Ramadan khareem

WANNE IRIN SHIRI KA YI WA RAMADHANA ? SAHABBAI (RIDWANILLAHI ALAIHIM) Sun kasance suna addu'a da zarar an kammala azumin ramadhana suna cewa: Ya Allah ka kar'bi ibadunmu da muka gabatar a Ramadhana. Suna yin wannan addu'a tsawon wata shida. Sannan kuma su cigaba da yin addu'ar: Ya Allah ka kai mu ramadhana muna masu imani da lafiya. Wannan addu'a kuwa yin ta suke yi har sai sun riski ramadhana. Sahabbai shirye-shirye suke yi na tunkarar ramadhana tun watanni shida gabanin ramadhana. * Dan uwa wanne irin shiri kake yi game da wannan wata mai cike da dukkan alkhairai wato ramadhana? * Wanne tsari ko shiri kake yi game da yawan tilawar Al-Qur'ani da zaka gabatar a ramadhana? * Wanne shiri kake yi na nafilfilin Salla d'ori akan wanda kake yi kafin ramadhana? * Wanne irin tanadi kake yi na abinda zaka ciyar ga masu azumi a Ramadhan? Wadannan sune abubuwan da ya kamata mu sanya su a gabanmu a wannan lokaci da watan ramadhana ke fuskanto mu gadan- gadan. Watan ramadhana kyauta ce, falala ce, rahma ce, sannan dacewa ce Allah ya bawa duk wanda ya samu damar kaiwa cikinsa, to, alamar godiya ga Allah ga duk wanda ya samu wannan kyauta shine yawaita ibada, da neman gafarar Allah a cikinsa. Allah yasa mu dace da albarkatun watan ramadhana muna masu imani da cikakkiyar lafiya, ya bamu ikon bauta masa yadda yake so, ya kuma karba mana ibadun, ya gafarta mana zunubanmu. Ameen

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA