GIRMAN KAI KASHI NA BIYU.
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
Tambaya Ta 1:
Mene ne GIRMAN KAI da JIJI DA KAI?
AMSA: Girman kai shi ne qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane.
Wannan ma'ana ta zo a cikin hadisin Abdullahi bn Masud (ra) cewa wani mutum ya tambayi manzon Allah (saw) game da girmankai sai, manzon Allah (saw) ya ce: “Girman kai shi ne qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane”. - (Sahihu Muslim:167).
Shi kuwa jiji da kai shi ne mutum ya riqa alfahari da taqama da fankama da baiwar da Allah ya ba shi ta asali ko ilimi ko sarauta ko kyawun halitta ko yawan dukiya da sauran su.
Tambaya Ta 2: Girman kai nau'i nawa ne?
AMSA: Girman kai naui biyu ne: 1. Girman kai na kafurci. Misalinsa shi ne girman kan da Iblis ya yi wa Allah (swt). Da kuma kafurai da su ka kafircewa Allah da Annabawa. 2. Girman kai na sabo. Wannan shi ne mutum ya riqa qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane.
Sai mun hadu a fitota 03 da yardar Allah
Allah yasa mudace. Ameeeeen
Comments
Post a Comment