MEYE AMFANIN YIN LALLE?

MEYE AMFANIN YIN LALLE?

 

KARANTA KIJI 'YAR UWA

 

Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ta kwadaitar da muyi lalle akwai sirrika acikin sa.

 

      Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafan sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana yana reserving ni imar mace ba tare da ya gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai: Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa lalle inyadan huce sai kiyi sit bath dashi nã two weeks in Allah yayarda zata warka

 

: Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle spoon daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake using dinsa don gyaran skin wato Fata

 Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle spoon daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake using dinsa don gyaran skin wato Fata

 Mu dawo kan mau du in mu, lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata, in kina son gyara fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum 30 mins b4 wanka sai Kinga clear diff in two weeks in sha Allah: Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun zakiga canji, sannan gamai son kamshin skin

: Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu

: Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk zakiga canjin skin in sha Allah: Sannan ga Amare kum

Kafin kiyi dilke na aurenki

: Skin zatayi laushi, haske da kuma santsi

 

 Two months before bikin ki zaki iya wannan keda kanki kuma zakiji dadin hakan

 

 

 Ki samu lalle mai kyau ki kwaba da turaren ki mai maiko, turaren gargajiya mai mai dinnan to ki jika kamar one bucket ba ruwa ruwa sosai ba Kamar dai kunu, kullum sai ki shafe jikinki da hadin lallen nan duka jikin ki, sãi kizo ki saka turaren wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara jikinki hayakin turaren nan ya shiga sosai sai ki fita kije kiyi wankan ki zakiga change in your skin rapid change kuwa

 

 Daga karshe kuma ga masu fama da pimples, er uwa ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki after months kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH