kuzo sha labari
GATANAN GATANANKU
Wani manomi ne dai ya ke da jakinsa wanda ya ke aiki da shi shekara da shekaru. A kwana a tashi jaki ya fara tsufa har ba ya iya moriyar maigidansa da komai. Da manomi ya ga haka sai ya fara shawarar yadda zai rabu da jaki ko ma ya halaka shi ya huta da ciyar da shi da ya ke yi kullum.
Da jaki ya gane abin da manomi ke shirin kulla masa sai ya gudu. Ya ce a ransa, "Bari na shiga birni na koyi waka, wata kila na zamo mai dogaro da kaina!" Yana cikin tafiya a hanya, sai ya hadu da kare yana kwance a gefen hanya, sai faman fuka ya ke yi. Jaki ya tambayi kare me ya same shi ya ke ta fuka?
Kare ya ce, "Ai da kyar na sha a hannun mai gidana, wai zai kashe ni saboda yanzu na tsufa ba na iya farauto masa komai. Yanzu ina tunanin yadda zan yi da rayuwata in rika samun abinci" Jaki ya ce, "Af! Matsalarmu daya da kai.
Ni zan shiga birni ne na koyi waka, idan za ka bi ni taso mu je." Kare ya tashi ya bi Jaki suka ci gaba da tafiya.Ba su yi nisa da tafiya ba, sai suka hadu da kyanwa a kan hanya, tana tafiya shajaran majaran, kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwan zafi.
Jaki ya dube ta ya ce, "Ah, su maguru 'yan gatan mutane, yau kuma me ya same ki duk kamarki ta canja haka?" Kyanwa ta dubi Jaki ta ce, "Ba dole kamata ta canja ba, uwargijiyata na neman ta halaka ni wai saboda na tsufa, ba na iya kama berayen da suke yi mata barna a gida.
Saidai na sha madara na kwanta a kan shinfida ina lashe jikina. Wai ita ta gaji da ba ni madara tunda ba ni da moriyar komai. Yanzu ban san yaya zan yi da rayuwata ba." Jaki ya ce, "Kai 'yan Adamakwai butulci, mu ma abindaya faru da mu ke nan. Za mu shiga birni mu koyi waka, mu dogara da kanmu, idan za ki bi mu shi ke nan." Kyanwa taamince da bin su.
Jaki da kare da kyanwa suka kama hanya suka nufi birni. Suna cikin tafiya sai suka hadu da zakara, gashin jikinsa a yamutse. Jaki ya tambaye shi abin da ya same shi. Zakara ya ce, "Na yi daron yanka ne! Yau ina cikin hutawa sai na ji maigidana ya kama ni, wai zai yanka wa bakonsa da zai kawo masa ziyara, ni kuwa ban san lokacin da na fizge daga hannunsa ba.
Ina cikin gudu ke nan muka hadu da ku." Jaki ya ce, "Mu ma nan duk guduwa muka yi daga iyayen gijinmu. Za mu shiga birni ne mu koyi waka, idan kana da sha'awa ka biyo mu mu tafi. Zakara ya bi su, suka rangada.
Can sun kusa isa birni sai dare ya yi musu. Jaki ya ce su kwana a nan kafin gari ya waye su shiga birni.
Suka sami wata babbar itaciya, Jaki da Kare suka kwanta a karkashinta, Kyanwa da Zakara kuwa suka hau saman itaciyar. Zakara ya haye can kololuwar itaciya. Da dare ya fara yi sosai, sai Zakara ya kyalla ido ya hango hasken wuta can nesa da su.
Ya fada wa saura, suka ce lalle gida ne inda hasken nan ke fitowa, yana da kyau su matsa can su kwana, da su kwana cikin daji. Suka tashi suka nufi inda hasken ke fitowa har suka zo dab da shi.
Suka ga ashe gida ne, kade- kade da bushe-bushe na fitowa daga ciki. Suka matsa kusa da wani daki da tagarsa take a bude. Da ya ke Jaki ya fi su tsawo, sai ya leka ta tagar.
Ya ga mutane ne zaune, suna ci suna sha, wasu kuma suna kida da busa da rawa. Jaki ya fada wa abokan tafiyarsa abin da ya gani. Ya tambaye su ko akwai dabarar da za su yi su kori mutanen nan su mallake gidan, su yi zamansu a nan suna koyon waka.
Kare ya ba da shawara cewa, zai hau bayan Jaki, kyanwa ta hau bayansa, Zakara ya hau bayan Kyanwa, su afka cikin dakin, mutanen za su ji tsoro su gudu su bar musu gidan.
Duk suka amince da wannan shawara ta kare. Kare ya hau bayan Jaki, kyanwa ta hau bayan Kare, Zakara ya hau bayan Kyanwa. Suka shiga gidan, suka zagaya ta kofar dakin, suka afka cikin dakin.
Jaki ya kwala kuka, kare ya yi haushi, kyanwa ta yi kuka, zakara ya kwala cara. Mutane suka firgita, suka yi waje da gudu, suka bar kayan kida da busa.
Jaki, kare, kyanwa da zakara suka zauna suka ci suka sha, suka yi hani'an. Sun samu gida, ga kuma kayan waka sun samu. Da suka gama cin abinci, suka kwanta domin su huta, zuwa da safe su farakoyon wakarsu.
Mutanen nan kuwa da aka kora daga cikin gida, suka yi ta mamakin abin da ya koro su daga cikin gidan nan. Can suna tsaye suna hangen gidan daga nesa, sai suka ga an kashe wutar gidan, ya koma cikin duhu. Sai wani mutum mai karfin hali da jarunta a cikinsu ya ce zai je ya dubo ko mene ne a cikin gidan nan.Ya tafi har ya shiga cikin gidan, ya shiga cikin daki. Ya laluba inda ashana ta ke ya dauka.
Ya kyasta domin ya kunna fitila, sai kuwa hasken ashanar nan ya dauko idanun kyanwa, ya gansu war warwar.
Sai ya tsorata ya yi waje da gudu, wajen fita ya taka wutsiyar kare, da kare ya ji zafi sai ya zafga masa cizo a kafa har jini ya fita. Ya kara rudewa ya fada wa jaki.
Jaki kuma ya takarkare iya karfinsa ya watsa masa harbi, ji kake tim! Mutumin dai ya yi karfin hali ya fita da gudu.
Kafin ya fita kuma zakara ya yi tsalle ya karta masa yaga a fuska..
Comments
Post a Comment