Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’
Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da
kurajen ‘pimples’
Assalamu alaikum, barkanmu da
sake saduwa a wannan fili Na
samu sakonni mata da yawa da
suka nemi na yi bayanin yadda za
su rabu da kurajen ‘pimples’.
Duk
da na ta taba gabatar da irin
wannan bayanin, amma
sakamakon neman da mutane
suka yi na ga dacewar
maimaitawa.
Ga bayanin
hanyoyin da za ki bi wajen
rabuwa da kurajen ‘pimples’:
(1) Da farko ana so awa biyu ko
uku kafin ki kwanta barci sai ki
shafa man goge baki a fuskarki,
musamman wuraren da kurajen
pimples suke da yawa. Ba
kowane irin man goge baki za ki
shafa ba, ana so ki shafa farin
man goge baki ne. Idan kin ga
dama za ki iya wanke fuskarki
idan man goge bakin da kika
shafa ya kai minti 30, idan kin ga
dama kuma za ki iya kwantawa
da shi har zuwa wayewar gari. Za
ki rika maimata hakan har zuwa
wadansu kwanaki, idan kin yi
hakan za ki ga canji a fuskarki.
(2) Ki kasance mai yawan shan
ruwa. Yana da kyau duk inda za
ki je ki sanya ruwa a Cikin jakarki
ba wai dole sai kayan kwalliya ba.
Yawanta shan ruwa ba wai zai
sanya miki laushin fata ba ne
kawai, a’a, zai taimaka miki wajen
yaki da kurajen pimples din da
suke fuskarki. Haka yana da kyau
ki guji yawan cin abincin
gwangwani, kasancewar suna
dauke da wasu sinadarai da za
su rika sanya kurajen fuska. Ya
kamata ki yawaita cin ‘ya’yan
itatuwa da suka hada da su
abarba da lemu da ayaba da
kankana da sauransu.
(3) Ki rika amfani da abin
shafawar da ake kira ‘Antiodident
spray’, irin su Jane Iradale da
Neutrogenia Rapid Clear da Acne
Eliminating Spot Gel da
sauransu, hakan zai taimaka miki
wajen daidaita man da ke fatarki,
wanda masana fata suka ce idan
ya yi yawa yakan haifar da
kurajen fuska.
(4) Ki kasance mai amfani da
man ‘Cornmeal’ a fuskarki, yakan
sanya kurajen fuska su motse
sannan a hankali su bace, misali
man shi ne, Intagilo Clear Sal
Cleanser. Sannan ki rika amfani
da man da ke hana yaduwar
kwayar cutar bakteriya, irin
wannan man yakan ratsa kofofin
da suke fatar fuskarki da ma
jikinki gaba daya, sannan yana
yakar kwayoyin cutar da suke
fatarki, a lokaci guda ya daidaita
miki yawan man da yake fitowa
daga fatarki. Zai kuma cire miki
kwayoyin halittar da suka mutu a
cikin fatarki. Misalinsu; Phytomer
Gommage da Luffa-0.
(5) Yana da kyau ki ware wata
rana ko wadansu ranaku a cikin
mako ba tare da kin shafa kayan
kwalliya a fuskarki ba, hakan zai
bai wa fatar fuskarki samun
‘yancin shigar da kuma fitar da
iska ta kofofinta ba tare da wani
cikas ba. Haka idan za ki shafa
kayan kwalliyar a fuskarki, to ki yi
amfani da kayan kwalliyar da ba
sa toshe kofofin fatar fuska.
(6) Ki kasance mai shafa mai
domin fatar fuskarki ta kasance
cikin danshi, kasancewar
wadansu kurajen fuskar sun fi
bata fuska idan fuska tana bushe.
(7) Yi amfani da man ‘Tea Tree’
domin ba wai kawai yana baje
kurajen fuska ba ne, a’a yana
rage karfinsu da kuma kalarsu. Za
ki sami ire-iren wadannan man a
shagunan sayar da kayan
kwalliya na zamani.
(8) Ki kasance mai yin taka tsan-
tsan wajen amfani da ire-iren
man shafawar da kike amfani da
su a gashin kanki, ma’ana kada ki
sake ya rika taba fuskarki hakan
zai iya haifar miki da kurajen
fuska, kasancewar wadansu
sinadaran an yi su don su
taimaka wa gashin kai ne, don
haka idan suka shiga kofofin fatar
fuskarki, sai su haifar miki da
matsala.
(9) Ki kasance mai gasa kurajen
fuskarki: Duk lokacin da kurajen
pimples suka fito miki sai ki samu
wani kyalle mai tsafta, sai ki
tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda
ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai
ki fito da shi, sai ki rika dora shi a
kan wajen da kurajen suke,
sannan ki rika gogawa a hankali,
zafin kyallen yakan sa kurajen su
motse daga nan su mutu.
(10) Ki guje yin amfani da
hannunki wajen fasa kurajen da
suke fuskarki, domin hakan yana
kara yawansu hade da sanya
fuskarki ta kara cabewa.
kurajen ‘pimples’
Assalamu alaikum, barkanmu da
sake saduwa a wannan fili Na
samu sakonni mata da yawa da
suka nemi na yi bayanin yadda za
su rabu da kurajen ‘pimples’.
Duk
da na ta taba gabatar da irin
wannan bayanin, amma
sakamakon neman da mutane
suka yi na ga dacewar
maimaitawa.
Ga bayanin
hanyoyin da za ki bi wajen
rabuwa da kurajen ‘pimples’:
(1) Da farko ana so awa biyu ko
uku kafin ki kwanta barci sai ki
shafa man goge baki a fuskarki,
musamman wuraren da kurajen
pimples suke da yawa. Ba
kowane irin man goge baki za ki
shafa ba, ana so ki shafa farin
man goge baki ne. Idan kin ga
dama za ki iya wanke fuskarki
idan man goge bakin da kika
shafa ya kai minti 30, idan kin ga
dama kuma za ki iya kwantawa
da shi har zuwa wayewar gari. Za
ki rika maimata hakan har zuwa
wadansu kwanaki, idan kin yi
hakan za ki ga canji a fuskarki.
(2) Ki kasance mai yawan shan
ruwa. Yana da kyau duk inda za
ki je ki sanya ruwa a Cikin jakarki
ba wai dole sai kayan kwalliya ba.
Yawanta shan ruwa ba wai zai
sanya miki laushin fata ba ne
kawai, a’a, zai taimaka miki wajen
yaki da kurajen pimples din da
suke fuskarki. Haka yana da kyau
ki guji yawan cin abincin
gwangwani, kasancewar suna
dauke da wasu sinadarai da za
su rika sanya kurajen fuska. Ya
kamata ki yawaita cin ‘ya’yan
itatuwa da suka hada da su
abarba da lemu da ayaba da
kankana da sauransu.
(3) Ki rika amfani da abin
shafawar da ake kira ‘Antiodident
spray’, irin su Jane Iradale da
Neutrogenia Rapid Clear da Acne
Eliminating Spot Gel da
sauransu, hakan zai taimaka miki
wajen daidaita man da ke fatarki,
wanda masana fata suka ce idan
ya yi yawa yakan haifar da
kurajen fuska.
(4) Ki kasance mai amfani da
man ‘Cornmeal’ a fuskarki, yakan
sanya kurajen fuska su motse
sannan a hankali su bace, misali
man shi ne, Intagilo Clear Sal
Cleanser. Sannan ki rika amfani
da man da ke hana yaduwar
kwayar cutar bakteriya, irin
wannan man yakan ratsa kofofin
da suke fatar fuskarki da ma
jikinki gaba daya, sannan yana
yakar kwayoyin cutar da suke
fatarki, a lokaci guda ya daidaita
miki yawan man da yake fitowa
daga fatarki. Zai kuma cire miki
kwayoyin halittar da suka mutu a
cikin fatarki. Misalinsu; Phytomer
Gommage da Luffa-0.
(5) Yana da kyau ki ware wata
rana ko wadansu ranaku a cikin
mako ba tare da kin shafa kayan
kwalliya a fuskarki ba, hakan zai
bai wa fatar fuskarki samun
‘yancin shigar da kuma fitar da
iska ta kofofinta ba tare da wani
cikas ba. Haka idan za ki shafa
kayan kwalliyar a fuskarki, to ki yi
amfani da kayan kwalliyar da ba
sa toshe kofofin fatar fuska.
(6) Ki kasance mai shafa mai
domin fatar fuskarki ta kasance
cikin danshi, kasancewar
wadansu kurajen fuskar sun fi
bata fuska idan fuska tana bushe.
(7) Yi amfani da man ‘Tea Tree’
domin ba wai kawai yana baje
kurajen fuska ba ne, a’a yana
rage karfinsu da kuma kalarsu. Za
ki sami ire-iren wadannan man a
shagunan sayar da kayan
kwalliya na zamani.
(8) Ki kasance mai yin taka tsan-
tsan wajen amfani da ire-iren
man shafawar da kike amfani da
su a gashin kanki, ma’ana kada ki
sake ya rika taba fuskarki hakan
zai iya haifar miki da kurajen
fuska, kasancewar wadansu
sinadaran an yi su don su
taimaka wa gashin kai ne, don
haka idan suka shiga kofofin fatar
fuskarki, sai su haifar miki da
matsala.
(9) Ki kasance mai gasa kurajen
fuskarki: Duk lokacin da kurajen
pimples suka fito miki sai ki samu
wani kyalle mai tsafta, sai ki
tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda
ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai
ki fito da shi, sai ki rika dora shi a
kan wajen da kurajen suke,
sannan ki rika gogawa a hankali,
zafin kyallen yakan sa kurajen su
motse daga nan su mutu.
(10) Ki guje yin amfani da
hannunki wajen fasa kurajen da
suke fuskarki, domin hakan yana
kara yawansu hade da sanya
fuskarki ta kara cabewa.
Comments
Post a Comment