BB

1. Blackberry Enterprise: BB Enterprise yana daya
daga cikin manyan feature na blackberry, wanda
zaka sanya email dinka akan waya tayi
synchronizing din contacts dinka da messages
dinka na email, zaka samu saqon email akan
wayar ka ta blackberry Kaman yadda kake samun
saqon Text Message. Zaka iya saita wannan
Enterprise din ne idan ka danna setup a cikin all
apps ka zabi email account, ze baka daman
sanya email dinka da password, cikin mintoci
kadan zaka ga email dinka suna shigowa… Kuma
zatayi backup din Numbers dinka dake kan waya
zuwa email dinka, koda ka rasa wayar ka da layi,
welcome back bazata zama matsala ba kuma
zaka samu duka lambobin ka idan ka sake sanya
email dinka akan wata BB.


2. Blackberry Messenger: BBM as of last year itace
kadai ta rage dalili da wasu suke amfani da BB,
amma android na fara wa se suka ji dama basu
fito da wannan tsari ba… Duk da haka BBM ta BB
tafi ta android features, domin da ita zaka iya
Voice Chat ta wifi, wato kayi chatting da mutum
kaman kana waya dashi, sede wannan ko
qwandala ba’a taba maka kyauta ne… BBM dinta
tana da kyau sosai har ze iya nuna ma contacts
dinka waqoqin da kake ji ko video da kake kallo,
wanda wannan zaka iya cire feature din ta
Option a BBM app dinka. Applications suna
integrating a cikin ta kuma su nuna a updates
dinka, misali facebook app zata hada alaqa da
bbm dinka, zata nuna maka facebook friends
dinka da suke amfani da bbm kuma suke bbchat,
hakan ze baka daman adding dinsu ba tare da
wahala ba.


3. Minimizing Application: Kasantuwar ta tana
daukan java applications, zaka iya ajiye
application a bude kuma ka koma kan wani
application kayi aiki, idan kana son komawa kan
ta farkon se ka danna Menu button ka riqe, zata
jero maka su duka se zaba.


4. Clear Camera: BB tana daya daga cikin wayoyi
masu camera me kyau, zaka samu Bold 3 me 3.2
Mega Pixel ta dauki hoto da clear Kaman 5.0 MP
ne ya dauka, sannan basu cika nauyi barkate
wanda zesa MCard dinka yayi saurin cika.


5. Picture Geo-Tagging: BB Camera zata dauki
hoto kuma ta dauki sunan gari da aka dauki
hoton, Idan kana kano zatayi renaming hoton
zuwa Kano-20140201-001. A inda Kano itace
sunan garin da ake a lokacin da aka dauki hoton
2014 shekaran da aka dauki hoton, 02 watan
February da aka dauki hoton sannan 01 kwanan
watan da aka dauki hoton… 001 kuma yana nuna
hoto na farko kenan a ranan… Idan kabar Kano
kazoo Kaduna suna zata koma Kaduna muddin
kana da BIS akai kuma tana kunne.. Idan ka
bude Camera na BB, zaka ga wasu menus a qasa
guda biar, na tsakiyan itace ta daukan hoto,
dama dashi itace gurin seta Flash, can dama
kuma Scene Modes, idan ka dawo hagu daga
button din da ke daukan hoton itace ke daukan
lokacin se ka kunna, can hagu kuma tana nuna
preview din hotunan da ka duka ne.


6. Easy Customization: Blackberry unlike android,
bata da wuyar seti, Kaman wasu masu android
zaka samu saving number kanshi nayi masu
wuya, akwai wanda yaje saving number na cikin
tsakiyar dare kawai se ya qwala mun call, yace a
be gane kanta bane… A bb zaka iya canza
kamannin wayar ka da themes, bata dauka apps
masu yawa balle ka rasa abun yi da ita.


7. Fast Downloading: Wayar BB tana da saurin
downloading, tana daya daga cikin dalilin da nake
ganin Curve 2 ba waya bace domin bata da 3G,
sannan zaka iya saita downloadis biyu a lokaci
daya kowanne na tafiya akan 80-120kb per
seconds, depends da yanayin qarfin network din
gurinku ko kuma lokacin…


8. Easy File Sharing ONLINE: Idan kana da BB to
damuwar ka da café kadan ne, domin zaka iya
daukan hoto ka tura ta email, ko ka aika wa wani
ta whatsapp ko wani chatting da zaku iya
haduwa… Akwai mutane dayawa ‘yan kasuwa
masu zuwa kwatano su siyo motoci, da yawan su
zasuje su dauki hoton motoci su aika wa
customers dinsu, ba sai sunje café ba kuma bat a
email ba, kawai zasu aika da hoton ta whatsapp
kuma ya fito clear ba tare da wasting time ba.


9. Cheapest Subscription: Subcition dinta kuwa
tafi ta kowace waya sauqi, although android dasu
iPhone zasuyi komai da na ambata a sama sede
bata da sub na kanta wanda hakan kuma cikas
ne babba.'


10. BABBAN GARABASA: Tare da wayar BB, da
kudi qalilan zaka iya Unlimited downloads, idan
kana da BB zakaiya subcrition na naira dari kacal
amma zaka ci data da tafi 2gig… ni nayi kuma
kullun idan inaso zanyi… BBCDAY zuwa 21600 zai
daura ka akan tsarin MTN blackberry complete
daily plan, wannan plan din yafi na 1000 dinsu
na monthly, nasamu report akan cewa na
monthly na qarewa idan anyi downloads masu
yawa, se na bashi wannan sirrin, to yanzu ya
gwammace yayi ta near dari kuma ya mori
abunda dubu biyu bazata saya mashi ba… Idan
kai ma’aboci downloading ne, ko kana sana’a ta
computer ko flashing, kuma kana buqatan
downloading flash files, applications ko software,
kai koda kai ma’aboci kallon films ne zaka iya sub
din naira dari kuma kayi downloading films sama
da ashiri…
Ina yawaita sub dina da yamma, se na seta
downloads na sanya wayan a caji, zan bari tayi ta
downloading da ucborwser, har inyi bacci… iyaka
in tashi in tarar sun gama downloading gaba
daya, inada 32gig Mcard, amma akan 8gig nake
downloading, cikin kwana biyu zasu cika se in
tura 32 gig, idan sun cika se na mayar kan hard
drive me 500gig… kenan maimakon yasar da BB
dinka dan komawa android, ina laifi ka sayi koda
tour ce, kada ka cikata da applications kuma
kada ka damu da chatting da ita, amfanin ta
tazama na receiving call da kuma downloading,
idan buqatan downloading ya taso se kayi Sub
din dari na MTN ta hanyar Tura saqon BBCDAY
zuwa 21600…

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA