Alkwari Na 3

ALKAWARI 3

babu komai na taimake kane saboda Allah bani bukatar wata godiya daga gareka, nima wata rana zan iya zuwa agunka domin neman taimako". haba haleematu ni ai banida wani abu wanda zaki nema aguna. Na kare maganta tareda yimata kallo wanda yake nuna alamar mamaki "hmm hausawa fa sunce ba'a san inda rana ke faduwa ba" haleematu tafada tana kallona...

inkau har akwai abinda zaki nema aguna to na tabbata dakin nema nikuma zanyimaki koma minene.... Ahaka dai mukayi bankwana, sannan tajuya fuskarta ixuwa inda wasu mutane da suke zaune, da alama yan aikin gidan ne, sannan takira " sadam! Sadam!!" har sau biyu, sannan naji wani ya amsa "na am hajiya" tache kakai wannan mutumen a katsina "angama hajiya" yafada atakaiche...

Daganan muka dauki hanya muka doshi garin katsina... Bamu zame ko inaba sai unguwar tudun wada, sadam dreba ya saukeni adai dai kofar gidanmu sannan yakada motarsa tareda kugamata wuta.... Ina shiga gida khadija ce nagani aduke tana hura wuta, sallamar danayi ne yasanya ta dago kanta. Da gudu ta nufoni tayi tsalle tafada ajikina tareda fadar yaya yaya, hawayenda suka zubo daga idanuwanta ne suka hanata fadar wata magana, saidai murmushi kawai takeyi wanda bayada maraba da dariya, sai alokacin nagane hawayen murna ne takeyi..

Khadija kanwata ce itace yar auta a gidanmu, mu ukku ne mahaifinmu ya rasu yabari, ni sai ahmad sannan khadija. Jin muryata ne yasanya mahaifiyata fitowa daga daki cikin murna muna hada ido da ita, kawai sai naga ta duka ta daga hannuwa sama tanayima Allah godiya da yamaido mata danta. Bayan nazauna ne umma tanemi tasan abinda yafaru dani, nikuma nakwashe komai nafada mata tundaga farko har karshe...

Bayan nagama ne nake tambayarsu ina ahmad?? Sallamar da akayi itace ta hana su umma bani amsar tambayar danayimasu... Wani dan saurayi ne yashigo tareda tambayar "anan ne gidan su ahmad bashir muhammad? Nace eh nanne, kafin inkara wata magana, sai naji yakuma cewa "ana bukatar ganinku da gaggawa saboda yanxu haka yana emergency a general hospital sakamakon mota data kadeshi" nan take muka dunguma xuwa asibiti.

Dukda bawani nisa kedakwai ba daga unguwar tamu xuwa asibitin ba amman saida mukahau mota kirar (keke napep), wadda kanawa suke kira da (adaidaita sahu). Shigarmu keda wuya muka dauki hanyar da zata sadamu da emergency, muna shiga muka nufi dakinda ake kai yan accident, wani likita yataso yatarbi gabanmu tareda fadar muyi hakuri yanxu ana chikin dubashi idan angama za'a yimaku magana, yanuna mana wasu kujeru dake jere ajikin bango, muka zauna...

Jim kadan saiga wani dan tsamurmurin likita yafito mai wani katon kai, fuskarshi da alamar damuwa karara kamar wanda yake shirin yin kuka, cikin hanzari natashi nakarasa agunshi tareda tambayarshi likita ya jikin nashi?? Sunkuyar dakai yayi daga bisani kuma sai yadago kansa tareda fadar.....




Dago fuskarsa yayi, wadda tuni hawaye sunyimata kawanya sannan yakara dacewa, "munyi iyakacin kokarinmu naganin mun ceci rayuwar wannan bawan Allah, amman babu yadda zamuyi Allah yariga ya yanke hukunci, saidai kawai aci gaba dayimasa addu'a Allah yajikansa kuma ya gafartamai!!!"

yana gama fadin maganarsa kawai yawuce gaba batareda yatsaya yin wani abuba, Umma dake tsaye a gefenmu babu abinda ke fita daga bakinta sai "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"yayinda khadija kau kuka kawai take rusawa abinta batama ko tinanin acikin mutane take..... Koda yaushe umma acikin tinanin rashin ahmad take, munyimata magana wannan tinanin zai iya haifar mata da matsala, amman taki saurarenmu sai abinda yayi gaba.

Bayan rasuwar ahmad da sati daya, inacikin daki sai naji karar khadija, cikin sauri nafito domin inga abnda ke faruwa. Umma ce nagani kwance abakin kofa dasauri nakarasa na tambayi khadija lfy miya faru?

Bantsaya jin amsa daga garetaba kawai nafita waje dasauri nasamo mota bamu zame ko inaba sai asibiti... Batare da bata lokaci ba akashiga da ita domin duba lfyarta....

Mundauki kamar awa guda (1hour) zaune sai wata likita mace tafito, cikin hanzari natashi na tarbeta tunkafin takaraso nake tambayarta doctor tana ina? Dagamin hannu tayi tana magana ahankali, "ku kwantar da hankalinku munyi iya gwaje gwajenda zamuyi mungano cewa jininta ne ya hau, saidai kuma faduwar datayi tasamu matsala a kashin bayanta..."

tanagama magana sai na tambayeta, likita yanxu miye abin yi? Batareda tabani amsa ba, sai dai ta nunamin wani office tace inshiga likitan da zaiyimata aiki yana nan ciki, Shiga nayi da sallama sannan nazauna akan daya daga cikin kujerun da aka tanada domin masu ganin likita... Zaune yake hankalinshi kwance, ya dukar da kanshi a kasa yanata wasu yan rubuce rubuce, daga bisani kuma yadago kanshi "kune wa anda kukawo wannan matar?"

yakarasa tambayarsa yana kallona ta cikin siririn farin gilashin dake sanye a fuskarsa. Gyada kai nayi kamar kadangare cikin wata sarkakkar murya nabashi amsa "eh nine" atakaice... Sannan yace marar lafiyar tana bukatar aiki sakamakon faduwa datayi akan wani abu wanda yayi silar fitar wani kashi daga cikin kasusuwan bayanta, kuma kashin da yafita bai tsaya a'inda yakeba, ya bar wurinsa yafada akan (spinal code) wanda hakanne yasanya bata iya yin komai dakanta, tundaga kugunta har zuwa kafafuwanta sundaina aiki, bazata iya yin komaiba, kuma kome zakayimata bazatasan kanayi ba, daga kugunta xuwa abinda yayi samnta har kanta nanne kawai zaka taba taasan kataba.

kuma bakomai bane yasanya haka sai wannan kashin daya je agun (spinal code) din yayi kane kane. Yanxu dole sai anyimata aiki, kuma ana bukatar kudi (naira dubu dari da ashirin) kuma tana bukatar aiki da gaggawa sbd kashin yanada tsini, idan ba'ayi aiki da gaggawa ba zai iya yin silar datsewar (spinal code) din, kuma idan tadatse babu maganar gyarawa saidai hukuncin Allah. Nan take zufa tayoman lale marhaban, duk ta mamaye jikina kamar wanda aka tsamo daga cikin teku, tinani na kawai ina zansamo wa'annan kudin, nan take natuna da chek dinda yasmeen tabani lokacinda zata tafi makaranta, cikin azama da kwarin guiwa na nufi gida, ina shiga na nufi dakina, wanda yakoma kamar dakinda mahaukata ke kwana, kana shiga wasu ledoji ne bakake da farare, zasu rinka yimaka barka daxuwa, daga gefen hannun dama kuma wasu kujeru ne murgudaddu wa'anda suke shirin burmawa da duk wanda yazaunasu batareda ixni ba, gefen haggu kuma wani teburi ne wanda yake kama da teburin masu shayi, a samanshi wata tsohuwar t.v ce black and white wadda nima bansan shekarunta ba, daga kasa kuma wata shekararriyar radio ce wadda marhin gidan kaset dinta ya dade da tafiya yawon duniya, daga ganin radion zaka fahimci ita kanta ganimarta aka ciwo, daga sama kuwa wata fanka ce take juyawa wadda take barazanar fadoma dukwanda ya isheta da kallo.....

Tsalle nayi nafada akan katifata wadda batada maraba da kasa sbd tsabar tauri, wata kura ta tashi tareda wasu kwa

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA