Posts

Showing posts from June, 2015

RUNDUNA TA BAKWAI

>>> RUNDUNA TA BAKWAI >> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA Wata rana zaidu dan harisatu ya dawo daga saye da sayarwar sa daga garin sham sai ya hadu da wasu kafirai yan kabilar bani fazazata, mazauna wani kauye da ke cewa wadilkura, sai suka tare zaidu dan harisatu suka kwace duk wani abu da ya sayo a karshe ma dai sun so su kasha shi allah ne ya kareshi daga sharinsu. Don haka sai yazo ya sanar da manzon allah {saw} abin da suka yi masa . Sai manzon allah {saw} ya tura zaidu tare da wasu sadaukai suka nufu wannan kauye na wadannan yan fashi n kafirai domin su dauko fansar abin da sukayiwa zaidu. Ita dai wannan rundun koda taje garin sai suka zagaye shi suka karkashe mafiya yawan muta nan garin harma aka ribato matar sarkin garin suka taho da ita bayan sun tagaiyara garin baki daya. Wannan shine abin da yafaru da runduna ta BAKWAI a takaice in allah yaso zamu kawo muku runduna ta TAKWAS. Ku kasance damu ta wannan shafi mai albarka don samun abubuwa daban daban. Wato @[17422305611...

RUNDUNA TA BIYAR

Image
>>> RUNDUNA TA SHIDA >> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA A cikin watan rabi’ul auwal ne labara ya zowa shugaban halitta cewa wasu daga cikin kafirai sunyo sansani domin su kwace dabobbin wasu musulamai a wani gari da ake cewa haifa’u, wani kauye ne a kusa da madina, su kuma kafiran suna wani kauye da yake da suna kassatu mil ashirin da hudu ne daga madina. To koda wannan labara ya zowa shugaba sai ya samu mutum goma daga cikin sahabbai a bias jagorancin muhammadu dan muslimata ya tura su domin bada kariya gay an uwanmu musulmai da kuma fito na fito da azzluman kafiran wannan yanki. To andade ana fafatwa tsakanin wadannan sahabbai na manzon allah {saw} da kuma wadannan miyagun kafirai a inda su kafiran suka samu nasarar kasha duk kan sahabban nan guda goma amma banda shi muhammadu wato kwamandan yakin amma shima a zaton su sun kashashi saboda raunukan da yasamu. To bayan sun tafi sai ya farfado ya dawo gida ya bawa manzon allah labari n yanda al’amarin ya kasance, to sai manzo a...

RUNDUNA TA BIYAR

Image
>>> RUNDUNA TA BIYAR >> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA Kabilar banu asadi, sune suke da wata mummunar al’ada ta cutar da duk wani musulmi da yabi ta kusa da garin su don haka sai labara ya zowa shugaban halitta {saw}. Sai manzon allah {saw} ya shirya runduna ta mahaya arba’in ya bawa ukashatu kwamandan yaki domin su je su tarwatsa shakiyancin wadannan shaidanu. A lokacin da ukashatu ya nufi gari wayan nan makiya allah yasa sai da suka kusa karsawa gari sai labara yazo musu don haka sai kowanen su ya cika rigarasa da iska suka gudu suka bar garin. Amma duk da haka ukashatu suka shiga garin suka samu wani mutum shi kadai yana ta barci sai suka ce ya nuna musu dabobin wayannan kafirai da suka gudu suka bar garin. Ba tare da bata lokaci ba, wannan mutum ya tashi ya fara nunawa musulmai dukiyoyin wadannan kafirai musulmai suka tattaro dabbobi da dukiyoyin su suka juyo dasu a mazaunin ganima kuma haar musulamai suka dawo garin madina babu abin da ya shafesu dan gane da cutar wasu k...

RUNDUNA TA HUDU

>>> RUNDUNA TA HUDU >> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA It dai wannan runduna mai dunbin albarka ta kasance ne a shekara ta shida da hijirar manzon allah {saw}. It dai wannan runduna ta tafi a karkashin jagorancin muhammadu dan aslamat, barade talatin ne suk fita wannan yaki ko wanensu yana kana bin hawansa suka je gari yan kabilar bakaru dan kilabi a wani gari da ake cewa bariyya. Haka dai wadannan sahabbai suka shiga wannan gari suka far musu da yaki a inda suka kasha mutum goma daga cikin wadannan kafirai ragowar kuwa suka cika rigarsu da iska. Su kuma sahabbai suka samu nasarar koro dabbobin su. Suna cikin hanyar su ta dawo wa ne suka hadu da wani kafiri mai suna sumamatu dan usalu yana daga cikin manyan yan kabilar bani hanifa, anan ma sahabbai suka cafke shi suka tafi da shi a mazaunin fursunan yaki ba tare da sun san koshi waye bah. Koda suka je dashi wurin manzon allah {saw} koda manzon allah yagan shi nan take ya gano waye shi manzon allah {saw] ya bijirowa da wannan sa...

RUNDUNA TA UKU

>>> RUNDUNA TA UKU >>>> RUNDUNAR ZAIDU DAN HARISATU KA KARANTA A NUTSE. Bayan manzon allah yayi hijira daga makka zuwa madina, Bayan wannan hijira ne kafirai suka ci gaba da azabtarwa da cutar da musulman da suke agarin makkah harma daga karshe harma daga karshe kafirai suka yiwa musulamai korar da ake yiwa kare suka fitar da musulmai daga cikin garin makkah bayan sun kwace dokiyoyin su. To akan haka ne sukuma musulmai suka yi niyar mayar da murtani akan wannan zalunci da aka yiwa yan uwan mu musulmai, ana cikin wannan yanayi ne kuwa sai labara ya zowa manzon {saw} cewa ga wasu ayarin kafirai can sun dawo daga fatauci daga kasar sham zuwa makkah kuma suna dauke da kyawawan kalolin abinci tare da tsadadun riguna na alfahari, a lokacin babu abin da manzon allah {saw} ya fara yi sai ya sai ya zabi wani gwarzo daga cikn jaruman barade daga cikin sahabbai wannan gwarzo, manzon allah {saw} yana yawn shugabantar da shi a cikin mafiya yawan yake-yake. Ita dai wannan rundun...

RUNDUNA TA BIYU

>>RUNDUNA TA BIYU >>> GANIMA TA FARKO A ADDININ MUSILUNCI KA KARANTA A NUTSE. Ganima ta farko a addini ita ce wacce aka sameta a cikin wata runduna ta manzon allah {saw} da ya tura ta abisa jagorancin abdullahi dan ja’ashin, tare da jarumai tamanin (80) a cikin sahabbai. Sai dai kwamadan wannan rundun wato abdullahi dan ja’ashim wata rana bayan manzon allah {saw} ya idar da sallah isha’I sai yakira abdullahi dan ja’ashim, y ace dashi, ya kai abdullahi gobe tun da asuba ina son ganinka kuma kazo cikin shirinka na yaki. Tun da asuba abdullahi dan ja’ashim ya fito da makamansa na yaki, tare da tokobinsa da kayan harbi tun na wacen lokacin. Bayan manzon allah {saw} ya idar da sallar asuba ya fito daga masallaci sai kawai manzon allah {saw} ya ga abdullahi a tsaye sai manzon allah {saw} ya nemi maga takardar sa aka rubuta wata wasika sai manzon allah {saw} ya je gurin abdullahi dan ja’ashim yace dashi. “Nashugabantar dakai acikin wadancan sadaukan, sannan sai manzon allah {sa...

runduna ta farko

>>RUNDUNA TA FARKO ≥> Mai sauraro wannan itace ruduna ta farko wacce manzon allah {S A W } ya shiryata kuma ya aikata domin suje su tarbi wata gayar ayarin KAFIRAIN kurashawa da suka dawo daga garin sham daga cikin daga cikin wayanan kafirai akwai abu jahal tsinannen ubangoji, su wadanan musulmai da mazon allah {SAW} ya tura zuwa wannan fafatawa musulmai su talatin ne (30) amma su kuwa arna su dari uku ne(300). Shugaban wannan runduna ta musulmai shi ne sayyidina hamza dan abdulmutalabi. Ita dai wannan tuta da manzon allah (saw) ya bayar itace tuta ta farko da manzon allah (saw) ya tura runduna don daukaka addinin allah wannan kuwa yafaru ne acikin watan azumi shekara ta daya bayan hijira. Ita dai wannan tuta fara manzon allah ya mikata ga sojojin musulinci a inda wani sahabi mai suna marsadu dan kanzi dan husaini ya karbi wannan tuta suk nausa suka tafi tare da umarnin manzon (saw). A lokacin da wadannan bangarori biyu suka h adu suka daidaita domin fara yakar junan su kowane...

anga WATA

√√ALHADULILLAH ANGA WATA√√ Yanzu haka munata jin karar wani Abu Kamar BINDIGA a baban birnin JIGAWA wato DUTSE. wada yake Nuna cewa anga wata a wasu wuraren kuma SARKIN ya bad a Umar nin kowa ya dau AZUMI. Allah yasa mugama lafiya ameeen

Ramadan khareem

WANNE IRIN SHIRI KA YI WA RAMADHANA ? SAHABBAI (RIDWANILLAHI ALAIHIM) Sun kasance suna addu'a da zarar an kammala azumin ramadhana suna cewa: Ya Allah ka kar'bi ibadunmu da muka gabatar a Ramadhana. Suna yin wannan addu'a tsawon wata shida. Sannan kuma su cigaba da yin addu'ar: Ya Allah ka kai mu ramadhana muna masu imani da lafiya. Wannan addu'a kuwa yin ta suke yi har sai sun riski ramadhana. Sahabbai shirye-shirye suke yi na tunkarar ramadhana tun watanni shida gabanin ramadhana. * Dan uwa wanne irin shiri kake yi game da wannan wata mai cike da dukkan alkhairai wato ramadhana? * Wanne tsari ko shiri kake yi game da yawan tilawar Al-Qur'ani da zaka gabatar a ramadhana? * Wanne shiri kake yi na nafilfilin Salla d'ori akan wanda kake yi kafin ramadhana? * Wanne irin tanadi kake yi na abinda zaka ciyar ga masu azumi a Ramadhan? Wadannan sune abubuwan da ya kamata mu sanya su a gabanmu a wannan lokaci da watan ramadhana ke fuskanto mu gadan- gadan. Watan rama...