
<<<>>>> RUNDUNA TA SHIDA <<<>>> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA A cikin watan rabi’ul auwal ne labara ya zowa shugaban halitta cewa wasu daga cikin kafirai sunyo sansani domin su kwace dabobbin wasu musulamai a wani gari da ake cewa haifa’u, wani kauye ne a kusa da madina, su kuma kafiran suna wani kauye da yake da suna kassatu mil ashirin da hudu ne daga madina. To koda wannan labara ya zowa shugaba sai ya samu mutum goma daga cikin sahabbai a bias jagorancin muhammadu dan muslimata ya tura su domin bada kariya gay an uwanmu musulmai da kuma fito na fito da azzluman kafiran wannan yanki. To andade ana fafatwa tsakanin wadannan sahabbai na manzon allah {saw} da kuma wadannan miyagun kafirai a inda su kafiran suka samu nasarar kasha duk kan sahabban nan guda goma amma banda shi muhammadu wato kwamandan yakin amma shima a zaton su sun kashashi saboda raunukan da yasamu. To bayan sun tafi sai ya farfado ya dawo gida ya bawa manzon allah labari n yanda al’amarin ya kasance, to sai manzo allah ya dan jinkirta musu kadan sai acikin watan rabi’ul akhiri sai yaske tura wata rundunar a kakashin jagorancin abu ubaidatu dan amiru domin yaje shima yayi maganin wayannan yan iska, to amma meke faruwa tun kafi su isa wannan gari tuni kafirai sun ranta a na kare gaba dayansu sun gudu. Koda abu ubaidatu yaga haka sai suka shiga garin suka koro dukan dabbin garin suka taho gida. Wannan shine abin da yafaru da runduna ta shida a takaice in allah yaso zamu kawo muku runduna ta bakwai. Ku kasance damu ta wannan shafi mai albarka don samun abubuwa daban daban. Wato @[174223056110540:0]
Comments
Post a Comment