RUNDUNA TA HUDU

<<<>>>> RUNDUNA TA HUDU <<<>>> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA It dai wannan runduna mai dunbin albarka ta kasance ne a shekara ta shida da hijirar manzon allah {saw}. It dai wannan runduna ta tafi a karkashin jagorancin muhammadu dan aslamat, barade talatin ne suk fita wannan yaki ko wanensu yana kana bin hawansa suka je gari yan kabilar bakaru dan kilabi a wani gari da ake cewa bariyya. Haka dai wadannan sahabbai suka shiga wannan gari suka far musu da yaki a inda suka kasha mutum goma daga cikin wadannan kafirai ragowar kuwa suka cika rigarsu da iska. Su kuma sahabbai suka samu nasarar koro dabbobin su. Suna cikin hanyar su ta dawo wa ne suka hadu da wani kafiri mai suna sumamatu dan usalu yana daga cikin manyan yan kabilar bani hanifa, anan ma sahabbai suka cafke shi suka tafi da shi a mazaunin fursunan yaki ba tare da sun san koshi waye bah. Koda suka je dashi wurin manzon allah {saw} koda manzon allah yagan shi nan take ya gano waye shi manzon allah {saw] ya bijirowa da wannan sarki addinin musulunci amma yaki karbar addinin musilinci , amma duk da haka manzon allah {saw} yaci gaba da kyautata masa sannan yayi umar nin asake shi kuma asaki duk wani dan kabilar wannan mutum. To a lokacin da wannan mutum yaga kyawawan dabi’un manzon allah {saw} daga karmic da mutunci irin na shugaban mu annabi muhammadu {saw} nan take sai yadawo wurin annabi ya mika wuya ya musulunta ba tare da an tilas ta masaba , harma yake cewa da manzon allah {saw} yana mai cewa::: Ya manzon allah {saw} kasani cewa walhi kafin yau yau dinnan babu wani wanda nake gaba da shi sama da kai kuma babu fuskar da nake kyamar in gani kamar fuskarka to amma yau fuskarka tazama itace mafi soyyuwar fuskoki a gareni, kuma walhi adacan babu wani addini da nake mutukar kinsa a zuciya sama da addinika to amma yanzu wallahi addinika shine mafi soyyuwar addinai a gareni dukkansu kuma walllahi ada can babu wani gari da nake mutukar adawa da shi kamar garinka to amma wallahi a yanzu nafi sansa fiye da dukkan garuruwan duniya baki daya. Manzon allah {saw} yayi mutukar farin ciki da musuluntar wannan babban mutum mai karmic da girma a cikin muta nan sa , saboda ta sanadiyar musuluntar sa anasamu wasu da dama daga cikin muta nansa sun mika wuya sun karbi addinin gaskiya. A lokacin da wannan sarki ya kama hanyarsa ta komawarsa gida sai ya yanke shawarar shiga makka domin yayi umara don haka kawai yana shiga garin makka da yake suma kafiran makka sunyi mutukar saninsa domin a garinsu ne suke suyo duk wani abinci na alfarma, ko da ya shiga garin makka sai ya fiti fili ya nunawa kafiran makka cewa shifa ya karbi musulunci To daga farko su wadannan sun so su cutar dashi amma kuma sai suka tuna gudun mawar da garinsu yake basu na kayan masarufi don haka sai suka rabu dashi amma sai da ya rantse musu da allah bazai sake sayar musu da komai daga garin suba har sai sunyi imani da shugaban halitta, tun daga ranar wannan sarki ya yanke alakar cinikayya dasu , a sandiyyar wannan abu da yay musu sun shiga cikin matsala to anan ne sai manzon allah {saw} ya aikawa wannan mutum cewa yaci gaba da harkar kasuwanci dasu saboda karamci na shugaban halitta. Shi kuma sarki sumatatu nan take ya karbi wannan umarnin shugaban halitta annabi muhammadu {saw} ya dawo da harkar kasuwan ci da su. Sarki sumatatu ya taka rawar gani sosai a cikin addini musulunci musanman ma a lokacin wafatin manzo {saw} a yayi da mutane da dama sukayi RIDDA harma suka bi musailamatul kazzabi . Shi kuma sarki sumatatu ya zare dantse yaci gaba da kiran mutane yana nuna musu cewa lallai duk wanda yayi RIDDA yabi musailamatul kazzabi to lallai wannan ya tabe bashi da rabo duniya da kuma lahira. To daga nan ne mafi yawa daga cikin muta nansa suka dawo, yardar allah ta tabbata ga wanna sarki jarumi wato sumatatu. Wannan shine karshen gwagwarmayar RUNDUNA TA HUDU ina allah yaso zamu kawo muku runduna ta biyar ku kasance damu Zaku iya biyomu ta wannan PAGE namu mai albarka wato @[174223056110540:0] Or you can follow this link www.facebook.com/gaskiyatafikwabohausa1

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA