'YAN AREWA AL-MAJIRAI NE DA BASU DA GODIYA INJI DOKUBO ASARI

'YAN AREWA AL-MAJIRAI NE DA BASU DA GODIYA INJI DOKUBO ASARI

Duk da cewa hukumar SSS ta gargadi 'yan adawa da su kame bakinsu daga kalaman tashin hankali kafin zaben 2015 to amma 'yan uwan shugaban kasa irinsu Dokubo Asari har yanzu suna Cin karen su babu babbaka.

Dokubo jiya yayi wa kalaman Gwamna Sule Lamido Martani kan zargin Jonathan da Buhari na neman yamutsa kasar nan saboda bukatarsu ta kashin kai a 2015.

Dokubo yace Sule zancen banza yake, don yasan ko shi ko wani daga Arewa in ya tsaya zabe ba zai iya kayar da Jonathan ba shi yasa yake wannan soki burutsu.

Dokubo yace 'Yan Arewa almajirai ne da yakamata su yiwa masu ciyar dasu daga Kudu godiya amma basa hakan. kuma in dai Arewa bata canza daga tunaninsu na sune kadai suka iya mulkin kasa ba, to ba za a taba zama lafiya a Nijeriya ba.

Asari ya nemi da 'yan Arewa da ya kira almajirai da su rika godiya domin a addinin musulunci ma an nemi wanda ake taimakamasa ya rika godiya ga mai temakonsa daga Kudu.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA