ALKAWARI NA 1

ALKAWARI . Part 1.

Yunkuri nayi domin intashi amman naji gaba daya nakasa yin komai sakamakon rashin karfin jikina, wani zafi naji a hannuna kamar antsiramin wani abu cikin hanzari nayi sauri na dagashi, sai lokachin nalura da wata allura soke ga hannu na dawata roba doguwa, nanne nabi robar dakallo har inda tushenta yake, abinda idanuwa na suka gani shine yadauremin kai tare da bani mamaki.

Ledar jini che nagani arataye, yana biyowa tachikin wannan roba mai allura yana shiga achikin jikina. A chikin zuchiyata nake tambayar kaina, mike faruwa ne har ake karamin jini? Nanne nakali kane na wanda yaketa murna yana faman danna wayarsa domin yakira umma na yafada mata na farka amman ntwrk ya hanashi, kunsan network din 9ja da matsala...

nache ahmad meyafaru dani ne akemin karin jini, budar bakinshi sai yache "yaya yusuf awarka ashirin da hudu kwanche anan, wannan itache leda ta ukku da akasanya maka" rufe bakinshi ne yayi dai dai da turo kofa da akayi,....

wani mutum ne mai matsaikachin tsayi da alama shine likitan dayake kula dani saboda ganin yadda yayi shiga ta fararen kaya kamar wata sabuwar gawa. ba tareda wani bata lokachi ba ya karaso a'inda nake kwanche, tare da tambayar kanena chewa, tunyaushe yafarka? sai yachemai "yanxu yafarka bada dadewa ba", a nanne naga yabuda wani file dake hannunsa yana karantawa tachikin siririn farin gilashin dake sargafe a idanuwansa, batare da ya sakeyin magana ba yabude kofa yafiche abinsa.

Jim kadan sai gashi yadawo da magunguna achikin leda, yaba kanena tare da umurtarshi yadda zaya bani maganin. Ananne ya yafiddo yabuda yabani wasu kwayoyi tareda ruwa achikin cup domin insha, amman achikin raina inata kokonto wane asibiti ne wannan masu bada magani kyauta batare da masu jinya sunbiya kudi ba? Ina gama shan maganin, najuya domin ajiye kofin akan wani dan teburi dake gefen gadon da nike kwanche, ananne naga wata yar dunkulalliyar takarda wadda ake kimlache sako mai mahimmanchi achikinta, wadda ake kira da "envelop",

nadauka tareda kokarin duba ko minene achiki. sunan yasmeen ne nagani abayan takardai wannan ne yasa na kagu da inbude domin ganin abinda ke kunshe achiki, ina budawa sai naga wata yar takarda mai dan tsawo ta fado daga chikin envelop din, chikin hanzari nasanya hannu nadauka tareda duba abinda ke achiki, wanda idanuwa na suka bani tabbachin chek ne nabanki, mai dauke da kudi naira naira dubu dari biyar, 500,000naira a rubuche, tare da sa hannun yasmeen,...

Nanne naji wani irin faduwar gaba, kasanchewar ni bako ne awurin kama kudi masu wannan irin yawa haka, lokachi guda kuma xuchiya ta tambayeni me yasmeen take nufi da wa'annan kudin masu yawa? Idan kyautache tayiman, to miye silar yiman wannan kyautar haka? Ananne namaida hankali na akan envelop sakamakon akwai wata takarda wadda banfiddo ba, hannu na nasanya achikin emvelop din tare da zaro wata takarda wadda take chike makil da rubutu, kamar haka.


Nafara karantawa kamar haka.... "amincin Allah ya tabbata agareka masoyina tauraro acikin taurari, nasan zakayi mamakin abnda nake kokarin sanar dakai sakamakon alkawarin damukayi na zama dajuna har abada, yusuf kasan inasonka kuma na tsani dukwani abnda yake kokarin shiga a tsakaninmu, shiyasa xuchiyata take takaichi tare da tsoron sanar dakai saura kwana biyu jirginmu zai tashi ranar asabar, sbd abbana ya matsa akan dole sai nafita waje nayi karatu, nayi iya kokarina domin inkauda wannan maganar amman abin yachi tura, shiyasa ma haryaje yachi gaba da shirye shirye batareda ya sanar dani komai ba, saida lokachi yakure sannan yafadamin ya samarmin admission, inshirya domin tafiya

"massachusett (code fish) university" dake london... yusuf dan Allah karikemin soyayyata amana zandawo bayan nagama karatuna kuma kai kadaine namijinda xuchiyata takeso amatsayin abokin zaman rayuwa, kuma ga kudinan kaje bank ka amsa domin duba lafiyarka... Daga mai kaunarka "yasmeen jafar muhammad"...

Bayan nagama karanta takardai wasu hawaye sukarinka yin ambaliya suna sulalowa ahankali sunabi tabisa kumatuna, wani sashen xuchiyata kuma yana fadamin "wannan ba abin tada hankali bane, abinda zakuji dadi ne saboda neman ilmi tatafi kuma zata dawo"

wani bangaren nadaga xuchiyata kuma yanata tinanin yadda rayuwata zata kasanche batareda yasmeen ba"... Karar bude kofa naji wanda shine yayi silar fiddoni daga tekun tinaninda na afka, tunkafin sushigo naji sunyi sallama, muryar mahaifiyata che naji tareda kanwa ta suna shigowa, Karasowa tayi agabana tareda yin magana dawani irin launi mai nuna alamar tausayi karara

"yaya yusuf ya jiki" na amsa jiki dasauki kanwata, sai alokachin mahaifiyata ta ida karasowa a'inda nake tareda fadar "sannu dannan kaji ya jikin naka"?? Nikuma sai nafada "da sauki umma" a takaiche...

Lokachinne takalli ahmad dake tsaye abakin gadon ya sanyamu agaba da alama tinanin wani abu yakeyi, umma che takatse shi daga tinanin dayakeyi, "ahmad me likitan yafada ne akansa?"ahmad yadago kansa tareda ba umma amsar tambayar datayimasa "yaji sauki sosai umma, kuma doctor yace idan wannan ledar jinin takare za'a iya sallamarshi gobe in

Allah ya yadda" bakaramin dadi naji ba danaji ahmad yafada gobe za'a sallameni "nasan zankara ganin yasmeen" abnda nafada kenan achikin xuciyata batareda kowa yajiba... Shiru kowa yayi wurin seconds talatin sannan najuya nakalli kanwata tana tayin wasa da yan yatsun hannunta, sannan nakatse shirun da tambayarta, kanwata yau wace rana? "

yaya yusuf yau juma'ah (friday)" atakaiche tafadaman tana kallona da alamar mamaki karara a fuskarta na ganin yanda namanta lissafin kwanaki, nikam bandamu da abnda take nufiba saima wani dadi danakeji achikin raina ina fada gobe asabar in Allah ya yadda kafin su yasmeen su tafi za'a sallameni....

Haka nawuni tunani tareda kosawa gobe tazo, ji nake kamar injuya agogo kawai kowa yaga lokachi yakoma karfe 6 nasafe, wanda danasan abinda zai biyo baya, da banyi zumudin zuwa filin jirgi ba da niyar yima yasmeen bankwana.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA