jega

Hukumar zaben Nigeria na can na gudanar da
wani taro domin yanke hukunci akan ko za a
gudanar da zaben kasa baki daya ranar asabar
mai zuwa.
Hukumar na ganawa ne da wakilan dukkanin
jam'iyyun kasar domin yanke shawara.
Wannan ganawa ta zo ne bayan ganawar da
Majalissar Kasa ta yi ranar alhamis inda aka
shafe awa bakwai ana tattaunawa akan batun
zaben.
Bayan da aka kammala taron wanda ya samu
halartar tsaffin shugabannin Nigeria da
gwamnoni da manya manyan jami'an tsaro, an
shawarci hukumar zabe ta yi la'akari da halin
da ake ciki na tsaro wajen yanke shawarar
ranar da za a gudanar da zaben.
Shugaban hukumar zaben dai ya gabatar da
hujjojinsa na cewar a shirye hukumar ta ke ta
yi zaben ranar 14 ga watan Febrairu
Saidai wasu rahotanni na cewar manyan
jami'an tsaro sun gabatar da kukan cewar ba
zasu iya bayar da tabbascin tsaro ba idan aka
ce za a yi zaben ranar asabar mai zuwa.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA