Posts

Showing posts from September, 2015

SUNAYEN SANATOCI 83 WAYANDA SUKA MARAWA BOKOLA SARAKI BAYA DUBA KO AKWAI NAKA

1. David Umaru (APC – Niger East) 2. Ali Ndume (APC – Borno South) 3. Godswill Akpabio (PDP – Akwa Ibom West) 4. Biodun Olujimi (PDP – Ekiti South) 5. Malam A. Wakil (APC – Bauchi South) 6. Isah Misau (APC – Buachi Central) 7. Emmanuel Paulker (PDP – Bayelsa Central) 8. Ogola Foster (PDP – Bayelsa West) 9. Gershom Bassey (PDP – Cross River South) 10. James Manager (PDP –Delta South) 11. Ahmadu Abubakar (APC – Adamawa South) 12. Joshua Lidani (APC – Gombe South 13. Achoma Nneji (PDP – Imo North) 14. Shehu Sani (APC – Kaduna Central) 15. Salihu Egye (APC – Nasarawa South) 16. Mao Ohuabunwa (PDP – Abia North) 17. Mohammed Ohiare (APC – Kogi Central) 18. Phillip Gyunka (APC – Nasarawa North) 19. Abdullahi Adamu (APC – Nasarawa Central) 20. Samuel Anyanwu (PDP – Imo East) 21. George Sekibo (PDP – Rivers East) 22. Monsurat Sunmonu (APC – Oyo Central) 23. Jeremiah Useni (PDP – Plateau South) 24. Ogba Obinna (PDP – Ebonyi Central) 25. Aliyu Abdullahi (APC – Niger North) 26. Sunny Ogbuoji (PDP ...

SUNAYEN SABBIN MINISTOCIN DA BUHARI ZAI NADA

Sabbin Ministoci Da buhari Zai Nada . . Ga jerin sunayen ministocin da shugaba Bahari ya mikawa yan majalisa wadda zasu tantance a yau:- : 1.Prof. Tam David West 2.Femi Falana (SAN) 3.Lt.-Gen. Abdulrahman Dambazu (rtd) 4.Prince Olagunsoye Oyinlola 5.Wale Edun 6.Abubakar Malami (SAN). 7.Mrs. Ifueko Omoigui-Okaru 8.Chief Bode Mustapha 9.Engineer Segun Oni 10.Dr Kayode Fayemi 11.Dr. Abba Ruma 12.Chief Kanu Agabi 13.Donald Duke 14.Babatunde Raji Fashola 15.Chibuike Rotimi Amaechi 16.Rotimi Akeredolu 17.Oby Ezekwesili 18.Festus Odimegwu 19.Engineer Funsho Kupolokun 20.Yinka Folashade Oredola 21.Bisola Adegbenro 22.Isaiah Danjuma (son of TY Danjuma) 23.Dele Momodu 24.Kehinde Lawanson 25.Chief Bayo Ojo (SAN) 26.Pat Utomi 27.Charles Chukwuma Soludo akwai wasu wanda basa cikin jerin a yanxu . . shin mai zakuce . . . . YI LIKE NA WANNAN PAGE DON SAMUN INGANTTATUN LABARAI ⇛ @[174223056110540:0] ⇛ @[174223056110540:0] .

MEYE AMFANIN YIN LALLE?

MEYE AMFANIN YIN LALLE?   KARANTA KIJI 'YAR UWA   Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ta kwadaitar da muyi lalle akwai sirrika acikin sa.         Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafan sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana yana reserving ni imar mace ba tare da ya gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai: Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa lalle inyadan huce sai kiyi sit bath dashi nã two weeks in Allah yayarda zata warka   : Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle spoon daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake using dinsa don gyaran skin wato Fata  Saboda maganin d...

yasalam

yassalam wata badala ce da akayita kwanakin baya allah ya karemu ameeen http://www.mywapblog.com/en/post.php?go=Go&file=yasalam.jpg

BARAKA DA SALLAHR DA ZAN IYA BAWA DAUKACIN ABOKAINA MATA DA MAZA

Image
Assalamualaikum Yan Uwa Na Mata Da Kuma Maza Inaiwa Daukacin Wanda Allah Ya Bawa Damar Yin Azumin Yau Barka Da Shan Ruwa. Bayan Haka Zanyi Amfani Da Wannan Dama Ta Neman Afuwa Ga Daukacin Abokaina Baki Daya Wanda Naiwa Laifi Koda Kuwa Magana Ta Fatar Baki Ce Kokuma A Comment Da Nakeyi Kodai Makamancin Haka Da A Yafemin Don ALLAH Nikam Nayafewa Kowa. ALLAH Ya Hadamu Da Alkairin Wannan Wata Ameen Summa Ameen.

HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WADDA YA YI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARAFAT KENAN).

    HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WADDA YA YI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARAFAT KENAN).     ANNABI (SAW) YA FARA DA CEWA: “Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a wannan wuri a yau. Ya ku mutane kamar yadda ku ka riki wannan wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa mutane kayan da suka ba ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku. Ku tuna fa, hakika Allah zai yi sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.   Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye addininku. Yanzu kan ya ...

BAYANI MAI AMFANI

Jamaa ayi mana afuwa sakamakon wasu yan canje canje da zaa gani bakomaine ya janyo hakanba sai don inganta muku shafin mungode da kullawarku allah ya bar zumunci.

LABARIN MAI SAYYEN BIRRI

"A Wani kauye a Kasar Zimbabwe Wani Mutum yace wa mutanen wannan Kauyee duk Wanda yakamo 'biri' zaibashi dala Ashirin; Mutanen wannan Kauye suka jeji sukayi takamo birare suna kawo masa yana basu dala ashirin - ashirin; Bayan wani lokaci sai kasuwar taja baya. Koda yafahimci haka sai yakara farashi akan duk Wanda Yakawo 'biri' dala talatin; Kauyawa suka bazama kuma akayita kamo birurruka, Bayan wani lokaci kasuwar ta kuma ja baya dan birurruka sunyi karanci. Can sai wannan mutumi yacewa Kauyawa yanzu kam duk Wanda yakawo biri zansayeshi dala arba'in, nafa suka sake bazama ganin biri yazama Jan aiki bama ta batun kama shi ba, sai jifa-jifa. Wannan mutumi sai yasake cewa Kauyawan nan, Ni zanyi tafiya zuwa Afrika ta kudu domin wasu harkokin kasuwanci na, amma ga Mataimakina nan duk Wanda yakawo masa 'biri' zaibashi dala dari. Nanfa Kauyawa hankali yatashi ina za'a samu biri duk sunkame su. Bayan wani lokaci sai shi mataimakin wannnan d'an kasuwa ya...

KALLOLIN MIYA IRI DABAN DA BAN

miyAR ugWU

MIYAR UGWU Kayan Da Ake Bukata Kayan Ciki Nama Ganda Stockfish Crayfish Ugwu Leaf Mai Agushi Seasoning Spices Yadda akeyi Ki sami ganyen ugwu ki gyara ki yanka kanana, ki wanke ki ajiye. Ki tafasa namanki da kayancikin. Ki soya manjanki ki xuba markadadden kayan miya ki wanke stock fish ki xuba da gandarki da kk dafa tayi laushi kk yanka kanana a ciki k xuba dakakken agushi d maggi kayan dandano da dakakken crayfish ki bari ta dahu sosai sannan ki xuba ugwun da yawa ki sauke bayan kamar minti 10 shikenan uwar gida

MIYAR ALBASA

hmmmm

Rayuwa kenan images.jpeg

wanda bai samu zuwa aikin haji ba toga dama ta samu

'Yan uwana wadanda bamu samu damar zuwa hajjin bana ba, ga wata shawara nan daga babban Malamin nan Ibnu Rajab Alhanbaliy (rah) yace: - Duk wanda bai samu damar tsaiwar Arfah ba, to yayi kokari ya tsaya bisa iyakokin Allahn nan wanda ya sanshi. - Duk wanda bai samu damar kwana a Muzdalifah ba, to yayi kokari ya kwana cikin biyayyar Allah aduk inda yake, domin neman Kusancin Ubangiji. - Duk wanda bai samu damar zuwa Mina domin yanka abin yankansa ba, to yayi kokari ya yanke son zuciyarsa domin isa zuwa ga cikar burinsa. - Duk wanda bai samu damar isa zuwa ga Dakin Allah ba, saboda yayi masa nisa, to yayi kokari ya nufi Uvangijin 'dakin. Domin shi yafi jijiyar wuyansa kusanci gareshi. Daga littafin LATA'IFUL MA'ARIF shafi na 633.

TUNATARWA; Ranar lahadi 29 ga watan zul qa'adah daidai da 13 sept shine ranar karshe na yanke kumba da aski ga masu layya

TUNATARWA; Ranar lahadi 29 ga watan zul qa'adah daidai da 13 sept shine ranar karshe na yanke kumba da aski ga masu layya. Litinin daya ga watan zulhijja daidai da 14 ga watan sept - laraba10 ga watan zulhijja dai dai da 23 ga watan Sept, kuyi Azumi ,Sadaka,Kyauta,kyautatawa iyaye, Sada zumunci, da duk aikin alheri acikinsu yadda zaku iya saboda Allah yayi rantsuwa da wadannan kwanaki goma masu albarka ne wanda babu kwanaki goman da suka kaisu albarka a shekara.(wato yinin kwanakin) Da Annabi (SAW) ya gayawa sahabbai, sai suka tambayi Annabi (SAW) ko da JIHADI fisabi lillah,? Yace koda JIHADI fisabi lillah sai Wanda ya fita Jihadin da dukiyarsa kuma ba abinda ya dawo. Wato an kasheshi kuma an kwashe dukiyar.

BUDURWA KI LURA DA WANNAN SOSAI

YA KAMATA KI NISANCI WADAN NAN ABUBUWAN KAPIN KIYI AURE >>>> (1) ki nisanci duk wata qawa da zata ke bayyana miki tsaraicinta. (2) kada ki yarda qawarki ta ke ya baki ta fuskar sha'awa. (3) ki guji qawar da zata ke rungumeki da nufin wasa. (4) ki tsoraci qawar da za ta ke kunna miki fina finan madugo. (5) ka daki yarda qawarki ta ke kama hannunki na tsawon lokaci don idan ta jima tana shafa miki hannu da sannu zata kai ga mabudin sha'awa shi ne ta fara shafa miki kirjinki wato. (6) ki nisanci qawar da za ta ke shafa gashin kanki. Idan siffar qawarki ya burgeki sai kice masha allah, wace Allah ya kyautata mata sura (siffa) amma tabawa ko ayi wasa dashi ''gashi, kirji da sauran gabobin jiki'' wannan mijinta ne ya keda iko akai. Dafatan Allah ya kare mana yan uwa mata masu wannan halayen amin.