LABARIN MAI SAYYEN BIRRI

"A Wani kauye a Kasar Zimbabwe Wani Mutum yace wa mutanen wannan Kauyee duk Wanda yakamo 'biri' zaibashi dala Ashirin; Mutanen wannan Kauye suka jeji sukayi takamo birare suna kawo masa yana basu dala ashirin - ashirin; Bayan wani lokaci sai kasuwar taja baya. Koda yafahimci haka sai yakara farashi akan duk Wanda Yakawo 'biri' dala talatin; Kauyawa suka bazama kuma akayita kamo birurruka, Bayan wani lokaci kasuwar ta kuma ja baya dan birurruka sunyi karanci. Can sai wannan mutumi yacewa Kauyawa yanzu kam duk Wanda yakawo biri zansayeshi dala arba'in, nafa suka sake bazama ganin biri yazama Jan aiki bama ta batun kama shi ba, sai jifa-jifa. Wannan mutumi sai yasake cewa Kauyawan nan, Ni zanyi tafiya zuwa Afrika ta kudu domin wasu harkokin kasuwanci na, amma ga Mataimakina nan duk Wanda yakawo masa 'biri' zaibashi dala dari. Nanfa Kauyawa hankali yatashi ina za'a samu biri duk sunkame su. Bayan wani lokaci sai shi mataimakin wannnan d'an kasuwa yacewa mutanen wannan Kauye, kunga wadannan "birurruka" da kuka siyarwa da megidana Kuje ku kawo dala tamanin-tamanin zansayar muku dasu,idan maigidana yadawo sai kusayar masa akan dala dari- dari tunda yace muku haka zai siya duk Wanda yakawo masa biri. Kauyawa suka bazama kowa yadauko Ajiyarsa sukayi ta siyan birurruka har saida suka sayesu kaf. Daga nan basu kara ganin Maisayen 'birurruka' ba balle mataimakinsa

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA