RUNDUNA TA BIYAR

world-war-1-620x330.jpeg <<<>>>> RUNDUNA TA BIYAR <<<>>> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA Kabilar banu asadi, sune suke da wata mummunar al’ada ta cutar da duk wani musulmi da yabi ta kusa da garin su don haka sai labara ya zowa shugaban halitta {saw}. Sai manzon allah {saw} ya shirya runduna ta mahaya arba’in ya bawa ukashatu kwamandan yaki domin su je su tarwatsa shakiyancin wadannan shaidanu. A lokacin da ukashatu ya nufi gari wayan nan makiya allah yasa sai da suka kusa karsawa gari sai labara yazo musu don haka sai kowanen su ya cika rigarasa da iska suka gudu suka bar garin. Amma duk da haka ukashatu suka shiga garin suka samu wani mutum shi kadai yana ta barci sai suka ce ya nuna musu dabobin wayannan kafirai da suka gudu suka bar garin. Ba tare da bata lokaci ba, wannan mutum ya tashi ya fara nunawa musulmai dukiyoyin wadannan kafirai musulmai suka tattaro dabbobi da dukiyoyin su suka juyo dasu a mazaunin ganima kuma haar musulamai suka dawo garin madina babu abin da ya shafesu dan gane da cutar wasu kafirai koda akan hanya ne. Anan wannan runduna tayi nasarar tsoratar da wadanan gayyar kafirai da suke cutar da musulmai. Kuma ankarya tattalin arzikin su balanta na su sake samun damar cin zarfin musulunci. Wannan shi abin da yafaru da runduna ta biyar a takaice in allah yaso zamu kawo muku runduna ta shida. Ku kasance damu ta wannan shafi mai albarka don samun abubuwa daban daban. Wato @[174223056110540:0] Or you can follow this link www.facebook.com/gaskiyatafikwabohausa1

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA