jonathan
Idan bawai mutanen kasa na so sumai da mu zamanin jahiliyya bane, Me zamuyi da Buhari - Jonathan
A cikin Jawabin da shugaban kasa yayi Jiya a jihar Legas wajen kaddamar da kamfen dinsa na yakin neman zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, Jonathan ya lissafa ire iren abubuwan da ya gudanar da kuma bayyana irin rashin cancantar Buhari da ya zama shugaban kasan Najeriya a 2015.
Kadan daga cikin abubuwan da ya fada a cikin jawabinnasa sune:
Tsaro:
Shugaban kasa yace kamar yadda jam’iyyar adawa ta APC take cewa gwamnatinsa basuyi kokari akan kyautata tsaro a kasa Najeriya ba ya musanta cewa gwamnatinsa ne kuwa sukafi kowa kyautata tsaro a cikin sahun gwamnatocin da suka wuce a baya.
Ya kalubalanci Buhari da ya gaya ma yan Najeriya abin da gwamnatinsa sukayi a 1983/84 da kasa fin kudi na fannin tsaro tunda ko bindiga daya gwamnatinsa basu suya ba ma sojojin Najeriya a wancan lokacin.
Cin hanci, Rashawa da satan kudin gwamnati:
Shugaban Kasa Jonathan yace shi bazai kama mutumba ya kulleshi kamar yadda Buhari yake ikirari idan ya kafa gwamnati zaiyi.
Yace haka kawai bazai kama uban wani ko kawun wani ya daure ba domin ya saci kudin gwamnati.
Yace gwamnatinsa na amfani da hikima ne wajen ganin ta kau da cin hanci, rashawa da satan kudin gwamnati.
Jonathan ya kara da cewa bayan kirkiro da sababbin Jami’o’i guda 12 da yayi, ya wadata manoma da takin zamani, ya bunkasa tattalin arzikin kasa inda Najeriya ne yanzu tafi kowace kasa a nahiyar Afrika girman tattalin Arziki kasa.
A cikin Jawabin shugaban kasan yakara da cewa tun lokacin da ya hau karagar mulkin kasannan wahalar mai yakare a kasa Najeriya.
Yace ba kamar da ba inda ake wahalar mai yanzu sai dai kashiga gidan mai kasha ka wuce.

Comments
Post a Comment