Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’
Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’ Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a wannan fili Na samu sakonni mata da yawa da suka nemi na yi bayanin yadda za su rabu da kurajen ‘pimples’. Duk da na ta taba gabatar da irin wannan bayanin, amma sakamakon neman da mutane suka yi na ga dacewar maimaitawa. Ga bayanin hanyoyin da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’: (1) Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki. (2) Ki kasance mai yawan shan ruwa. Yana da kyau duk inda za ki je ki sanya ruwa a Cikin jakarki ba wai dole sai kayan...