BUDURWA KI LURA DA WANNAN SOSAI
YA KAMATA KI NISANCI WADAN NAN ABUBUWAN KAPIN KIYI AURE >>>> (1) ki nisanci duk wata qawa da zata ke bayyana miki tsaraicinta. (2) kada ki yarda qawarki ta ke ya baki ta fuskar sha'awa. (3) ki guji qawar da zata ke rungumeki da nufin wasa. (4) ki tsoraci qawar da za ta ke kunna miki fina finan madugo. (5) ka daki yarda qawarki ta ke kama hannunki na tsawon lokaci don idan ta jima tana shafa miki hannu da sannu zata kai ga mabudin sha'awa shi ne ta fara shafa miki kirjinki wato. (6) ki nisanci qawar da za ta ke shafa gashin kanki. Idan siffar qawarki ya burgeki sai kice masha allah, wace Allah ya kyautata mata sura (siffa) amma tabawa ko ayi wasa dashi ''gashi, kirji da sauran gabobin jiki'' wannan mijinta ne ya keda iko akai. Dafatan Allah ya kare mana yan uwa mata masu wannan halayen amin.
ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI
ReplyDelete