GIRMAN KAI KASHI NA TARA.
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?
Ci gaba...
5- Qarfi:
Qarfin jiki yakan sanya mutum yin girman kai da ji-ji-da-kai da jin isa da dagawa. Irin wannan ya faru ga Adawa a lokacin da Annabinsu Annabi Hudu (as) ya ke kiran su zuwa bautawa Allah, sai su ka yi girman kai. Kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Su kuwa Adawa sai su ka yi girman kai a ban qasa ba tare da wani haqqi ba, kuma su ka ce: wane ne ya fi mu qarfi? Shin ba su gani ba cewa haqiqa Ubangijin da ya halicce su shi ne mafi qarfi fiye da su? Kuma sun kasance su na jayaya da ayoyinmu.” - (Suratul Fussilat, aya ta 15).
Wannan aya tana nuna yadda Adawa su ka yi girman kai da dagawa saboda qarfi da Allah ya ba su, su ka manta cewa Allah da ya halicce su shi ne ya halicci qarfin, kuma shi ne ya ba su shi, mai makon su gode ma sa sai su ka qalubalanci annabinSa da cewa: wane ne ya fi mu qarfi?
Haka ma, qarfin tsaro da qarfin makamai ya kan sanya girman kai da fasadi a ban qasa, da mayar da sauran mutane bayi, kamar yadda Yahudawan Banun Nadhir su ka yi, su na zaton cewa, ko da za a yi yaqi, musulmai ba za su iya samun galaba akansu ba, saboda ganuwa da su ke da ita, da tanadi da su ke da shi. Allah madaukakin Sarki ya ce: Kuma su ka yi zaton cewa ganuwar su (da tanadin su) za su kare su daga Allah, sai Allah ya bullo mu su ta inda ba su zata ba." - (Suratul Hashari, aya ta 2).
Wannan ayar na nuni akan yadda wasu kabilu kamar yahudawa da sauransu, da wadansu manyan qasashen yamma ma su qarfin tsaro da tattalin arziki, su ke jiji da kai da dagawa, da fasadi a ban qasa da hada fitina tsakanin al'umma, da mayar da ragowar qasashe kamar bayinsu. Sun gafala cewa Allah (swt) zai iya karya su ta yadda ba su zata ba kamar yadda ya karya tarayyar Soviet da ke Rasha? Haqiqa shi Allah ba a ja da shi!
Sai mun hadu a fitowa ta 09 da yardar Allah
Comments
Post a Comment