TARIHIN KANO A Takaice
Kano sunan babbar kasar Hausa ce kuma masarauta ce mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewaye. Haka kuma Kano gari ne babba wanda ya kunshi kabilu masu yawa tare da harkokin arziki. Gari ne mai manya manya malamai kamar su mallam Nasiru Kabara,Shehu Abubakar Atiku,Shek Ja'afar Mahmud Adam. Sanna Garine Mai tarin Ya'nkasuwa kamar su Aliko Dan Gote,Aminu Alhasan Dantata,Mallam Isyaka Rabi'u da dai sauran su.
Yawan mutanen da suke garin Kano yakai kimanin mutane Miliyan Goma (10,000,000) a kidayar da aka yi a shekara ta 2006. Kano tana da matukar tasiri a yawan mutane a Najeriya, saboda ita ce ta fi kowace jiha yawan mutane a Najeriya. Idan ka zo Kano za ka samu mutane daga ko'ina a fadin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, haka kuma za ka tarar da mutanen Sin, da kuma na kasashen Larabawa kamar Sudan, Misira (Egypt), Lebanon, da kuma mutanen kasashen Turai.
Kano ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci, haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can Kano tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya. Jihar Kano tana da iyaka da misalin jihhohi hudu su ne :-
Jihar Kaduna
Jihar Katsina
Jihar Jigawa
Jihar Bauchi
Comments
Post a Comment