ya same mu ba?"
Manzon Allah (saw) ya ce: “sai na je qarqashin al'arshi na yi sujjada ga Ubangijina, sai ya yi min budi kuma ya kimsa min godiya da kykyawan yabo a gareshi, wanda ba a taba budawa wani irinsa kafi na ba." sannan Allah madaukakin sarki ya ce: “dago kanka, tambayi abinda ka ke so a baka, ka nemi ceto za a baka", sai na dago kaina, sai na ce “ya Ubangiji al'ummata al'ummata" sai a ce “ka shigar da al'ummarka wadanda babu hisabi akansu ta qofar dama, sannan su yi tarayya da sauran mutane ta sauran qofofin.." (Bukhari: 4343, Muslim: 287).
[color=maroon To idan har wadannan manyan manzanni ulul-azmi za su zama ma su qanqan da kai da jin tsoron ubangiji tare da ganin qwarjininsa su ka sa tunkararsa a wannan rana saboda kuskure guda daya wanda kuma an tabbatar mu su da cewa an yafe mu su shi; wane mutum ne zai iya daga kai, ko ya yi qafafa da girman kai saboda 'yar guntuwar ibadar da bashi da tabbas ko an karba ko ba a karba ba, kuma shin an yarda da shi ko ba a yarda da shi ba? Har ya ce zai yafewa mutane zunubasu ko ya ce da mutane su yi abinda su ka ga dama ya lamunce mu su? Lallai a cikin wannan mummunan tunani a kwai rudin shaidan da rudin zuciya da rashin darajanta Allah da rashin sanin qimar addininsa. Allah ka kiyashe mu don rahamarKa.
°
°
Sai mun hadu a fito ta 12 da yardar Allah
Comments
Post a Comment