wanda bai samu zuwa aikin haji ba toga dama ta samu
'Yan uwana wadanda bamu samu damar zuwa hajjin bana ba, ga wata shawara nan daga babban Malamin nan Ibnu Rajab Alhanbaliy (rah) yace: - Duk wanda bai samu damar tsaiwar Arfah ba, to yayi kokari ya tsaya bisa iyakokin Allahn nan wanda ya sanshi. - Duk wanda bai samu damar kwana a Muzdalifah ba, to yayi kokari ya kwana cikin biyayyar Allah aduk inda yake, domin neman Kusancin Ubangiji. - Duk wanda bai samu damar zuwa Mina domin yanka abin yankansa ba, to yayi kokari ya yanke son zuciyarsa domin isa zuwa ga cikar burinsa. - Duk wanda bai samu damar isa zuwa ga Dakin Allah ba, saboda yayi masa nisa, to yayi kokari ya nufi Uvangijin 'dakin. Domin shi yafi jijiyar wuyansa kusanci gareshi. Daga littafin LATA'IFUL MA'ARIF shafi na 633.
Comments
Post a Comment