TIJJANIYYA AWARENESS KUNGIYAR BOGI CE.

TIJJANIYYA AWARENESS KUNGIYAR BOGI CE.

(Inji sheikh Dahiru Bauchi)

BABU WANI DAN TIJJANIYYA NA GASKIYA DA ZAI TALLATA JONATHAN.

(Inji sheikh Dahiru Bauchi)

Abin da ke tsorata mu
game da zabe mai zuwa

Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin
musuluncin nan Sheikh dahiru
Usman Bauchi ya zanta da Aminiya
inda ya yi bayani game da zabe mai
zuwa da kuma matsalolin tsaro a
Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta
kasance:
Aminiya: Me za ka ce game da yadda
wata kungiya ta fito a jarida tana
nuna cewa tana tare da shugaba
Jonathan da sunan Tijjaniya
Awareness?
Sheikh dahiru: Dukkan godiya ta
tabbata ga Allah Madaukacin Sarki.
Hakika kwanakin baya akwai wata
kungiya mai suna Tijjaniya
Awareness iniatibe forum ta hada
hotona da na shugaban kasa da
sunan cewa wai tana wa shugaba
Goodluck Jonathan kamfen. Babu
wani dan Tijjaniya na gaskiya da zai
tallata shugaba Jonathan a Najeriya,
saboda haka muna nisanta kanmu da
wannan kungiya ta bogi. Kuma babu
mamaki wadansu ‘yan siyasa ne suke
amfani da wannan kungiyar domin
kawo rudani a tsakanin al’umma.
Kuma su suka dauki nauyinsu domin
shiga kafafen watsa labarai da
wannan farfaganda. Saboda haka
idan su ‘yan Tijjaniya na gaskiya ne
su fito fili mu gansu.
‘Yan darikar Tijjaniya ba su da wani
aiki sai zikiri da hailala da salatin
Annabi, wadannan su ne manufofin
‘yan Tijjaniya, ba shiga harkokin
siyasa ba. Nasha fada a baya, ni ba
dan kwangilar yayata shugaba
Jonathan ba ne.
Aminiya: Mene ne sakonka ga
al’umma game da babban zabe da ke
tafe?
Sheikh dahiru: Ina kira da babban
murya ga al’ummar Najeriya da kowa
da kowa ya fito ya kada kuri’arsa a
ranar zabe, domin ta haka ne za a
fitar da Najeriya daga halin da take
ciki. Ni ba dan siyasa ba ne, amma
abin da ya kamata al’umma su yi shi
ne su zabi gaskiya a ranar zabe.
Babban tsorona shi ne idan aka zabi
Jonathan a zaben 2015 ba za a zauna
lafiya a Arewa ba. Idan kuma aka zabi
Janar Muhammadu Buhari mutanen
kudancin Najeriya ba za su bari a
zauna lafiya ba. Fatanmu a nan shi ne
a yi zabe cikin kwanciyar hankali da
lumana.
Aminiya: Da gaske ne ka ce shugaba
Jonathan da amurkawa ne suke
kashe mutane a Najeriya?
Sheikh dahiru: Wannan magana ba
gaskiya ba ne kuma ban fadi haka ba,
abin da na fada shi ne, hakkin
gwamnati ne ta kare rayuka da
dukiyoyin al’umma, duk gwamnati
da ta gagara samar da tsaro to tabbas
ba ta da amfani a wajen al’umma.
Don haka muna ganin watakila
gwamnati tana da hannu dumu-
dumu a wannan rikici wanda ya yi
sanadiyar lakume dimbin rayukan
al’umma a wannan shiyya na Arewa
maso gabas.
Akwai wani tsohon soja da muka
tattauna da shi, ya bayyana mini
cewa idan aka ba shi dama zai iya
kawar da ‘yan Boko Haram a dajin
Sambisa da ke jihar Borno. Na fada,
zan kuma sake fada, gwamnatin
Najeriya tana wasa da rayukan
al’umna. Allah zai kawo mana
karshen wannan matsala wanda ya
zamo kadangaren bakin tulu ga
gwamnatin Najeriya.
Mun bada wadansu addu’o’i da yanzu
haka ana cigaba da yi, kuma nan da
makonni uku masu zuwa muna fata
abubuwa za su canza a Najeriya. Masu
mana kulle-kulle Allah zai tona musu
asiri.
Kuma za mu cigaba da fadan gaskiya
babu wanda ya isa ya rufe mana baki,
yanzu gwamnati ta cire rubutun
ajami a jikin sabuwar Naira 100, idan
Allah Ya kawo wata sabuwar
gwamnati za mu tilasta mata sai ta
mayar da rubutun da aka cire.
Aminiya: Wane tsokaci za ka yi game
da yadda aka gudanar da bukukuwan
maulidi na bana?
Sheikh dahiru: An gudanar da bikin
maulidi na bana cikin kwanciyar
hankali, saboda haka muna godiya ga
Allah. Akwai dimbin mutanen da suka
halarci wajen maulidin wanda aka
saba gudanarwa a dandalin Ibrahim
Badamasi Babangida a cikin garin
Bauchi. Daga cikin kasashen da suka
halarci wajen maulidin akwai
mutanen Ghana da Kamaru da Nijar
da Senigal da Maroko da Chadi da
Gini, da sauran wadanda suka fito
daga sassa daban-daban na nahiyar
Afirka. Gwamnonin jihohin Zamfara
da Jigawa sun taimaka mana, kuma
gwamnan jihar Bauchi Malam Isa
Yuguda ya halarci wajen taron,
sannan ya ba mu gudunmawa.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH