Rayuwar yarinta akwai dadin tunawa.

Rayuwar yarinta akwai dadin tunawa.

Ka tuna sanda idan gidan tv zasu bude sai su saka wani labule mai fari da baki?

Ka tuna sanda muke kallon india ranar lahadi a ctv?

Ka tuna sanda muke dawowa daga makarnatar boko muna jin yunwa kuma ana filin cigiya da sanarwa?

Wai kuwa yaran yanzu suna wasan daren ranar alhamis da juma'a sanda ba makarantar dare?

Ka tuna exercise book din mu da muke wa wakar "na daya fafalolo...." ?

ka tuna sanda muke siyan biro eleganza?

Allah sarki, duk sanda naga za'ayi labaran tara (network news) sai naita jin haushi

Na tuna sanda ake shirin nan na ctv "hana wani hana kai"

Idan na tuna sanda muke fita tashe da azumi nakanji dadi

Ni dai ban taba la6ewa a bandaki ba lokacin da nake azuminð

Allah sarki motar gwangwani ta da kuma ta kara, ko waye ya dauke min ita?

ka tuna tallan nan da ake ayi na buhun bacco "ka fasa min buhu da tsinin kanka........"

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA