Posts

Showing posts from January, 2015

YA KAMATA KUJI LABARINAN

Watarana Annabi (S.A.W) sundawo daga wajen yaki tareda sahabbansa, sai suka keta tacikin wata sahara suka yada zango a wajen. Kishirwa na damunsu har makogwaron sahabbai yafara tsagewa saboda tsananin zafi dakuma kishinruwa. Har saida suka fara yanka rakumi domin susha ruwan tunbinsa. Sai sayyadina Abubakar (R.A) yace: "Ya RASULLAHI karoka mana Allah yabamu ruwa musha mana. Nan take sai Annabi (S.A.W) yadaga hannayensa masu tarin Albarka yafara addu'a. Sayyadina Abubakar yace: "Nan take sai mukaga ruwan sama yana sauka kamarda bakin kwarya mukasha muka Qoshi damu da dabbobinmu". Sayyadina Abubakar yace: "koda muka duba sai mukaga a iya bakin inda muke anan ne kawai akayi ruwan". Ubangijinsa ya yarje masa komai!!! MUHAMMAD RASULLAHI kenan dan gatan Allah. Ya Allah ka lullubemu da rahamarka kuma ka sanyamu acikin cetonsa a ranar Al-Qiyama

YA KAMATA KUJI LABARIN WANNAN MATAR

YA KAMATA KUJI LABARIN WANNAN MATAR . . Akwai wata mata alokacin manzan Allah (s.a.w) tana sharar masallaci, Annabi yace idan wannan matar tarasu ko wani lokacine a gayamasa. Lokacin da matar tarasu da daddarene, shikuma ka'ida ta manzan Allah idan akayi sallar isha'i ya shiga gida ba'amar sallahma, saidai a saurara xuwa gari yawaye, sabo da yasa safiya xuwa dare duk ta jama'ace. Amma daga dare kuma xuwa asuba na matansane. Bayan nan sai sahabbai suke cewa yaza'ayi, sai suka yanke shawara suka sallaceta, aka kaita kabarinta, bayan gari yawaye sai Annabi baiga wannan mataba, sai yayi tambaya yace tana ina.? Sahabbai suka bashi amsa suka cemar tarasu, manzan Allah yace mesa ba'aje aka gayamanba, sai sahabbai sukace ai kace idan kashiga gida kadda ama sallama. Sai manzan Allah yace aje anunaman kabarinta na sallaceta, aka nunawa Annabi yamata sallah irin ta gawa, yana idarwa yace wallahi da kabari cike yake da duhu, amma gashi adalilin sallah ta kabarin yayi haske ...

BUHARI 4 CHANGE

PEOPLES GENERAL AT GLANCE: ★BIO-DATA: ◆ NAME: Muhammad Buhari; ◆ DOB: 17th December 1942; ◆ NATIONALITY: Nigerian; ◆ STATE OF ORIGIN: Katsina State; ◆ HOME TOWN: Daura; ◆ MARITAL STATUS: Married; ★EDUCATIONAL BACKGROUND: ◆ Elementary School, Daura ~ 1948-1952; ◆ Katsina Model School, Katsina ~1953; ◆ Katsina Provincial School (now Government College Katsina)~1956-1961; ★MILITARY CAREER/TRAINING: ◆ Military Training School, Kaduna ~1963; ◆ Officer’s Cadet School, Aldershot (UK)~Oct.'63; ◆ Platoon Commanders’ Course Nigerian Military College, Kaduna ~1964; ◆ Mechanical Transport Officer’s Course Army Mechanical Transport School, Borden (United Kingdom) ~1965; ◆ Defence Services’ Staff College, Wellington (India) ~1973; ◆ United States Army War College ~ 1979-1980; ☆MILITARY APPOINTMENT/EXPERIENCE: ◆ Platoon Commander, 2nd Infantry Bat. '63-64; ◆ Mech Trans. Officer, Lagos Garrison, '64-65; ◆ Transport Coy Commander, 2nd Brigade,'65-66; ◆ Batt Adjutant/Commander, 2nd Briga...

topa

Gwamnati Ce Ta Taimaka Wa Karuwar Rashin Aikin Yi — Ciroma An kalubalanci gwamnatin kasar akan irin salonta wajen samar da ayyuka ga jama’ar kasa. Ciroman Mafara, Alhaji Bala Usman ya bayyana cewar hanyoyin da gwamnati ke bi wajen bada aiki ya taimaka gaya wajen kara durkushewar ayyuka ga jama’a. ya kamata a kowani lokaci gwamnati za ta bullo da hanyoyi wajen saukakawa jama’a radadin talauci ta bullo da hanyar da za a iya samun kudin shiga ta yadda kudaden ma zasu taimaka wajen samar da wasu hanyoyin aikin ga jama’a. Ciroman yace a koda yaushe ake son bada aiki ba’a bada shi inda ya kamata domin kusan duk masu karamin karfi da ke samar da kudaden shiga ga gwamnati su ake taushewa, bai kamata a ce aikin da za a bayar akwai irin kamfanin da zata iya gudanar shi a jiha ba amma a tsallake a dauko wasu kamfanoni a waje a basu ba alhalin ba zasu iya bada kashi saba’in na ayyukan ga wadanda suka can-canta ba. Ya kamata gwamnatocin jahohi da na tarayya su canja tunaninsu lokaci ya wuce da zamu...

GANYEN NA'ANA'A

GANYEN NA'ANA'A Na'a-na'a wani ganye ne mai kamshi mai yado wanda ke son guri mai dausayi sai ta yi ta yaduwa kafin wani dan laokaci duk guri ya cika Na'a-na'a ganye ne mai matukar albarka yana da amfani sosai a wajen al'umma Larabawa da mutanen yankin Asiya sune mutanen da suka fi yin amfani da ganyen na'a-na'a a cikin abincinsu yawanci dukkan abincinsu zaka samu an saka na'a-na'a a ciki kodon ya karawa abincin kamshi ko don amfaninta a jiki hatta shayi in balarabe zai sha zaka tarar sau da dama sai ya hada da na'a-na'a a ciki A bisa binciken da aka yi an gano cewa ganyaen na'a-na'a na da amfani sosai ga jikin dan adam musamman ma ga masu ciwon hauka in suka juri shan na'a-na'a koda yaushe zasu sami lafiya haka kuma ana amfani da shi wajen yin shayi magani kwalliya turare da sauransu DAGA CIKIN AMAFANIN GANYEN NA'A-NA'A 1. Lizimtar amfani da ganyen na'a-na na maganin hauka 2. Shan ta nasa baki ya rinka kam...

Rakumi dan baiwa

RAKUMI DA AMFANINSA WAJEN KIWON LAFIYA “Ashe ba za su duba ga rakumi yadda aka halittasu” suratul gashiyat aya na 17 Manzon Allah s.a.w ya umarci wasu mutane daga kabilar Ukl ko Uraina su sha nonon rakumi da fitsarinta bisa wani lalura na rashin lafiya da suke fama da ita {sahih Bukari 2855 sahih Muslim 171} Rakumi dai wata halittace daga cikin dabbobin da Allah madaukakin sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da Allah yakeɓanci raƙumi da su kuma ya halicci raƙumi da su domin su zamo ayoyi abin lura ga ma'abota hankali Rakum kasaitacciyar dabbace da Allah ya halitta domin ya iya biyan buƙatar al'ummar da suke rayuwa a ɓangaren hamada ana samunsu a kasashe da dama wasu kasashen saboda darajarta gwamnatin kasar har ma'aikata take budewa don kula da su Rakumi kan iya rayuwa har na tsawon kwana takwas ba tare da ci ko sha ba sai yasa idan raƙumi ya samu inda zai sha ruwa kasancewar yana da matuƙar bukatarsa sa...

WAYAFI HAUKA CIKIN MAHAUKATAN GARURUWAN NAN???

WAYAFI HAUKA CIKIN MAHAUKATAN GARURUWAN NAN??? 1. Mahaukaci daga KATSINA TA DIKKO yana yawo tsirara amma akwai takalmi a kafansa. 2. Mahaukaci daga BAUCHIN YAKUBU shima tsirara yake yawo amma akwai gilas a idonsa 3. Mahaukaci daga SOKOTO BIRNIN SHEHU DAN GASKIYA AKAYI KU. shima tsirara yake yawo amma akwai hula akansa. 4. Hahahaha Mahaukaci daga ZARIA GARIN MASU WAWTA shima haka yake yawo tsirara amma akwai bell a 'kugunsa. 5. Mahaukaci daga KANO TA DABO TUMBIN GIWA KODA ME KAZO ANFIKA yana yawo ba riga amma akwai wando a ƙugunsa . Achikinsuwayafi hauka.

LABARIN WATA MATA DA KISHIYARTA

LABARIN WATA MATA DA KISHIYARTA Akwai wata mata itada kishiyarta, wacce take mugun Qinta. Wata Rana Mijinsu baya nan yayi tafiya, sai Uwar Gidan tayanke shawarar cewa: Idan dare yayi zataje ta kashe kishiyar ta domin ta huta da ganinta. Haka kuwa akayi dare yanayi sai taje ta dauko sabuwar wuka ta nufi Dakin Kishiyartata cikin Fushi. ☼☼☼ALLAHU AKBAR☼☼☼ Kunsan kometagani kuwa?? Tana zuwa sai taga wannan matar a kwance babu kai a jikinta, sai gangar jikin kawai tagani, Razana da tsoro yakamata ta takoma dakinta cikin Fargaba Har Gari ya waye bata rintsaba. Da safiya tayi sai taje wajen kishiyar, Abin mamaki koda taje saita tararda matar a kicin tana hada Break Fast, Tace da ita Wance dan Allah jiya Meya faru dake da dare Sai Matar tace nadade banji dadin Barci irin jiya ba, Sai kishiyar tayi mamaki matuka tace to wacce Addu'a kika karanta da zaki kwanta bacci?? Sai ita wannan matar tace: Na karanta wadannan Surorin kafin na kwanta bacci kamar haka: ☼1. QULHUWALLAHU AHAD kafa Uku. ☼2....

Rayuwar yarinta akwai dadin tunawa.

Rayuwar yarinta akwai dadin tunawa. Ka tuna sanda idan gidan tv zasu bude sai su saka wani labule mai fari da baki? Ka tuna sanda muke kallon india ranar lahadi a ctv? Ka tuna sanda muke dawowa daga makarnatar boko muna jin yunwa kuma ana filin cigiya da sanarwa? Wai kuwa yaran yanzu suna wasan daren ranar alhamis da juma'a sanda ba makarantar dare? Ka tuna exercise book din mu da muke wa wakar "na daya fafalolo...." ? ka tuna sanda muke siyan biro eleganza? Allah sarki, duk sanda naga za'ayi labaran tara (network news) sai naita jin haushi Na tuna sanda ake shirin nan na ctv "hana wani hana kai" Idan na tuna sanda muke fita tashe da azumi nakanji dadi Ni dai ban taba la6ewa a bandaki ba lokacin da nake azuminð Allah sarki motar gwangwani ta da kuma ta kara, ko waye ya dauke min ita? ka tuna tallan nan da ake ayi na buhun bacco "ka fasa min buhu da tsinin kanka........"

TIJJANIYYA AWARENESS KUNGIYAR BOGI CE.

TIJJANIYYA AWARENESS KUNGIYAR BOGI CE. (Inji sheikh Dahiru Bauchi) BABU WANI DAN TIJJANIYYA NA GASKIYA DA ZAI TALLATA JONATHAN. (Inji sheikh Dahiru Bauchi) Abin da ke tsorata mu game da zabe mai zuwa Sheikh dahiru Bauchi Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya zanta da Aminiya inda ya yi bayani game da zabe mai zuwa da kuma matsalolin tsaro a Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Aminiya: Me za ka ce game da yadda wata kungiya ta fito a jarida tana nuna cewa tana tare da shugaba Jonathan da sunan Tijjaniya Awareness? Sheikh dahiru: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Hakika kwanakin baya akwai wata kungiya mai suna Tijjaniya Awareness iniatibe forum ta hada hotona da na shugaban kasa da sunan cewa wai tana wa shugaba Goodluck Jonathan kamfen. Babu wani dan Tijjaniya na gaskiya da zai tallata shugaba Jonathan a Najeriya, saboda haka muna nisanta kanmu da wannan kungiya ta bogi. Kuma babu mamaki wadansu ‘yan siyasa ne suke amfani da wann...

►FALALAR JUMA‘A►

►FALALAR JUMA‘A► Juma‘a ita ce mafi girma a cikin ranaku da ALLAH Madaukakin Sarki ya halitta, ta yadda ya bawa yahudawa zabi sai suka zabi asabar, sa‘annan Ya bawa nasara zabi sai suka zabi lahadi, mu kuma al‘ummar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam sai ALLAH ya azurta mu da wannan rana ta juma‘a. A cikin ta ne ALLAH Madaukakin Sarki ya halicci babanmu Annabi ADAM (AS) kuma a cikin wannan rana aka sauko da shi daga AL- JANNAH, kuma a cikin irin wannan rana ALLAH Madaukakin Sarki zai tashi alqiyama. Hadisi ya tabbata a cikin muslim cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce idan ranar juma‘a ta zo duk halittun ALLAH Madaukakin Sarki hankalinsu a tashe yake (sabo da tsoran kada ALLAH ya tashi qiyama a wannan ranar). Sai mutum da al-janni kawai hankalin su yake a kwance. Haka kuma yana daga falalar ta juma‘a Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce akwai wata sa‘a wanda duk ya riske ta yana mai addu‘a to ALLAH zai karbi addu‘arsa. Muslim ne ya rawaito. Ana son kamew...

jonathan

Idan bawai mutanen kasa na so sumai da mu zamanin jahiliyya bane, Me zamuyi da Buhari - Jonathan A cikin Jawabin da shugaban kasa yayi Jiya a jihar Legas wajen kaddamar da kamfen dinsa na yakin neman zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, Jonathan ya lissafa ire iren abubuwan da ya gudanar da kuma bayyana irin rashin cancantar Buhari da ya zama shugaban kasan Najeriya a 2015. Kadan daga cikin abubuwan da ya fada a cikin jawabinnasa sune: Tsaro: Shugaban kasa yace kamar yadda jam’iyyar adawa ta APC take cewa gwamnatinsa basuyi kokari akan kyautata tsaro a kasa Najeriya ba ya musanta cewa gwamnatinsa ne kuwa sukafi kowa kyautata tsaro a cikin sahun gwamnatocin da suka wuce a baya. Ya kalubalanci Buhari da ya gaya ma yan Najeriya abin da gwamnatinsa sukayi a 1983/84 da kasa fin kudi na fannin tsaro tunda ko bindiga daya gwamnatinsa basu suya ba ma sojojin Najeriya a wancan lokacin. Cin hanci, Rashawa da satan kudin gwamnati: Shugaban Kasa Jonathan yace shi bazai kama mutumba ya kulleshi kama...

'YAN AREWA AL-MAJIRAI NE DA BASU DA GODIYA INJI DOKUBO ASARI

'YAN AREWA AL-MAJIRAI NE DA BASU DA GODIYA INJI DOKUBO ASARI Duk da cewa hukumar SSS ta gargadi 'yan adawa da su kame bakinsu daga kalaman tashin hankali kafin zaben 2015 to amma 'yan uwan shugaban kasa irinsu Dokubo Asari har yanzu suna Cin karen su babu babbaka. Dokubo jiya yayi wa kalaman Gwamna Sule Lamido Martani kan zargin Jonathan da Buhari na neman yamutsa kasar nan saboda bukatarsu ta kashin kai a 2015. Dokubo yace Sule zancen banza yake, don yasan ko shi ko wani daga Arewa in ya tsaya zabe ba zai iya kayar da Jonathan ba shi yasa yake wannan soki burutsu. Dokubo yace 'Yan Arewa almajirai ne da yakamata su yiwa masu ciyar dasu daga Kudu godiya amma basa hakan. kuma in dai Arewa bata canza daga tunaninsu na sune kadai suka iya mulkin kasa ba, to ba za a taba zama lafiya a Nijeriya ba. Asari ya nemi da 'yan Arewa da ya kira almajirai da su rika godiya domin a addinin musulunci ma an nemi wanda ake taimakamasa ya rika godiya ga mai temakonsa daga Kudu.