wata kisa

KISSA MAI TSORATARWA.

Labarin wata mata da
mijinta, tana tashinsa Sallar Asuba, wata rana sai ta
tasheshi sai ya makara, jam'i ya tsere masa, sai ya
samu wasu sukai jam'i na biyu, bayan sun idar, sai
limamin masallacin yazo yace kaine mijin wance?

Sai yace yaya akai kasan sunananta? Sai yace yau nayi mafarki duk wanda suka halarci jam'in farko
sunzama yan Aljanna, sai naga harda mace guda
daya, sai na tambaya sai akace matarkace, sai mijin
ya tafi da sauri gida don yai mata bushara sai ya tarar
tayi sujjada, Ranta ya koma ga mahaliccinsa....

Don haka idan ka kasance kana barci sanda kaso ka tashi sanda kaso, ba tareda kula da lokutan sallah
ba, to tabbas zaka dauwama cikin bakin ciki...wallahi
sallahce hutun duniya da lahira...Allah ya fada
aharshen Annabi Ibrahim" Allah ka sanyani mai
tsaida sallah nida zurriyata.... Suratu Ibrahim.

To jamaa manufar kissa irin wannan tasa kowa ya duba yaga yaya yake da sallolin farilla, Allah kabamu ikon
kiyayewa.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA