►FALALAR JUMA‘A►

►FALALAR JUMA‘A►

Juma‘a ita ce mafi girma a cikin
ranaku da ALLAH Madaukakin
Sarki ya halitta, ta yadda ya
bawa yahudawa zabi sai suka zabi asabar, sa‘annan Ya bawa
nasara zabi sai suka zabi lahadi,
mu kuma al‘ummar Annabi
Muhammadu Sallallahu Alaihi
Wasallam sai ALLAH ya azurta
mu da wannan rana ta juma‘a.

A cikin ta ne ALLAH Madaukakin
Sarki ya halicci babanmu Annabi
ADAM (AS) kuma a cikin wannan
rana aka sauko da shi daga AL-
JANNAH, kuma a cikin irin
wannan rana ALLAH Madaukakin Sarki zai tashi alqiyama.

Hadisi ya tabbata a cikin muslim
cewa Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ce idan ranar
juma‘a ta zo duk halittun ALLAH
Madaukakin Sarki hankalinsu a
tashe yake (sabo da tsoran kada ALLAH ya tashi qiyama a wannan
ranar). Sai mutum da al-janni
kawai hankalin su yake a
kwance.

Haka kuma yana daga falalar ta
juma‘a Manzon ALLAH Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ce akwai wata
sa‘a wanda duk ya riske ta yana
mai addu‘a to ALLAH zai karbi
addu‘arsa. Muslim ne ya rawaito.

Ana son kamewa da yawaita
zikiri da salatin Annabi da iyalan
gidansa (a.s). Ana son
yawaita karatun al-qur'ani da
addu'o'i ko sauraransu ta hanyar
radio.

Yana daga cikin sunnar Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam yana
karanta suratul KAHFI kowacce
juma‘a. Da dai sauran falalar ta
masu dinbin yawa.

Ya dan uwa ka kasance mai koyi
ga abubuwan shugabanmu
Annabi Muhammadu Sallallahu
Alaihi Wasallam.

Ya ku musulmi! mu yi gasa a kan
wannan alheri mai girma, wanda
Allah ya sanya shi cikin ranar
Juma’a ga wanda ya sunnanta da
sunnan Annabi a cikin wannan,
mu tsaftacce jukkunanmu, mu sanya mafi kyawun tufafin mu, (Musamman farin Tufafi)
mu yi asuwaki, mu sanya turare,
mu yi sammako don mu tafi
sallar Juma’a, mu lazimci
ladubban Annabi (S.A.W), da tsari
na Muhammadiyya.

Mu kasance daga cikin masu rigaye zuwa alherai,
masu rabauta da mafiya
daukakar darajoji, Wannan
falala ce ta Allah da yake ba da
ita ga wanda ya so.

Ya Allah yasa mu dace

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA