alkawari na 2
ALKAWARI 2
A daren ranar juma'ah bawani bacci nayiba sosai wanda zai ishi idanuwana saboda rigimar danarinka yi da bacci akan bazanyiba shikuma yazo yayiman kane-kane a idanuwa, nikuma gani nake idan nakwanta lokaci bazaiyi gudu ba sosai, nafiso inayi ina duba agogo, shiyasa duk bayan dakika daya ko biyu sai nadaga kaina naduba agogon dake makale ajikin bangon asibitin, haka nakasance bankwanta ba sai wurin karfe 02:30am na dare sakamakon karfina da bacci yaci, shima hakan yanada nasaba ne da ruwan da aka tafka jiya da daddare achikin garin namu na katsina wani sanyi yarinka shigowa tako ina har saida nasanya mayafi na lullube,
ina lullubewa shikuma bacci sai yasamu wurin zama a idanuwa na.......
Cikin ikon Allah batare da wani bata lokaci ba, gari na wayewa saiga likita yazo yaduba lafiyata tareda bada iznin zamu iya tafiya gida yanxu saboda ansamu abinda akeso, dadi da murna aguna abin ba'a magana, tamkar wanda akaba kyautar kujerar makka domin sauke farali. Bayan fitar likita sai kuma ga mahaifiyata tazo itada hadiza domin kawomana karin kumallo, ananne ahmad yashaida masu ansallamemu.
Shiryawa mukayi muka tattara komai namu domin tafiya gda, fitowa mukayi daga asibitin muka doshi tudun wada..... bayan munxo gda ne nashirya domin infita batareda kowa yasani ba, sbd idan umma tasan zanfita, bazata barni ba... Tsohon mashin dina najawo wanda idan ina tafiya kararshi tamkar ana bakacen tsakuwa acikinsa, ina sauri intafi saboda lokacin tashin jirgin yakusa saura 30 minute, bantsaya ko inaba sai filin jirgi, na'aje mashin dina inda aka tanada domin ajiyar ababen hawa....
Wani irin faduwar gaba naji saboda abinda idanuwa na suka hango... Wata mace ce, wadda nikeda tabbacin aunty bilki ce...... Aunty bilki mace ce mai matukar masifa kuma ta tsani talaka batason talaka ko kadan, kanwa ce ga alhaji jafar muhammad mahaifin yasmeen, wanda babban dan siyasa ne wanda yarike mukamai daban daban acikin mulkin nigeria, matarsa guda daya kuma yanada 'ya 'ya guda ukku, biyu maza sai daya mace, usman, aliyu sai yasmeen yar autarsu.... Aunty bilki ta taba yin aure wanda ta auri "ibrahim sabo", abokine ga alhaji jafar, amman saboda tsabar masifar aunty bilki, dole tasa suka rabu da mijin nata tadawo gidan yayanta da zama tareda da danta guda daya wanda take masifar so kuma take nuna masa gata, wanda suke kira da "Abba".........
Bayan natsaya ina tinanin tayadda zantunkari aunty bilki, nasan idan taganni bazata barni inshiga agun yasmeen ba, wani bangaren na zuciyata kuma yache "kaje kawai babu abinda zaifaru" cikin karfin hali naci gaba da tafiya, ina karasawa agunsu, sai naduka nagaida ta, wani irin kallo tayiman tareda yatsine fuska kamar taga wani mummunan abu, cikin bacin rai take magana "kai maye har anan saida kabiyota? Wai kai wane irin dabba ne? Yasmeen tayi kama da kalarka ne? banza matsiyaci talaka wanda rayuwarsa batada wani amfani", nidai bance komaiba, kawai na sunkuyar dakaina ina sauraren ikon Allah...
Abayan aunty bilki kuwa wasu bakaken mutane ne katti guda biyu masu jajayen idanuwa, tsaye suke kikam ko motsawa basuyi kamar gumaka, batareda tayimasu wata magana ba, kawai tadan juya kanta kadan, kamar tana kallon kafafuwan mutanenda dake bayanta, cikin kwarewa da sanin aiki irinnasu, har suka gane abinda take nufi, cikin zafin nama sukayo kaina suka sungume ni inata billayi, sukanufi wani dan jeji dani sukayiman bugun tsiya kamar zasu fiddamin rai, saida sukaga nadaina motsi sannan suka kyaleni, daman ba cikakkar lafiya gareni ba, anan nasuma sukuma suka kama hanya sukayi tafiyarsu.... Bayan wani dogon lokaci sai nafarka, ganin yanda yanayin garin yachanza nayi zaton yamma ce tayi, amman azahari dana duba agogo sai naga karfe 01:30pm ananne sai nagane hadari ne yamaida garin haka kamar za'ayi ruwa..... Dakyar nasamu nafiddo kaina bakin titi inazuwa nan naji kamar ana juya duniyar gaba daya komai yakoma upside down anan nakara faduwa, daganan bansan abinda yakara faruwaba saidai kawai nabude idona naganni acikin
.
Cikin tsoro nake tambayarta "a'ina ne kuka kawoni?" "ku suwaye" cikin sanyayyar murya naji tana fadar " kwantar da hankalinka bamuda niyar zaluntarka" wata ajiyar zuciya nayi wadda take nuna alamar hankalina ya sauka daga kololuwar tashinda yayi, sannan ta tashi tafice abinta batareda takara yin wata magana ba... Wani mutun ne yashigo dakinda nike dawasu karikitai a hannunsa irin wa'anda likitoci sukeyin gwaje gwaje , tareda ledar magunguna, turo kofarda yayi ne yabani damar ganin abinda ke wajen dakin, sai alokacin nagane ashe ba'acikin asibiti nake ba... Karasowa yayi agabana yaci gaba da sanyaman magani a wurarenda naji raunika ajikina, bayan yagama, sannan yabi jikina yanade da bandeji, lokacinda yagama aikinsa shine yayi dai dai da dawowar wannan matashiyar yarinyar wadda bansan ko wacece ba. Zama tayi akan wata kujera wadda take a gefen gadon danake kwance sannan tafara magana dacewa "bawan Allah inaso kafadamin ko kai waye kuma suwanene sukayimaka wannan aikin?
wani dogon lumfashi naja sannan nabata labarin abnda yafaru dani a filin jirgi tundaga farko har karshe.... Bayan nagama ne sannan nakara da tambayarta, ita wacece kuma a'ina kuka kawoni?... Sunana haleematu "Badole bane kasan ko ni wacece" tafada ayayinda take girgiza kanta, "amman inaso kayadda dani, kuma kasanya aranka na taimakeka ne kawai kuma banida wata manufa bayan hakan, kuma nan dakake gani gidan gona ne.
"nakawoka nanne, sbd bansan ko suwaye sukayimaka wannan abinba shiyasa naji tsoron shiga dakai cikin gari....... Yau kwana biyu kenan rabona da gida, hankalin kowa ya tashi bama yan gidanmu ba kadai, hatta mutanen unguwarmu suna chikin damuwa, anyi sanarwar gidajen radio da t.v amman babu wata magana mai dadi... Tafiya muke achikin mota bamutsaya ko inaba sai acikin garin daura......
Zaune suke acikin wani makeken fallow tsararre wanda yake daukeda abubuwan kayatarwa dayawa, Alhaji usman ne zaune shida matarsa hajiya binta, sun maida hankalinsu akan makekeyar t.v din dake makale ajikin bango. "alhaji kaidai bakada wani channel din kallo sai kttv" matarsa ce tafada ta fuskar tsokana, "hajiya kenan ai kallon kttv yanada amfani saboda kana gida zakasan halinda garinku yake chiki dama kasarku baki daya... Shigowarmu a falon ne yayi silar tsaidasu daga firar dasukeyi tareda maido kallonsu akan kofa domin ganin wa'anda ke sallama. Barka daxuwa diyata yar auta daga ke babu wata duk mai sonki shine nawa makiyinki ko kallo bai isheni ba" hajiya binta che takeyiwa diyarta wannan kirarin.
Alhaji yadubeni tareda bani umarnin inzauna, bayan nagama gaishesu ne sannan alhaji yake tambayarta wanene wannan ko abokin karatunki ne? Wani murmushi tayima mahaifin nata tareda fadar "a'a dady", sannan ta sunkuyar dakanta tagayamasu duk abnda yafaru, alhaji usman yanuna tausayi karara a fuskarsa..... Alhaji usman salisu zango mahaifin haleematu ne, kuma haifaffen garin daura ne dan asalin garin zango, babban dankasuwa ne wanda yayi suna acikin garin katsina, matarshi daya Itace hajiya binta da diyarsu guda daya haleematu......
Muna nan zaune sai mukaji ana sanarwa a cikin t.v... Kowa tsuru-tsuru yayi babu wanda yayi wata magana saidai kallonda Alhaji yakeyiman kamar mai niyar gano wani abu acikin fuskata. Nikau hankalina yayi matukar tashi domin jin yanda ake nemana kamar kudi, sai alokacin tunani na gaba daya yakoma akan gida, cikin kaguwa da rawar jiki namike tareda yimasu sallama daniyar tafiya gidanmu saboda nasan hankalin kowa a tashe yake yanzu sakamakon rashin ganina...
Cikin sauri nanufi hanyar fita waje, muryar Alhaji usman ce ta ratsa kunnena "yaza'ai katafi kai kadai batare da wani ba? Kaduba fa kaga yadda jikinka yake, yakamata ko wanka kayi kafin katafi ko, yakarasa maganarsa da yanayin tausayi karara a fuskarsa. A ranar nagane gidan "Alhaji usman salisu zango" gida ne na mutunci kuma sunsan darajar mutane. Bayan nagama komai nayi shirin tafiya, kamar wani dansu wanda suka haifa ne zaya tafi, haka sukazo mukayi bankwana, nayimasu godi

Comments
Post a Comment