topa
Gwamnati Ce Ta Taimaka Wa Karuwar Rashin Aikin Yi — Ciroma
An kalubalanci gwamnatin kasar akan irin salonta wajen samar da ayyuka ga jama’ar kasa. Ciroman Mafara, Alhaji Bala Usman ya bayyana cewar hanyoyin da gwamnati ke bi wajen bada aiki ya taimaka gaya wajen kara durkushewar ayyuka ga jama’a. ya kamata a kowani lokaci gwamnati za ta bullo da hanyoyi wajen saukakawa jama’a radadin talauci ta bullo da hanyar da za a iya samun kudin shiga ta yadda kudaden ma zasu taimaka wajen samar da wasu hanyoyin aikin ga jama’a.
Ciroman yace a koda yaushe ake son bada aiki ba’a bada shi inda ya kamata domin kusan duk masu karamin karfi da ke samar da kudaden shiga ga gwamnati su ake taushewa, bai kamata a ce aikin da za a bayar akwai irin kamfanin da zata iya gudanar shi a jiha ba amma a tsallake a dauko wasu kamfanoni a waje a basu ba alhalin ba zasu iya bada kashi saba’in na ayyukan ga wadanda suka can-canta ba.
Ya kamata gwamnatocin jahohi da na tarayya su canja tunaninsu lokaci ya wuce da zamu zauna muna bautar wasu alhalin muma muna bukata, yanzu ayyukan da mutanen kasar talatin ko fiye da haka zasu iya yi sai a dauke shi amikawa wani kmafani a waje, wanda hakan na iya zama barna ko mayar da kasa baya. Yanzu idan za’a gudanar da kwalbatoci ko hanyoyi akwai kamfanonin ‘yan kasa da zasu iya yinsu amma saboda wani boyayyen manufa sai a karkatar da ayyukan ga wasu manyan kamfanonin basu iya sharewa kowa hawaye.

Comments
Post a Comment