GIRMAN KAI KASHI NA BIYAR
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?
Ci gaba...
2- Arziki ko yawan dukiya:
Su kan sanya mutum girman kai da ji-ji-da-kai da alfahari da wulaqanta wanda ba shi da shi kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya ba mu labarin Qaruna da dukiyar da yake da ita da dagawar da yake yi wa alummarsa.
Allah (swt) ya ce:
“Haqiqa Qaruna ya kasance daga cikin mutanen annabi Musa sai ya yi mu su dagawa. Mun ba shi taskoki (ma su yawa) wadanda makullansu su kan yiwa jama'a ma su qarfi nauyin dauka. Ya yin da mutanen sa su ka ce ma sa, kar ka yi GIRMAN KAI, da alfahari domin haqiqa Allah ba ya son ma su girman kai da alfahari." - (Suratul Qasas, aya ta 76).
Wannan ayar ta nuna mana cewa, Allah madaukakin Sarki wanda ya halicce mu kuma ya ke da cikakken arziki, kuma ya ke bayar da arziki ga wanda ya ga dama ya hana mu yin girman kai da alfahari da dagawa akan dukiyar da ya bamu, domin yin haka ya kan sanya mutum ya halaka kamar yadda Qaruna ya yi aka halaka shi, kuma ya kan sa mutum ya rasa lahirarsa kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya ce:
"Wancan gidan na lahira mu na sanya shi ne ga wadanda basa nufin dagawa da fasadi a ban qasa. Haqiqa kyakkyawan qarshe yana tabbata ne ga ma su tsoron Allah." - (Suratul Qasas, aya ta 83). _
Abin mamaki a nan shi ne, mafi yawa waexanda su ka tara dukiyar haram; ko dai ta hanyar sata, ko qwace, ko cin dukiyar marayu, ko ta hanyar zalunci, su su ke girman kai da alfahari da jiji da kai da wulaqanta mutane saboda su na riqe da dukiya. Allah ka shirye mu, amin.
° ° ° °
Sai mun hadu a fito ta 06 da yardar AllAH
Comments
Post a Comment